Halima na gindin injin makarde tana markaden waken Awara, Mubarak da Zaidu suka fito cikin kayan makaranta suka fice amma bata ga keyar Mai Kano ba. Don haka cikin sauri ta karshe makarden ta kashe injin din ta nufi daki.
Yaron dan kimanin shekaru sha biyu yana ta dininiya don dai kar yaje makaranta ya jawo wannan ya saki ya kamo wannan ya saki.
Ta daga labulen tana kallon shi. "Sannu uban shiririta kowa ya tafi sai kai kadai me kuma kake jira?
Ya jawo jakar makaranta yana fitowa har ya kusa ficewa sai kuma ya dawo.
"Yauwa Mama dama. . .