Safina Bata San lokacin da su Amal da Husna suka shigo ba har zuwan haj wasila da ficewar su dashi zuwa Asibiti duk bata sani ba saboda tsabar haushi da takaici na Rushewar burin ta dole ta kwana juyi da tsinewa ciwon da ya kawo mata tazgaro akan muhsin.
Washegari ta sheko wanka na neman fitina inda take godewa Anty maimuna da ta samo Mata turaren Nan tunda dai tayi me wahalar wato samo zuciyar muhsin ai ta gama Babban aikin ciwo kuma yayi ya gama.
Ta fito inda ta taka Aman da muhsin yayi a Daren jiya sai kawai. . .