Skip to content
Part 5 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Fitar shi gidan kai tsaye yanufi hanyar fita wajen gari . Tafiya Mai nisa kafin ya iso kofar wani gida Wanda Yake shi Daya kwal acikin dajin sai dai tafiya kadan zakayi zaka taras da wani karamin kauye Mai suna Taka Tsaba. Ya faka motar ya fito ya shuga gidan mai dakuna rututu. Amma Kuma gidan yafi kama da kufai don mafi yawan dakunan gidan kofofin su zubo wasu kuma tagogin sun rufzo, filin tsakar gidan kuwa babu komai fetal Yake sai wata tsohuwar Rijiya. Kai tsaye ya nufi wani daki wanda ke sake da labule ya danna kanshi babu ko sallama. Wani mutum ne me kwalkwalan idanu sai dai ba idanun nashi ne abin mamakin ba sai yadda kafafun shi suke a lauye tamkar an nade tabarma ko an nade alkaki. Kayan jikin shi sun hade saboda datti bakinshi cike da dabzar goro. Kazanta dai zuryan.Babu komai acikin dakin sai kwarya dake gaban shi sai Kuma wasu sassa na jikin namun dawa irin Kan kura me cike da wasu ciyayi da fatar damisa da su hauren giwa da kafafun wata dabbar Mai Kama da Zaki.


Alhaji Aminu ya dire agabanshi Yana kirtar kasumbar shi. “Lauje kace kana son ganina? To gani fada min abinda Zubainar ta sanar dakai in har ta hado da matata da Kuma ya’yana to ka Gaya mata ba zanyi ba an Dade ba a tashi Al kiyama ba.

Lauje yayi Dariya kafin ya furzar da tukar goron shi Yana fadin”Ai kuwa in aka tashi Al kiyama yanzu Aminu ai ansha damu . Ya Rufe kwaryar dake gaban shi da faifai kafin ya dubi Alh Aminu.

“Waye Muazu a wurin ka? Ya dubi lauje da mamaki yadda akayi yasan Muazu. Amma da ya tuna Lauje na iya hango abinda me ciki zata haifa. Haka kuma abune mai sauki lauje ya gano ranar mutuwa sai ya aje mamakin shi gefe ya kuma amsawa laujen.

“Mu azu abokina ne tun na kuruciya. Mutum ne Mai tsentseni tunda nayi kudi ma ya janye jikin shi gareni dama shine me sadar da zumunci tsakanin iyalan mu kasan ni ban faye shiga shirgin mutane ba”.

“To jinin shi Zubaina ke bukata don Haka sai ka kawo Mata don ku zauna lafiya…

Yabi lauje da kallon Anya hanyar Nan me bullewa ce? Ganin ya yiwa lauje kuri da ido yasa laujen cewa

Ba fa Wasila aka ce ka kawo ba don nasan duk duniya babu mace a idonka sai Wasila….Lauje ya fada Yana shekewa da Dariya.

“Banso Zubaina ta sako min Muazu cikin tafiyar Nan ba. Mu’azu bai mori komai acikin kudina ba bare nace jinin shi ya zama Madara. Asalima Ni mu azu ya wahaltawa a lokacin kuruciya…”

“To kana iya bada jinin Wasila in yaso sai a kyale shi mu azun. Lauje ya fada cikin salon gatse ko arashi.

Ya dubi lauje.

“Wasilar ma zan iya badawa in dai anzo gabar da zanyi haka. Dan iska kake min gatse.

Yaja tsaki kafin ya mike yana shirin ficewa lauje ya kuma jaddada mishi cikin satin nan ake son jinin Muazun. Wanda sai an bashi wani abu ya karba daga hannun shi Aminun kafin ita Zubainar ta isa ga Muazu ta zuke jinin jikin shi. Ya fice ba tare da ya tankawa Laujen ba.

Ya iso gida zuciya na mishi turiri. Tana zaune a falon hannunta rike da Remote control tana saita tashar arewa Amal na home work muhsin Yana cin abinci. Ta dubeshi ta watsar inda yaran ke mishi sannu da Zuwa ya anmsa Yana cewa Haj Wasila ta bashi Ruwa.

Kamar ba zata tashi ba shima har ya kosa suka Mike a tare zuwa wurin fridge din inda ya dakatar da ita.

“Barshi Nagode. Ya bude ya dauko Goran Ruwan faro ya dawo ya zauna Yana cire hular shi Yana kallon Wasila dake cika tana batsewa hankalin ta akan TV Amma ya San ba TV take kallo ba hankalin ta Yana kanshi. Yana zaune Yana amsa wayoyin mutane Akira ko shi ya Kira har su Amal da muhsin suka fice ya rage daga ita sai shi ya dubeta. “Wai Halima kuwa tana zuwa gidan Nan?

“Wace Haka? Ta tambaya tana kwabe baki. “Matar mu azu nake nufi. Ya Bata amsa.

Ta yi mishi kuri da ido ta dade tana kallon shi kafin tace. “Uhum baka san inda take bane kake tambaya ta? “Na sani Mana ai naga kamar kawarki ce shiyasa na tambaye ki. Shiyasa kuke faduwa jarabawa ana tambayar ki kina wani bawa mutum nonses answer.

“Ai naga kamar mijinta shine abokin ka shi ya kamata ka tambaya ba matar abokin ba.yaja tsaki ya Mike tabishi da kallo taba fadin. “In ma dai ga Halimar ta raya maka sai dai ka mutu da bakin ciki ko kuma ka taya watakil shi Mu’azun ya saketa sai ka Auro Ni Kuma nace karya kenan.

Ya juyo Yana kallon ta don ya fahimci zaurancen da take mishi. Wai tana nufin Yana son Halima? Sai kawai ya shige ciki ya barta tana cancana maganar.

Ya Dade a yau bauyi barci ba saboda sabon lamarin da Zubaina ta ballo mishi na jinin abokin shi koma ace aminin da ya zarce dan Uwa wato Muazu. Amma da ya hada uku da biyar sai suka bashi takwas.

Ya kuma hada shahara da Amincin su da Muazu a mizani sai yaga shaharar ta rinjayi Amincin. Dole ya sallama ya kuma zabi shaharar har zai mika jinin Muazun ga Zubaina. Washegari ya cika mota da abin Arziki buhun shinkafa da carton din taliya da macaroni da duk wani abu na dangin kayan masarufi ya nufi gidan Muazun dake unguwar Rafin Yan wanki.

<< Hawaye 4Hawaye 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.