Skip to content
Part 55 of 76 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

“Shine kika tsaya kina kuka shabe shabe har da Hawaye haka?

“In ban yi kuka ba me zanyi saboda Allah ko bakiji nace Miki shegiyar matar can tayi wa mijina Aure da wannan yarinyar Mai Kama da agola ba?. Har zuwa yanzu fa mama muhsin Bai karbe Ni a matsayin matar Auren shi ba Ina ma na ganshi Yana can hankalin shi na wurin Husna kuma Babu Wanda ya sanar Dani zaiyi Aure sai a Bakin Amal nakeji.

Anty maimuna ta Rike kugunta tana cizar leben ta cikin takaici kafin ta cewa Safina, “Bari naje wurin wasila naji Ashe har kiyayyar ta Kai Haka na nasawa ayi Miki kishiya?

Ta fice fuuuu Safina na biye da ita har sashen haj wasila tana zaune sai ganin su tayi kamar an wurgo

“Ashe kiyayyar da kike Mana har takai haka wasila da har kike saka muhsin yayiwa Safina kishiya? Me ya hana kice ya sauwake wa Safina Auren shi sai ku huta.

“Dama shi ya Auro ta? Ai ya ci ace Kuna ganewa ke da Safina kun taba ganin kafar muhsin ta tako kofar gidan ku da sunan yazo wurin Safina? Ai bana ce ya yi hakan ba Uban shi ne yayi hakan idan yarki ta gaji da zaman Rashin yanci ai tasan hanyar gidan ki Kuma ba Rike ta nayi ba idan Kuma kece Kika gaji duk hanya a bude take dama ai ban Rufe Miki ba na fada Miki tunda burin ku na Auren muhsin ya cika sai ku jira cikar nawa na fiddo muki ita Ashe Baki lura nawa burin ne ke dab da cika ba? To Kar ki Kuma sako Ni a lamarin ku ai Baki ganni lokacin hadawa ba bare yanzu lokacin Rabawa. Kuma da kike maganar kiyayya ni kuwa in ki ku ace naki wa? Maimuna fa kike sai Yar ki Safina Baki lura nice uwar muhsin ba da kuke wahalar da kanku Akan shi? To muhsin ma ban tunanin Yana kawowa Ran shi wata aba Wai ita Safina don Haka garzaya wurin uban muhsin ku gyarota duk yadda kukayi yayi daidai ai dama dashi kuka Saba kullawa da kwancewa ba Ni wasila ba da na zamo Yar bakin ciki da Hana Ruwa gudu.

“Ai kin gama magana Kuma yau din Nan in Sha Allah Zan wuce da Safina muhsin kuwa ba dai shi ba dai Zama da wata mace da sunan matar Aure ba sai dai ko dadiro ko farka tunda abun duk ya biyo ta hanyar Rashin mutunci to wasila ki Rubuta ki aje Ni da Safina Baku ci Mana mutunci a banza kowa ya Hana uwar shi barci shima kuwa ba zai Runtsa ba Wallahi ke da muhsin sai kun gane kaza Tara ta Isa layya indai ba fata ake son gani ba idan kuwa Haka ba ta tabbata ba kice ba maimuna ne sunana ba.

Ta finciki hannun Safina tana fadin, “Tashi muje anyi nasara Akan mu a wannan karon Amma ba nasara bace faduwa ce kasa warwas.
.
“A a mama ki barni don Allah Kar ki kashe min Aure ke dai ki Kara min kokari yadda Za ayi na samu muhsin.

Wani Mari me shegen zafi Anty maimuna ta kwadawa Safina.

“Don ubanki duk wannan cin mutuncin da Uwar muhsin tayi Miki ta Kuma yi min shegen danta Yana makale Aran ki? Ai nayi zaton ko da gwal aka kera muhsin Kya barshi Kuma ko da shine autan maza Amma shine kike neman nuna min kinfi son shi da Ni?

To idan kin zabi zaman rashin yanci zan zame hannu na in barki da masu son ganin kukan mu . Faduwa akasa tashi itace faduwa Amma idan har an tashi to nasara ce.

“Ni dai ki je mama Amma gaskiya yadda nake son muhsin ba Zan iya Barin shi ba mafarkai na sun Sha nuna min Rayuwar mu har da yaran da muka Haifa don Haka in ma Baki Nemo min taimakon ba Ni Zan nema da kaina da Kuma kudi na.

Haushi da ya Rufe Anty maimuna Bata San lokacin da ta Rufe Safina da duka ba, “Shegiya ke Kam da Kika Sha NoNo na furzarwa kikayi ba Hali na bane naci da kwakwa to ko Kare ya cinye zuciyar ki sai kin bar muhallin Nan tunda ba Rahama suke Rabawa ba.

Sai taja Safinar tamkar wata Yar yarinya Haka suka fice Anty maimuna na kumfar Baki da takaicin Safina. Kwana biyu Safina agida inda ta samu sa ar Anty maimuna ta fice ta kuwa koma gidan don ita Kam ba zata iya Barin muhsin ba inda Kuma ta nemi kawar ta siyama wadda akewa lakabi da siya suka SHIGA neman taimakon da muhsin zai dawo gareta inda siyar ta bata shawarar kawai ayiwa muhsin kiranye in yaso idan ya dawo sai a Dora aiki me shegen zafi Akan shi Wanda ko yaki Allah sai ya so Safinar ya Kuma zamo Mata bawa. Haka suka zube kudi aka Fara Aiki ta dawo gida tana jiran dawowar muhsin.

Ranar da Alh Aminu yaga gidan da su Mai Kano suka yada zango a Ranar ne Kuma ya Kira Yan ta addar shi da son su Zo gidan da ya Basu kwatance akan shi dai Mai Kano su fille kanshi suyi gunduwa gunduwa da jikin shi inda Kuma yace ita Kuma Husna a dauko mishi ita a kawo mishi da Haka ya tura Yan Aiken shi ya zauna zaman jiran dare don yasan yau din Nan Husna zata Fado komar shi inda ya kagu ya Soma da biyan bukatar Zubaina tayiwa Husna ciki don ya bawa Zubainar tayin dake kwance cikin Husnar

Me Kano da Yake kallon Husna a cikin napep din haushi ya kume shi yayi nufin narkawa husna dukan Shan gishiri Akan yadda take nacin son muhsin sai Kuma ya tuna maraicin ta ko ga Halima soyayyar Husna daban take kasancewar ta ita daya kwal cikin maza Hudu don Haka sai yayi Mata uzuri Kuma yadda muhsin yaso tafiya da ita ta nuna ba zata bishi ba sai da izinin shi inda taso tafiya ai da Bai iske ta ba Kuma ta fada mishi ba zata bar mahaifiyar ta a halin ciwo ba ta bishi don Haka sai ya kyale ta har napep ta sauke su a kofar gidan malam Abdulrazak suka shiga inda suka samu Salma Yar Amana tana kwancewa Halima kanta inda Kuma malamin ya Basu izinin tafiya gida sai dai a Rika Zuwa ana karbawa Halima Rubutu da magunguna.

Mai kano ya biya shi duk abinda ya bukata ya Kuma yi mishi godiya da Haka suka hado kayan su suka fito daga gidan inda Kuma Mai Kano ke tunanin Kai Halima shin tsohon gidan su ko kuwa ya Kama musu haya? Don Bai yarda da ya bar Halima ita kadai ba saboda tsoron sharrin Alh Aminu Haka Kuma Bai yarda ya kaita wurin hajiya ba.

Salma ce tace ya Bari su wuce gidan su kafin ya tsaida shawara sai su zauna a dakin ta . Da wannan ya yarda sai dai ya tambaye ta. “Salma Baki ganin akwai matsala akan matar Nan Adama?

“Kar ka damu babu wata matsala Ni ce kawai Zan iya yarda da mulkin ta Amma ba Zan Bari tayiwa mama ko Husna wani Abu ba Kuma ai tasan Kai din ba zaka yarda ba. Da haka ya Raka su har gidan inda ya nemi amincewar Adama.

“Kai wannan iskancin ku Mai lasisi kukeyi har ka jajibo uwar ka ka Mika Mata ? To Bata sanar da Kai Nan gida na bane ? To ban yarda Uwar ka ta zauna min ba sai dai ka biya zaman da zasuyi tun daga yau har zuwa lokacin da zaku Gama sheke ayar ku ku tafi.

“Zan biya ko nawa ne Kar ki damu ya zura hannu aljihu ya fito da kudi dubu goma ya Mika Mata yace sauran idan yaga adadin zaman da sukayi zai cika Mata.

Sai da ya aje musu komai na bukata kafin ya zube Agaban Halima Yana fada Mata zai koma Legos ya Kuma yi Mata fatan samun lafiya. Tayi murmushi tana shafa kanshi tana nuni da hannu Alamar Allah ya bashi Dace da nasara.

Sai yaji kamar Kar ya tafi ya bar Halima musamman saukin da tasamu yau yafi na ko yaushe Amma Dole ya tafi saboda ana ta Kiran shi. Da haka ya tafi Yana farin ciki.

Yayin da Kuma Yan Aiken alh Aminu suka dira a gidan malam Abdulrazak suka Kuma tako Rashin sa a babu Mai Kano babu Husna Dole suka koma suka sanar dashi.

Washegari kuwa ya Isa ga lauje Yake sanar dashi abinda Yake faruwa.

<< Hawaye 54Hawaye 56 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×