Skip to content
Part 44 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Cikin mutuntawa haj ta karbeshi suka gaisa tana ta dire mishi Ruwa da lemu har ma da tarin soyayyen Naman Rago na layya Domin kuwa Raguna biyu ya aikowa hajiyar ta na ta zuba godiya da shi Albarka.

Shi da kanshi yaji nauyin maganar da yazo da ita ta neman Auren Husna Amma da Yake yaci ya gyargyare sai ya girgije ya sunnar da Kai kasa inda har hajiyar ta Gane akwai magana a Bakin shi ta Kuma tambaye shi

“Yayane Aminu ko akwai wani Abu? Ya Kuma Rusunawa Yana kalailaice murya shi a Dole ladabi
“Wato haj wata magana ce ke tafe Dani sai dai ban sani ba ko Zaki fahimce Ni?

“Yanzu har akwai wata magana Aminu da zakayi zaton ba Zan fahimce ka? Ai kazama Dan gida a gareni Aminu Kai din ai Dana ne.

Yayi murmushi Yana fadin “Wannan Haka yake hajiya dama nayi wani tunani ne Akan husna da irin mijin da ya Dace ya karbi Auren ta da duba Raunin ta Amma sai tunani na ke hakaito min wannan mazan na zamani marasa Amana Amma dai daga karshe sai nayi tunanin tunda akwai Auren tsakanin mu nine yafi Dacewa da Auren Husna shine nake zaton kamar maganar zata Zama abin Indo Ina Aisha.

Ita kanta hajiyar taji wani gingirin Amma da Yake Allah yayi Mata masifar son Abun Duniya sai ta watsar da hasaso son Uwar Husna da mutumin dake gabanta yayi ikirari Kuma yanzu da Yake Dan akuya ne ya Kuma dawo Yar Yake so ba tare da ta San cewa Halima ma a yanzu duk wani ibtila I shine ya jefata a ciki ba amma da Yake ya kware da yaudara sai ya siye bakin tsohuwar har bata iya juya baya ga bukatar shi.

Hajiya tayi murmushi tana fadin, “Kai Aminu ka cika mutumin kirki Wallahi Anya kuwa a yanzu Akwai irinka? Wane irin gata ne yafi wannan? Wallahi na yarda Aminu in yanzu ka shirya Auren Husna kazo a daura ai babu wani Abu me wahala ai ka wuce Haka a wuri na Wallahi. Wannan ai mu kayiwa Aminu.

Amma shine kake ta noke noke Yayi murmushi Yana fadin ya gode Amma ta tsara lokacin da take ganin ta shirya don shi Yana tausayin maraicin Husna ne shiyasa har yayi wannan tunanin don Mata a yanzu suna Shan wahala wurin mazan Aure shi Kuma baya son Husna ta Sha wata wahala a Rayuwar ta. “Kar ka damu Aminu Shirin ka shine gaba da komai idan yanzu ka shirya me zamu jira? “To hajiya a barshi Nan da kwana talatin. “An gama, Cewar hajiya.

Ya dire Mata kudi masu auki a zuwan barka da salla kafin ya taso ya taho hajiya na ta bare bare inda tayi shiri ta nufi kurfi ta sanar dasu maganar Auren Husna suka Kuma yi na am da maganar haj ta dawo tana matsar HAWAYE Wai na tausayin halin da Halima take ciki ko amace ko a Raye? Har gashi Allah ya kawo lokacin Auren Husna Amma Halima ta faku.

Tun daga wannan Rana Alh Aminu ya budewa hajiya kulu bakin aljihu Wai tayiwa Husna siyayyar kayan Aure tunda ko ba shi zata Aura ba shine Dole yayiwa Husna kayan Aure. Ai kuwa hajiya ta SHIGA sissiyo Kaya ba tare da Husna ta San bikin da akeyi ba.

Ita kuwa Amal tun daga Ranar da ta samu lambar Mai Kano ta kasa Zama lafiya kusan kullum tana faman Kiran shi ko tura mishi sakon text message na fatan alkhairi wani lokacin in ta Kira ya dauka wani lokacin Kuma ya share Kiran Amma duk da Haka ba ta hakura ba kamar dai yanzu da take ta faman Kira yaki dauka. Ta dubi Husna fuska a kwabe kamar zatayi kuka, “Yaki dauka Husna Kira min don Allah da Taki wayar, Husna ta Kira shi bugu Daya Tak ya daga inda ta mikawa Amal ta karba da sauri tana fadin, “Yaya Mai Kano Ina wuni? Tuni ya dago da manufar Amal abinda yasa Yake share Kiran ta don ko Matan.

Duniya zasu Kare babu abinda zaiyi da jinin mutumin can tsanar su Yake ji tamkar yasa bindiga ya harbe su….”Kana ji na kuwa Yaya Mai Kano? Ta katse shi da fadin hakan

“Wai wacece ne ta dameni da Kira ? Ba Husna bace ne? “Nice Amal Yaya Mai Kano don Allah Kar ka kashe min waya ka saurare Ni don Allah Ina da sakon da Zan baka.

“Ki fada mishi in ma shi ya Baki sakon Ni Zan iske shi ya fada min idona da nashi tunda na gama sanin waye shi..

“Babu fa Wanda ya bani sakon Nan Mai Kano sai zuciya ta don Allah ka fahimce Ni Wallahi tun Ranar da na ganka Mai Kano zuciya ta Taki ta barni na zauna lafiya. Ban taba Jin son wani namiji in ba Kai ba Zan Roke ka don Allah don Annabi kayiwa zuciya ta gata ka karbi tayin soyayya ta. Bata San ya jima da tsinke wayar ba sai da ta gama fallaso sirrin zuciyar ta taji shiru inda ta duba taga Ashe tunda ta sanar dashi son da take mishi ya tsinke wayar, Sai kawai ga HAWAYE na zarya a fuskar ta, Tausayin ta ya Kama Husna ta…

Soma Bata hakuri. “Husna so baya Jin Rarrashi baya Kuma bukatar hakuri abinda kawai so ya sani a karbeshi a kula dashi ko da hausawa ke cewa in so cute ne hakuri magani ne ko kusa cutar so hakuri baya iya maganin ta in ma nace zanyi hakuri to mutuwa kawai zanyi don Haka bar hakurin Nan Husna Zan nade habar zani na har sai Naga nayi bajintar da Yaya Mai Kano ya Zo hannu na a matsayin mijin Aure na.

“Kice Zaki mutu ne a gwauruwar ki don in dai Ina numfashi Babu ku babu jinin Halima…. Kai Ni Kam na shuga uku na lalace Wai ta ina na kuskure da har ahalin Halima yake bibiyar Ahalina? Cewar haj wasila da ta gama Jin abinda Amal ke fada.

Amal ta dubeta fuska sharkaf da Hawaye. “Mami in dai ba son ganin gawata kike a gabanki ba don Allah Kar ki shata layi tsakani na da Mai Kano kin kuwa San zafin so? Kefa da Bakin ki kikace hada ku akayi da Daddy. Dau ta wanke Amal da wani Mari me shiga jiki.

“Bari na fada Miki Amal na Rantse Miki indai Mai Kano kike so to ba Zaki Aure shi ba ko bayan Raina kuwa ba Zan bar wasiyyar ki Aure shi ba yadda nayiwa Halima zarra a komai to Ina nufin a komai nayi Mata fintin kau ko shi wancan da Yake Rawar jiki zanga gidan uban da zai tabbatar mishi da mafarkin ido biyun da Yake hasashe. Ta fada na nuna muhsin da yake shigowa a mota saboda yanzu ya dawo daga wurin aiki.

Husna da jikin ta yayi sanyi ta Kama Amal ta kaita daki kafin ta fito wurin Yaya muhsin dake dakon zuwan ta inda Kuma Ashe Safina taga shigowar shi itama ta taho cikin salon daukar hankali Wai zata tarbeshi sai gasu sunyi taho mu gama da Husna inda Safina ta rungume muhsin cikin ba zata don baiyi zaton hakan ba inda ya shako wani masifaffen turare Kan kace me kanshi ya Soma juyawa inda Kuma Safinar Taki sakin shi shima cikin wani madaukakin mamaki da ya Kama Husna sai taga ya kankame Safinar har Yana Shirin Kai bakin shi da sunan kissing din ta inda taja shi suka nufi sashen su abinda yasa Husna Hawaye har ta kwasa aguje zuwa daki ta iske Amal dake kukan so sai suka taru suka yi ta abun su aka Rasa me Rarrashin wani.

<< Hawaye 44Hawaye 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×