Skip to content
Part 4 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Kwana biyu rak sai ga sammaci ya sameshi wai ana karar shi. Ya karbi takardar sammacin yana duba daga wace kotu ta fito? Ya kalli masinjan ya kuma kalli Bello yana murmushi.

“Kuje abin ku zanyi waya don ba zan samu halarta kotun ba saboda ina da tafiya a Ranar. Ya fito da kudi Yana basu a matsayin suyi kudin komawa.

Suna tafiya ya kira babban Alkalin chiff Jorge Bala Idris yake fada mishi an turo mishi da wata takardar sammaci daga wata kotu dake da mazauni a sabon titin filin jirgi yana so yasa a kori Shari ar .

Ranar shiga kotu tayi Bello ya iso tun wuri amma har sha biyu na rana babu batun zuwan wanda ake kara har aka tashi kotu . Abu kamar wasa sai ga karamar magana ta Zama babba inda masinjan Nan da suka kaiwa AlhajiAminu sammaci ya ce mishi ya daina wahalar da kanshi mutumin da yake kara fa ba karamin mutum bane ya hakura kawai ya barwa Allah domin ko babu ta inda zaiyi nasara akan shi.

Sai kuwa gashi yazo kotu yafi sau a kirga sai dai a saka mishi rana amma babu wani action da aka dauka ko za a dauka. Har dai ya yarda da maganar masinjan Nan. Karshe dai Dole ya janye jikin shi daga kotun Amma fa Yana Jin Babu yadda Za ayi ya hakura da jinin Safiyya bare Luba da har gobe ya kasa yarda da ba hadiye zuciya tayi ta mutu ba sakamakon ta addancin da aka yiwa yarta.

*****

Haj Wasila ta dubeshi da wani kallo me nuna tuhuma ko zargi amma saboda rashin makama yasa ta hadiye tsegumin ta ta kora da ruwa. Shima ya kalleta da wani duba na Baki San Allon ba da Baki barni Zama lafiya ba.

“Wai wWsila lafiya ne kike min wannan abun kamar wani danki Muhsin? Ta dubeshi tana harara . “Me nace maka ne da har ka fadi haka? “Da nasan haka shahara take Aminu da na roki Allah ya saka shamaki tsakanin ka da shahara ya barka da iyakar kudin da zamu ci abinci kawai. Suma na yau kadai gobe ka koma ya baka na yau kadai. Ya zuba Mata ido kafin ya tanka.

“Sai kuma aka yi sa a ke din ba daga gidan bil ama Dan ba’ura kika fito ba bare kiyi bajintar shiga halwa.

Idan Kuma Kika sake na gano kina adawa da daukakar da nake samu na rantse miki sai na kawo miki kishiyar da zaku ci Arzikin Nan tare. Ya fada don ya San babu abinda Wasila ta tsana irin kishiya ai kuwa ta Mike tsaye tamkar zaka Kai mishi sura.

“Mafarki kake Aminu. Na rantse maka mafarki kake idan kuwa kana son amsa sunan namiji don Allah kace ka shirya Aure. Ba mace guda ba don Allah ka Auro uku da Kai da kanka ka tsani daukaka a Duniya…

Wayar shi tayi Kara ya duba inda yaga sunan lauje da sauri ya nufi dakin shi ya bar haj wasila da kumfar Baki.

Ya daga wayar Yana fadin, “Me Kuma akayi lauje? Me Kuma ake son nayi? “Kazo Ina nemanka ka manta da na ce maka Zubaina tana bukatar jinin makusancin ka?

Ya tari laujen,

“In dai jinin matata ne ba zan bayar ba lauje . Haka ma ba zan bayar da jinin Muhsin ko Amal ba gayawa Zubainar haka kace nace ba zan bayar ba. Amma bayan mutanen Nan uku kowa ma Zan iya bayar da jinin shi gareta ita da dodon kod’i.

To jirani gani nan Zuwa . Ya fada Yana aje wayar ya SHIGA ban daki yayi wanka ya feso kwalliya ta neman magana dama gashi Dan Gaye me son ado da kwalliya.

Ya fito Yana baza kamshi, Wasila zaune Akan kujera tree seater ta dubeshi gabanta na sarawa don har ga Allah a Duniya Babu abinda take so da kishi irin mijin nata Aminu don Haka yanzu da taga ya dauko wanka sai tayi zaton akwai inda zaije din.

Suna hada ido yayi maza ya game fuska itama sai ta doka mishi harara ya fice ya barta da tafasar zuciya. Amal dake leko mamin tasu ta shigo tana fadin Kai Mami Daddy yayi kyau Ina zaije? Ta harari Amal din.

“Tashi kibi shi ki tambaye shi…..

Aikuwa Amal din ta sheka aguje daidai da ya bude motar zai shiga ta fada jikin shi tana fadin Daddy Ina zakaje? Sai yayi zaton ko Uwar tace ta turo ta ta tambaye shi. Sai yaga Bari ya tura mata haushi.

Ya shafi fuskar Amal din Yana murmushi. “Amal Wai sabuwar Momy Zan kawo Miki ai kina so ko? Ta daga kanta Alamar tana so

“Yauwa to Bari naje ita ce ke jirana zamuje wani wuri. “To Daddy safe journey”, thank you my lovely baby

Ya fice daga gidan inda Amal ta koma take fadawa mamin wai Daddy yace nem momy zai kawo Mata.

Tabi bakin yarinyar da kallo don ta gama yarda Auren zaiyi

Ta soma safa da marwa kirji na dukan Tara Tara har ba taji lokacin da muhsin ya shigo falon ba inda Amal ke fada mishi Daddy zai kawo musu new momy.

“Heyyyyy very nice Ina son new momy irin ta gidan su friend Dina tana da kirki Kuma ga bebis dinta masu kyau.

Haj wasila ta harzuka da maganar yaran inda ta biyosu da jifa da filon kujera suka fice aguje inda Amal ke kyalkyala mata dariya……..

“Ni Aminu zaiyiwa wannan Rashin mutuncin? Na Rantse da Allah ya kusa saka kudin shi ya siyo tashin hankali zanga ta inda wata mace ke da muhallin Zama a Nan gidan. Gidan shi na dab da konewa. Kishiya?

<< Hawaye 3Hawaye 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×