Skip to content
Part 37 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Jikin Husna ya dauki kyarma bakinta na karkarwa ta kasa cewa komai.

Ina zata Kai Daddy da sunan miji? Bata taba kawo hakan a Ran ta ba sai yanzu ta gano abinda Anty Amal take nuna Mata. Da kyar ta samu ta kwato maganar da Bakin ta yayi gardamar furtawa.

“Wallahi ban San hakan ba sai da Kika Ankara Dani . Ni da kaina yaci ace na gano hakan Amma da Yake Rai na da hankali na suna Kan Yaya muhsin sai ban kawo hakan ba.

“Ta Yaya Anty Amal zanyi Haka? Baban Yaya muhsin? Ko duk Duniya maza zasu Kare ba zanyi hakan ba ko don Yaya muhsin bare Kuma ke da Mami. Indai hakane kuwa yanzu Zan bar gidan Nan Wallahi.

Sai ta Soma jido Kaya inda Amal ta Riko ta.

“Nasan Baki Gane manufar Daddy ba shiyasa na sanar dake don ki kiyaye. Kuma Ina kike Shirin zuwa? Ai inda zakiji Bai wuce masanawa ba kin kuma bashi damar da Yake bukata don Nan Yana kunyar idon Mami da mu kanmu . Bari na fada Miki abinda Baki sani ba. Yanzun Nan da ya koro ki daga wurin Yaya muhsin kishine ya sa shi yin hakan har Yake neman Raba ku da Yaya muhsin din . Kawai dai ki kame kanki irin macen Nan da ke ankarwa da fassara kallon namiji kingane? Ta amsa da ta Gane .

Haka Alh Aminu ya kwana Yana Jin haushin muhsin washer gari Kuma ya Isa gidan lauje ya zayyano mishi abinda yakeji akan yarinya Husna.

Laujen ya gaggabe da Dariya Yana Fadin.

“Wai Kai wahayi akayi maka da Ahalin mu azu ne? Ka so uwa Kuma yanzu Diya kake so? Kana mantawa da kashedin Zubaina na cewa jinin ku Bai hadu da na Ahalin mu azu ba. Ka manta Asarar da kayi ne da har zuciya ta kwashe ka son yarinyar Nan.”

“Kira min Zubaina lauje na Roke ta su barni na Auri yarinyar Nan Wallahi idan ban Aure ta ba akwai matsala komai Zan iya bayar wa tun daga wasila zuwa muhsin da Amal na Rantse maka Zan bayar indai za abarni na Rayu da Husna.

Lauje ya hada garwashi ya Kira Zubaina sai kuwa gashi ta bayyana tana kyalkyata Dariya inda Kuma lauje ya Rattabo Mata bukatar Alh Aminu ta su barshi ya Auri Husna Yar wajen Halima.

Zubaina tace zai iya Basu bakaken karnuka guda d’ari? Bakaken jakkai guda d’ari? Bakaken maguna guda d’ari? Idan zai Basu zasu iya hakura su barshi ya Auri Husna Amma idan aka samu akasi wurin kawo musu karnuka ko jakkai ko maguna daya Bai cika ba Koda 99 basu Kai dari ba to zasu ballo tsiya a tabbatar komai dari aka Basu daidai. Kuma Kar ya sake Aure ya hada Dan shi da Dan mu azu ko Dan mu azu da nashi Diyan in ko akayi Haka Nan ma zasu ballo hancin tsiya.

Da Haka Alh Aminu yayi Mata albishir din Basu komai suka bukata indai sun yarda. Da haka Zubaina ta fiice shi Kuma ya cika da murna da farin ciki dama abinda yasa baiyi gaban kanshi ba don Bai manta kashedin Zubaina ba na cewa jinin su Bai hadu da na iyalan mu azu ba Amma yasan za a iya toshe Bakin Zubaina da wani Abu ko da jinin Ahalin shi ta bukata zai bayar sai akayi sa a Zubaina karnuka da jakkai da kuma maguna take so don Haka ya barwa lauje komai.

Ya taho gida Yana tunanin ta inda zai fara gyaro ta tsakanin shi da Husna don ya San indai daga hajiya ne bashi da matsala Amma kafin Nan sai ya fara sanin matsayin muhsin wurin ta don yaron ya Rike mishi makoshi

Ya na shigowa gidan ya iske Husna ta lallabo bayan muhsin dake cike ciken wasu takardu ta Rufe mishi ido inda hannun nata ya tabbatar wa muhsin itace don Haka sai ya yayi carab da hannunta ya Rike dai dai da shigowar Alh Aminu. Zuciya ta ciwo shi don kishin yaron Yake bil hakki tamkar zai Rufe shi da duka Amma sai ya wuce kamar Bai gansu ba. Kai tsaye ya wuto falon inda haj wasila da Amal ke zaune Yana fadin

“Wai wasila Ina maganar Auren Safina da muhsin da Kika sanar Dani? Ya kalle shi da mamaki tunda shine lambar farko da Yara yi Mata tutu a zuciya Akan maganar Auren.

“Wane Aure Kuma da ka nace Akan kassaruwar shi? Ba Kai ka Goya mishi baya ba kuka so yakata?

“To yanzu na Amince kiyo min list din komai da kike bukata Zan Baki don yaron can neman dauko min magana yakeyi…

Dariyar da haj wasila ta sheke ce ya sa shi binta da kallo sai da tayi Dariya har ta gaji kafin ta dube shi duba irin na sama da kasa.

“Uhum Alh Aminu kenan wato don kar ya dauko maka magana ne zaka yarda da batun Safina yanzu? Da dai ka fito ka Gaya min gaskiya Akan kun hada nema tare ne zanfi yarda tunda ai Kai ka Fara nuna mishi ya gujewa auren Safina . To Nima yanzu ban yarda ya Auri Safina ba sai wadda Yake so tunda kaima ai Haka ka ce min ko? Ai sai dai asan biri a San gata Wallahi amma Nima yanzu ne Zan murza gashin Baki don idona biyu banyi barci ba Kuna ba sai an fada min nake ganewa ba.

Ya saki Baki Yana kallon haj wasila.

“Haka kikace? Ya tambaye ta.

“Eh Haka nace Mana tunda anyi walkiya ta haska. Har gida maimuna tazo taci zarafina don tana ganin nice banso muhsin ya Auri Safina ba sai yanzu da yake bukatar ka ce kana tsoron Kar yaro ya kasa ka shine ka lallabo ka jona mishi Mata Kai Kuma kayi wuff da wadda Yake so to ban yarda ba Nima Wallahi shi da Safina sai dai su hadu su gaisa Amma Aure sai dai ko in na mutu don Zan nunawa maimuna da Kai Ina Nan a yadda kuka sanni.

“Zan kuwa shayar dake mamaki Wallahi ke da kanki Zaki karyata kanki. Ya fada Yana shigewa daki.

Amal ta dubi Hajiya Wasila, “Mami Kinga abinda nake fada ko? Ni fa ina tsoron Daddy Wallahi ya iya kulla tsiya.

“Nima na iya kulla tawa tsiyar shima namiji ya iya tsiya bare Ni da ko shaidan Yana tsoron makirci na?

 

<< Hawaye 37Hawaye 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×