Skip to content
Part 45 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Safina da take Jin yau din tamkar Ranar salla saboda farin cikin tarkon ta ya Kama tana kankame da muhsin Yana Jin wani Abu a zuciyar shi me kama da bugawar zuciya Akan Safina wadda Yake bawa hot kis ita kuwa sai wannan irin ikon Allah takeyi har ma tafishi iya soyayyar don Babu wata kunya a tare da ita bare Kuma ga Wanda takewa kulafucin kauna

Dabara ta Fado Mata ta maganin da akace ta zuba mishi a abinci don Haka sai ta zare jiki tana fadin ya Bari ya ci abinci.

Ta nufi kichen ta hado abincin ta kuma barbade shi da tarin magungunan hatta lemun da Ruwa sai da ta zuba makaman Aiki ta nufoshi cikin takun salo da firirita inda ya bita da kallo tamkar sakarai

Ita da kanta ta Soma Bashi abincin a Baki tana kashe shi da firar manta kowa sai ni.

Idon shi Akan ta yanajin tamkar mayen karfe na janshi zuwa ga Safina sai da ta tabbatar yaci abincin Sosai ya Kuma Kora Ruwan lemun kafin ta hada mishi Ruwan wanka inda Kuma kafin shigar shi ban dakin yaji ciki na juyawa har ya Dan Runtse ido saboda yadda yaji cikin na kartawa

Shigar shi ban dakin yayi daidai da kelaya uban Amai tamkar zai Amayar da Yan cikin shi sai Kuma Kai ya SHIGA juyawa inda ya dafe bangon toilet jiri na Shirin zubar dashi a kasa.

Bayan ya SHIGA ban daki ne ya bawa Safina damar daka tsalle tana murna kafin ta jawo wayar ta ta bugawa Uwar ta tana fadin.

“Mama Albishirin ki? Bata Bari maimunar tace goro ba ta Dora da fadin,

“Wallahi na yarda wannan turaren hatsabibi ne ai mutumin ki yau yazo hannu Wallahi in Gaya Miki yacika cikin shi da abinci Wanda yaji makaman Aiki Domin kuwa shakar turaren da yayi yau har hot kis ya bani.

Guda me tsananin karfi Anty maimuna ta rangada tana fadin, “To maza maza kiyi turaren Nan na tsuguno ki Kuma matsa wannan da na fada Miki duk kiyi ta Haka Dan banzan zai Zo hannu.

“Ai Yama Zo wallahi don Baki ga irin kallon da Yake bina dashi ba.

“To ba samun miji ba ki shanya Baki ke Dadi soyayya ki nemi ya Baki kudi don Sai munyi hakan ko zamu cimma buri Kar ma ki sake ki yarda dashi sai ya dire Miki masu nauyi tunda dai mukayi sa a yazo hannun ai shikenan don Baki nemi kudi daga gareshi ba gidan Uban wa Zan samu kudin karbo Miki wani taimakon?

“Mama da kinyi hakuri har yasan wacece mace tukuna zaifi saukin kamu amma yanzu da zuwan wannan damar kamar munyi azarbabi.

“Ke dai ballagaza ce wallahi aka fada Miki maza na da dadine ko da gishiri? Idan Kika biyewa soyayya Zan kawo idanu na zuba Miki na Kuma barki da Yaya wasila ki gani idan Zaki iya da ita.

“To Zan jaraba. Ta fada daidai da fitowar muhsin daga bandakin Yana tafe Yana layi don shi da kanshi yasan baya cikin hayyacin shi inda Safina ta taso da sauri tana Riko shi tana Kara narkewa ajikin shi Amma sai ta kula bai san tana yi ba.

Akan kujera tree seater ya zube yana mayar da numfashi kafin ya Kuma kecewa da Amai inda kuma Safina jiki yayi sanyi don ta tabbatar yau burin da take kokarin cikawa ya hadu da tazgaro don Haka sai haushi ya kuleta ta shige daki ta barshi kwance akan kujera Yana mayar da nunmfashi.

Amal da taga kukan su ita da Husna ba zai kawo musu mafita ba sai ta takawa nata burki har tana tambayar Husna abinda yasata kuka inda ta fada Mata abin mamakin da ya faru Akan idonta tsakanin Yaya muhsin da Safina Wai har Yana Shirin Kai bakin shi ga na Safina da sunan kissing.

A zabure Amal tana dafe kirjin ta tana zaro ido.

“Ina zaton wani Abu fa Husna Safina da Anty maimuna sunyi wani furuci da zai alamtawa me tunani zasu biyo ko ta kasa Amma tashi muje sashen nasu Naga abinda ke shirin faruwa.

Da sauri suka Isa sashen Nadu inda suka ci karo da Yaya muhsin ya fado daga saman kujerar Yana ta matsar ciki Alamar ciwon ciki Yake Kuma cikin Aman da yayi ya fado din don Haka aguje Amal ta nufi sashen haj wasila inda kuma husna ta Soma kamo shi suka zubawa juna ido shi Yana ganin ta da wani hazo hazo ita Kuma tana mishi kallon tausayi.

Haj wasila da Amal suka shigo aguje inda haj wasila ta tarairayo muhsin suka fito dashi inda Amal ta fito da mota suka nufi Asibiti.

Cikin ikon Allah ya samu har ya Soma dawowa hayyacin shi inda Kuma ya zubawa Husna ido Yana kallon ta har dai ya Miko Mata hannun shi ta karba ta rike.

“Me ke faruwa Dani ne darling? Wani Abu Mai Kama da mafarki ne na gani darling me ya kaini? Bana fatan sake kwata hakan duk wannan din ma ban San yadda akayi hakan ta faru ba wani Abu ne me kamar tilas ko Dole.

“Kana ADDU A kuwa Yaya muhsin? Barin ADDU A fa tamkar sakin wani layi ne Mai muhimmanci a Rayuwar bawa. Haka kuma komai zai iya faruwa indai babu wani shamaki.

Ya zuba Mata ido don har ga Allah baiyi ADDU A ba lokacin da lamarin ya faru don Haka tuna Akan gadon Asibiti ya Soma tuba ga Allah ya Kuma daura damarar yaki da shaidan makiyi na ZURIAR ANNABI Adam

Ita kuwa haj wasila ta cika ta Akan wannan wulakancin na Safina da tasan muhsin Bai lafiya Kuma Bata sanar da wani ba yanzu inda Husna Bata fadawa Amal hakan ba da shikenan sai dai ya mutu a nufo ta da gawar shi?

Ta kwalawa Husna dake gaban gadon muhsin Kira ita da Amal.

“Wai ya akayi har hakan ta faru ? Ta tambaya tana kallon Amal da Husna.

Husna ta fada Mata yadda sukayi taho mu gama da Safina lokacin da ya dawo har zuwa inda suka rungume juna Yana kissing din ta.

“Yana nufin ya Fara son Safina kenan? Ni zai watsawa kasa a ido?.

Sai ganin muhsin tayi a Gabanta. “Wallahi Mami ban San yadda akayi na tsinci kaina da hada jiki da ita ba. Abinda kawai na iya Rikewa shine na shaki wani turare me masifar hawa Kai tun daga Nan ban Kuma sanin inda kaina Yake ba sai dai na farko na ganni Akan gadon Asibiti.

“Zan kuwa ci kan bara ubar Safina da maimuna don na gano karatun nasu. Ta Mike da sauri ta na yafa gyalenta ta fito inda Amal ke Ruko ta tana fadin . “Mami ki Rabu dasu don Allah tunda Allah ya nuna ikon shi Akan Yaya muhsin din.

Dau ta haskawa Amal din Mari. “In Rabu dasu kike cewa don ubanki su nemi kashe min yaro kina maganar na bar su? Wancan Auren yau ya gama kwana guda Daya Tak a Duniya Zan kuwa CI uban maimuna da Safina.

Ta SHIGA mota ta figeta aguje ta nufi gidan.

<< Hawaye 45Hawaye 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×