Skip to content
Part 7 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Kuka take rerawa cikin Alhini da jimami da tausayin kai musamman wannan rayuwa da mutanen cikin ta basu faye yiwa kawunan su adalci ba bare su yiwa wani. Lallai mutuwa itace takobin dake datse igiyar Jin dadi ko akasinta. Mai maida Mata zaurawa Mai maida yaro maraya. Duka daya mutuwa ke yiwa tambarin dake watsuwa.

Yaran suka taso makaranta suka iske mahaifiyar su ta tusa gawar uban su tana kuka suma sai suka dauka gida ya tabbata na mutuwa.

Kan kace kwabo gida yayi dankam da mutane. Tuni aka sanar da masu hakki wato dangin Mu’azu tuni Kuma aka hau shirya shi har aka kammala aka kuma fice dashi zuwa gidan shi na gaskiya.

Wannan fitar ita tafi komai tashin hankali ba kuma kowa ya san hakan ba sai wanda mutuwar ta doka.

Alhaji Aminu yazo don ko ba a fada mishi ba to zai zo sai kuma Halima ta kira shi take sanar dashi, ya kuma zo da kayan abinci da kudi yayi ta hidima har aka share makoki kowa ya watse ya bar Halima daga ita sai yaranta biyar. Babban cikin su shine Mubarak shekarar Sha biyar. Sai mai bin shi Zaidu shi kuma Sha uku sai mai Kano shi kuma Sha biyu ba kadan sai Husna ita kuma shakara tara sai auta Sulaiman shi kuma shekara shida.

Hajiya Kulu mahaifiyar Halima tace lallai ta rufe gidan ta koma can masanawa gidan ta tayi takaba.

“Ki yi hakuri Hajiya nan ina Sana a kuma dama karfin Sana ar ne da kuma ikon Allah ne kurum ke rike damu . A bari na gama takabar tukuna.

Haka Halima tayi takaba ta gama Alhaji Aminu na zuwa yana kawo mata kayan abinci da kudi ya kuma ce duk hidimar yaran ta karatu da ta komai ma ake sanar dashi.

Hajiya kulu kam tana jinjinawa kokarin Alhaji Aminu akan Halima da Ya’yan ta don itama tana samun rabon ta dama ido ce ga kudi

Mubarak da Zaidu suna karatu kuma suna kokari babu laifi akasin Mai Kano da sai yanzu ma Halima ta gano idan ta turashi makaranta baya zuwa sai dai ya nufi wurin Yan gwangwani ya karbi kudi yaje neman kayan nauyi

A yau duk su Mubarak sun dawo Amma shi bai dawo ba sai can yamma sai gashi ya dawo kayan shi makal makal da bakin Mai

Ta dubeshi cikin takaici. “Sai yanzu aka taso ku daga makarantar? Yayi fici fici da idanu.

“Ya Ina tambayar ka kana Kare min kallo?

Zaidu ya ce Mama dubi kayan shi fa daga Yan gwangwani Yake dama malamin su yace min kwana biyu Baya zuwa makaranta.

Wannan maganar ita ta fusata Halima ta kuwa cacumo shi ta Soma tsula mishi bulala…

“Wato abinda ka tsira kenan? In tura ka makaranta sai ka waske ka tafi neman kudi ko? Kuka Yake Yana fadin ba zai sake ba kafin ta sake shi tana tunanin kulafucin da yakewa kudi.

Bata Sha mamaki ba sai da ya kwanta bacci cikin mafarki yake maganar wadda ke nuna lallai da gaske yake son kudin.

“Dubu talatin a hada da Dubu Ashirin ba hamsin kenan ba? Ta dube shi tana zaune ta gama sallar kiyamullaili tana tasbihi yana lissafin kudin shi tana mamaki. Da ta gama tasbihin sai ta Roka mishi Ubangiji yayi mishi zabi na Alheri ya Kuma bashi kudi na halal ta Kuma Rokawa dangin shi Rayuwa Mai Albarka tare da nemawa iyaye da miji Aminci a makwanci ta shafa kafin ta kwanta

Washegari ta hada shi da Allah da Annabi akan yaje makaranta yace zaije.”yauwa Dan Albarka ba kaji malamin ku yace komai yaro ya Zama daga Uwar sa ne ba? Yayi saurin gyada Mata Kai…

Yauwa to kayi karatu inda uwace daukakar yaro zaka daukaka a Duniya kudi Kuma zaka samesu har sai kace baka so.

Fuskar shi ta yalwata da farin ciki ya amsa Yana murna da Haka take lallaba shi yau yaje makaranta gobe ya yaudare ta yaje tsintar kayan nauyi . Kamar yau dai da suka rabu akan ya tafi makaranta. Yayin da Sulaiman kuma yau ya tashi da zazzabi inda ta taho kawo shi Asibiti aka yiwa Sulaiman allura aka bashi magani suka juyo zuwa gida inda ta jiyo Husna tace

“Lah Mama ga Mai Kano. Ta juyo inda ta hango shi cikin gareji yana tara kayan nauyi.

“Yaya Mai Kano? Husna ta kwala mishi kira ya waiwayo suka yi ido Hudu da Halima. Suka yi kallon kuda ta daga mishi hannu alamar sannu.

Akace marar gaskiya ko a Ruwa zufa Yake da ya dawo sai ya toge a kwar gida inda Halima tace ya shigo.Ya shigo ta zuba mishi ido inda ta gane ba dukan ne abin yi ba illah nasiha da Addua. Don haka sai take nasiha da nuni.

Da Haka dai aka samu suka gama scondry school inda yace shi Kam Halima tayi mishi afuwa ya gaji da karatun Nan tayi mishi Addua neman kudi zaiyi. Har kuwa Halima tayi amma sai tayi mishi fatan Alheri Akan dukkan abinda yasa gaba yayin da Mubarak da Zaidu suka wuce A B U Zaria

Kwana biyu da yin Haka Mai Kano na zuwa Yan gwangwani Yana samo Yan kudin shi inda Halima ke kokarin sama mishi Yar tireda a kofar gida don ta dauke hankalin shi har dai ta hado kayan tana jiran ya dawo tayi mishi ba zata. Sai me? Wayar ta tayi Kara ta dauka inda tajiyo muryar Mai Kano na fadin

“Mama kiyi min Addua nabi motar kayan nauyi zuwa Legos sai na dawo. Hawaye ya ciko idonta Amma ta hadiye ta amsa mishi.

“Allah Ya tsare hanya Mai Kano ya dawo min da Kai lafiya yasa kayi gamo da Alheri ya baka halal dinka ya kauda idonka daga Haram

Ya amsa Yana Jin tausayin ta Amma yaji dadin Adduointa.

Kwana Daya kwana biyu uku hudu har tsayin wata guda babu Mai Kano daga ita sai sulaiman da Husna. Ta damu matuka da Rashin Jin halin da yake don haka ta lalubi layin da ya kirata Amma akashe Dole ta hakura ta bishi da Addua

<< Hawaye 6Hawaye 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.