"Koma waye Kika Kira Bai Isa Raba wannan Auren naku da Alh Aminu ba mutuwa ce kawai zata Raba shi Wallahi Amma ba dai Dan Adam ba.
"Sai mutuwar ta Raba ai in na kashe shi Kuma Wallahi ke Zan ce Kika bani wannan shawarar Kinga sai mu SHIGA kason tare dake ! Cewar Husna wadda tayi maganar da tabbaci Akan fuskar ta, Hajiya ta juyo ta dubeta, "Kikace me Husna? Itama ta dubeta tana Kara maimaita mata abinda ta fada.
"Cewa nayi idan ya mutu sai Auren ya Rabu don wallahi Zan kasheshi ne in Kuma mayar da maganar ta. . .