Skip to content
Part 38 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Anty maimuna ta kulle wani Abu ta jefa cikin Rijiya tana fadawa Safina yadda Za ayi.

“Ai indai Yaya wasila itace Nima nice tunda abun babu mutunci zata ga abinda zai faru.

“Wallahi mama in na Auri muhsin sai matar Nan ta Gane da goshi ake salla ko an Sha giya Wallahi tunda dama tuni na gano itace ke min zagon kasa.

“Uhum Sha kurumin ki Safina ai Ni kaina nayiwa Yaya wasila mugun tanadi muddin Auren ku ya tabbata.

“To Mami ta Yaya zamu Gane aikin mutumin Nan yayi?.

“Ai sunan muhsin da kika Kira kafin na jefa layar Nan a Rijiya shi da kanshi zai Zo amsa Kiran da kikayi mishi harma ya furta Miki kalmar so inda Kuma Zaki soma gasa Dan banza fiye da yadda ake gasa masara. Ke dai zamo cikin shiri Nan da kwana biyu sai kinjiyo kyakkyawan Labari.

Safina ta daka tsalle tana Rungume Uwar ta tana murna da fatan cikar burin ta na auren muhsin.

Inda kuma a gefe guda Alh Aminu ya yanke shawarar zuwa har gida su kashe magana da Anty maimuna don ya gama Gane in ba aurowa muhsin Safina yayi ba to ba zai taba Barin shi samun Husna ba don Haka ya gama yanke shawara.

Kai tsaye washe gari ya nufo gidan maimuna inda Safina ta tarbeshi bayan sun gaisa Yake tambayar ta maimuna da Kuma mahaifin ta inda ta sanar dashi babanta yayi tafiya zuwa Abuja Amma mamar tana Nan inda yace tayi mishi magana da maimunar.

Aguje Safina ta karasa ga Anty maimuna ta fada jikinta tana fadin. “Wallahi aikin mutumin Nan yafi yankan wuka mama fito ga uban mijina ya karaso na Kuma San maganar ce ta kawo shi.

“Bana zato don ba uban shi akace zaizo ba shi ne da kanshi zaizo amsa Kiran ki. Nafi zaton dai ko Yaya wasila ce Babu lafiya.

“Allah yasa ma wucewa zatayi don na tabbata idan tana Raye akayi Auren Nan sai ta zame min olsa.

Da sauri maimuna ta fito tanayiwa Alh Aminu sannu da Zuwa inda ta dauko mishi Ruwa da lemu. Safina tana labe tana sauraren su bayan sun gaisa ya Dora da yi Mata bayanin abinda ya kawo shi.

“Wai maimuna me ke faruwa ne akan maganar Safina da muhsin? Ni naji shiru wasila ba tayi min wani cikakken bayani ba Ni Kuma na kula yaron in ba Aure akayi mishi ba yana dab da dauko min magana shine kawai na taho Nan wurin ki don ban samu amsar da ta gamsar Dani wurin wasila ba..

Maimuna tace. “Uhum Alh Aminu kenan ai Ni ban taba sanin Haka Rayuwar ta koma ba sai da wannan maganar ta taso inda na Gane naka shi ke bada Kai . Dama ance dadin Zama sai bare na Kuma yarda da hakan don Yaya wasila ta nuna min itace Bata son Auren Safina da muhsin shiyasa kaji shiru Kuma ai ba zata fada maka gaskiya ba tunda bata Taki gaskiyar ba . Shiyasa ma nace to Allah ya zabawa Safina mafi ALHERI yanzu Haka ma wani na Shirin fitowa. Ta hada da shara mishi karya.

“A a ku dakatar dashi maimuna don ai zumunci kuke son hadawa Kuma duk Wanda Safina zata aura ai Bai kamo kafar Dan uwan ta ba . Na so ta iske Mai gidan Amma Zan kirashi ta waya idan ya dawo kuma Zan Zo na sameshi muyi magana. Amma kafin ya dawo din Zan Baki hakuri Akan abinda tayi Miki ki Rabu da ita Ni yanzu nemawa muhsin Auren Safina ya kawo Ni Kuma don Allah Kar ku saka mishi Rana nesa in son samu ne wata Daya Tak nake so ku saka mishi don duk hakkin shi na sauke saura wannan.

Safina ta daka tsalle ta fada Akan gado tana murna yayin da maimunar Kuma ta nuna lallai ta hakura da muhsin gara ta Auri Wanda yazo yanzu tunda yaya wasila ta nuna Bata son Safina ba dadin muhsin zataji ba don Haka adaiyi hakuri kawai.

Sai ganin Safina sukayi ta fito tana fadin, “A a mama tunda shi baba yazo ya bada hakuri ai ki hakura kawai na Auri muhsin din.

Wani haushi ya kule maimuna Amma Dole ta share tana fadin, “To shikenan Allah ya zaba ALHERI. Da Haka yayi musu sallama ya wuce inda Anty maimuna ta buge Bakin Safina tana fadin

“Shegiya marar aji Ina nema Miki Daraja da martaba kina zubsrwa kanki yanzu inda a gaban Yaya wasila ne shikenan kinja min abin magana da Gori.

“To mama ai naji kina fadin ayi hakuri Kuma ba kudi muka Kai don hakan ta tabbata ba?

“To don ubanki da muka Kai kudi ance Miki uban shi ne zaizo ba shi ba? Da kin barni ai zance ya turo muhsin din da kanshi tunda an bada maganin da za a zuba mishi a abinci yadda zaiji kaunar ki Amma da Yake kin iya bada Mata Kika fito kina maida magana in kikace Haka zamuyi dake Wallahi Zan cire hannu na na barki ku goga da wasila idan Zaki iya.

Da mahaifin Safina ya dawo shima ya goyi bayan Alh Aminu inda Kuma aka tsaida magana wata guda Daya Tak.

Duk abinda akeyi alh Aminu Bai sanar da haj wasila ba don da gaske yayi nufin shayar da ita mamaki.
Su Anty maimuna ma kudi ya tura musu na kayan lefe da duk wasu hidimomi.

Sai da yarage saura sati biyu kafin ya bugo I V ya nufo gida don ya bawa muhsin ya soma rabo.

<< Hawaye 38Hawaye 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×