Skip to content
Part 39 of 54 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Ya shigo gidan inda ya hango Husna da muhsin har ma da abokanshi mukhtar suna fira suna Dariya.
Shigowar shi yasa duk suka nutsu musamman muhsin da ya Rasa gano dalilin da iyayen shi ke neman saka shamaki tsakanin shi da Husna don Bai hasaso komai ba

Mukhtar ya taso da sauri yana yiwa Alh Aminu sannu da Zuwa har suka gaisa inda Husna tayi maza ta wuce ciki bayan tace “Daddy sannu da dawowa

Ya bita da kallo lokacin da take shigewa inda ya dubi muhsin da mukhtar dake Duke gaban shi ya mikawa mukhtar tarin I V dain Yana fadin

“Yauwa mukhtar kazo a daidai karbi katin Nan ku Soma Rabo tun kafin lokaci ya kure.

Mukhtar ya Mika hannu ya karbo I V Yana fadin,

“Daddy na waye?

“Na abokin ka ne Ashe Bai fada maka ba?

Sukayi kallon kuda shi da muhsin kafin suka hau Rige Rigen duba sunan dake cikin katin inda sukayi Arba da sunan muhsin da Safina.

“Daddy? Ban Gane ba fa?

“Ka kusa ka Gane bani Nan da sati biyu zaka fahimta.

“Nifa Daddy ba son yarinyar Nan nake ba Kuma ai kayi min alkawarin tunda bana son ta ba za a hada Ni da ita ba.

“Yanzu Kuma Ni Naga kamatar hada ku don Haka jeka ku Soma Rabo.

“Ka yafe Ni Daddy Wallahi ban taba son yarinyar Nan ba Akwai wadda nake so in dai gata kake kokarin nuna min Daddy to ka Aura min Husna.

“Tashi ka bani wuri na gama magana. Ya dubi mukhtar Yana Fadin.

“Tashi kuje mukhtar duk abinda kuke bukata kazo ka sanar Dani don Kai na wakilta a komai ko da zaice ba zaiyi komai ba to Kai kaje ka samu Safina ku tsara komai ba lallai sai da shi ba. Ya bude dash din motar ya zaro bandiran kudi ya mikowa mukhtar Yana Fadin.

“Rike wannan a hannun ka idan ma Basu Isa ba kazo ka fada min. Mukhtar ya karba Bakin shi na son tambayar Daddy n Amma ya kasa.

Da Haka Alh Aminu ya shige ciki ya barsu Anan.

“Mukhtar Kar ka bawa kowa I V din Nan don na Rantse da Allah ba Zan taba karbar Safina a matsayin Mata ta ba Husna nake so ba Kuma Zan Daina son ta ba sai in Rai ne yayi halin shi.

“Ba zai yuwu ba muhsin Dole ka Bari na Rana katin Nan don ba Zan yiwa daddy Haka ba kaima in Zan baka shawara ka karba sai nace kawai ka karbi yarinyar Nan a matsayin matar ka don tana son ka in yaso daga baya sai ka Auri Husna kaga ka karbi zabin iyayen ka ka kuma Auri Husna zabin zuciyar ka.

“Tunda kuwa Daddy ya dage da Auren Nan mukhtar sai dai ya San yadda zai da ita Wallahi idan kuwa shi ke son ta sai ya aurawa kanshi kawai. Kuma Ni Kar ka sake ka nemeni Akan komai kaje ku karata Kai dasu

Ya fada Yana nufar cikin gidan

Alh Aminu Yana shiga ya samu haj wasila ita da Amal da Husna zaune a falo ya fito da IV ya Mika Mata ta karba tana dubawa shi Kuma ya nufi hanyar dakin shi Bai tsaya yi Mata bayani ba.

Cikin dukan kirji ta kalli sunan Safina da muhsin Rubuce jikin katin. Da sauri ta Mike tsaye tana bugun kirji don su Amal Basu kawo katin na bikin muhsin da Safina bane Amma ganin haj wasila ta Mike tana bugun gaba ya sa Suma duba katin.

“Me mutumin Nan Yake nufi? A Rikice Husna ta dubi haj wasila tana karkarwa inda Amal ta dafe Kai tana fadin, “Da yawun Yaya muhsin kuwa a maganar Nan Mami?

“Uhum ina fa yawun shi karfa karfa dai Kuma Wallahi.

Shigowar muhsin a Rikice yasa duk suka maida hankali Kan shi.

“Mami Kinga abinda Daddy yayi min kuwa? Ya Mika Mata I V din don idon shi ma ya Rufe Bai lura da katin a hannun ta ba.

“Na San abinda hakan ke nufi muhsin Rakumi ne ke kokarin shanye Ruwan Yan tsaki Kuma Wallahi ba Zan taba yarda ba don hakan hanya ce da maimuna zata samu ta muzanta Ni abinda Kuma ban shirya mishi ba kenan duk yadda zanyi Wallahi sai nayi don ganin Auren Safina Bai kullu ba.

“Kice kema naki Auren zai mutu kuwa, Cewar Alh Aminu da ya fito Kuma yaji abinda take fada.

“Matukar dai nice na haifi muhsin ba zai taba Auren Safina ba ko don na nunawa Uwar ta nice na haifi muhsin. Aure Kuma da kake maganar mutuwar shi sai me Nene don ya mutu? Na zabi Ni da Safina mu barranta da Auren indai nayi nasarar Hana ta SHIGA gidan muhsin.

“To ki Soma lissafin cikar wa adin mutuwar Auren ki tun daga yau din Nan don yadda Kika hasaso din haka abin Yake ba kince kin San me nake nufi ba? To hakan ce zata tabbata.

“To mu nutsa a yafiyar muga me nasara tsakanin Ni da Kai . Ta dubi muhsin.

Kai Kuma ban ce kaje komai na bikin Nan ba don maimuna ta Gane nice uwar ka suyi kidan su suyi Rawar su.

“Dama saboda Haka na wakilta mukhtar Akan komai ko yaje ko Kar yaje Babu abinda za a fasa. Wallahi kina Hana Auren Safina kema naki ba zai Kuma kwana guda Daya Tak a Duniya ba ai yadda nakeji komai da kowa Zan iya Rabuwa dashi Akan cikar nawa muradin.

Husna wadda kuka ya Rikitowa ta toshe Baki inda ta nufi daki da sauri tana hado kayanta don indai Safina ce matar Yaya muhsin ita Kam ta Gama zaman gidan.

Muhsin ya bi bayan Husna wadda ke kuka tana cusa Kaya a jakar trolley.

Ya Riko ta Yana Bata Baki akan ta saurare shi taji yadda abin ya faro Amma Ina Bata saurare shi ba sai da ta cika akwatin ta zuge ta jawo shi gyalenta ma a hannu ta Riko shi ta fito inda muhsin ke Fadin

“Mami don Allah ki hanata tafiya Taki ta saurare Ni bare taji abinda Zan fada Mata.

Haj wasila ta zabga mishi harara don ji take Husna ta Rike Mata makoshi miji na so yaro ma na so Kuma dukkan su batajin zata Bari su mallaki Husna shiyasa ba tacewa Husna komai ba inda Amal ta Riko ta tana Bata hakuri Akan ta tsaya amma da sauri ta fizge hannunta ta fice daga gidan tana sheka kuka. Inda shima ya bi bayan ta aguje amma ya na fitowa yaga har ta shige napep sun harba.

Da sauri ya dauko makullin motar shi ya bi bayan ta Amma ga mamakin shi har masanawa Bai hadu da napep din da ta SHIGA ba duk irin gudun da ya sheka.

Da sauri ya SHIGA gidan ko gaisuwar kirki basuyi da hajiyar ba ya Soma wara idanu da son ya hango ta Amma ko Mai Kama da kyallin ta Bai hango ba inda hajiyar ke tambayar shi lafiya ta ganshi Haka firgice?

“Hajiya ina Husna? Wace Husna kuma ? Husna dai hajiya yanzu ta taho fa.

“Bata Zo Nan ba gaskiya koma dai ko kun samu sabani. Da sauri ya koma gida Amma babu Husna Babu dalilin ta Bai tsinke ba sai da ya karade duk inda ya San zai sameta Amma bataje ba.

<< Hawaye 38Hawaye 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×