Skip to content
Part 70 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Ya Gama Jin labarin da Laujen ke karanto mishi Wanda yayi matukar firgita shi har ya kasa sauke wayar daga kunnen shi. Wannan shine ga koshi ga kwanan yunwa . Ta Ina zai iya moruwa a wannan halin da Yake ciki? Muradin zuciya ma wato Husna Dole suke kwana wuri Daya su Kuma tashi Amma bashi da wani hurumi da ya wuce Runguma da kiss duk da har yanzu sakamakon likita Bai fito ba bare yaji matsayin sa. Shi da kanshi ya San ya nakasa nakasar da baya fatan ta kasance har karshen numfashi Amma Yana ji ajikin shi cewa ko ya warke ba zai taba dawowa daidai ba Domin kuwa Mai Kano Bai mishi yankan da zai warke ba Allah ma ya taimake shi da Bai mishi fit Daya ba.

Husna yaji ta Rungumo shi tana Ritso hannuwan ta tana kwantar da kanta Akan kafadar shi tana tambayar shi.

“Daddy me kake tunani ne? Ga mamakin shi sai yaji zuciyar shi ce kadai ke da kawa zucin yarinyar Amma gangar jikin shi Babu komai musamman body feels din da ya nakasa . Ya Rungumo ta shima Yana shafa fuskar ta amma babu wani feeling da ya Saba ji idan ya kawo yarinyar Aran shi. Ita kuwa Babu komai a idonta sai yarda da Amincewa Wanda zuciyar ta bawa yarda sai dai Bata sani ba sunyi hannun Riga da muradan zukatan su .

Bai iya fada Mata komai ba Akan wannan Bala In dake tunkaro shi da kuma harkallar su da Lauje sai dai kawai ya fada Mata Babu komai.

Goloko ya shigo Yana aje kayan da aka aike shi siyowa saboda shike jigilar siyo komai da nemowa ita Kuma Yar giwar ta zuba ko ta bayar koma ta shige jikin shi tana zuba shagwaba tana wasa da tsinin hancin shi ko kasumbar shi Amma shi Kam Babu wani feeling inda ya Gane maganar Mai kano da gaske Yake kokarin tabbatar da ita.

Likitan dake duba shi ya shigo Rike da wata doguwar takarda wadda sakamakon ya fito Amma Kuma sai ya iske Husna da goloko Wanda dokar aikin nasu kuma Dole a sirrin ta fadar matsalar mutum sai dai a kebeshi don Haka ya nemi ganin Alh Aminu Wanda ya Mike suka fita tare zuwa Office din likitan Wanda ya Soma sanar dashi abinda takardar ta kunsa Akan ciwon shi.

“Kaga likita gajarce min kawai ko baka fada ba nasan dai karshe kace min na samu matsala ko?

“Haka ne Alhaji saboda datsewar jijiyoyin dake da alaka.

Ya dagawa likitan hannu Alamar ya gamsu ya Mike ya baro office din gaban shi na sarawa da irin wannan Rayuwar ai gara ace ka mutu. Bai Kuma Kara kwana Asibitin ba ya ce gida zai koma duk da likitan Bai sallame shi ba ya sallamo kanshi Husna Kuma ta biyo shi inda ya kaita sardauna Estate don Bai yarda ya kaita inda Amal take ba wadda tunda taje yace ta dawo gida ba wani ciwo bane da zata yi mishi gayya Dole sai dai waya take Kiran shi ta tambayi jikin shi don Haka Bata San Husna zaman jinya tayi ba.

Shi kuwa Muhsin da yazo gidan Bai ganta ba sai yayi zaton ko ba Nan gidan tazo ba don Bai San Daddyn ba shi da lafiya ba sai da ya tambaye Amal take sanar dashi in da Kuma yaje Asibitin a Ranar da Alh Aminu ya baro Asibitin sai dai wayar shi ya Kira Amma yaki dauka ya jera mishi Kira yafi Akirga Amma Bai dauka ba Dole ya hakura inda Kuma wayar shi ta hau Kara yaga Alh Bello ne ya dauka Yana fada mishi Yana son ganin shi ya fada mishi inda zasu hadu don shima Yana son ganin Alh Bellon don ya ji Wanda Yake Kara Akan yiwa Yar shi fyade Yana fatan ya zamo sunane kawai ya zamo daya ba hasashen shi na mahaifi ba.

Shi kuwa Mai Kano da yaji shiru shiru Husna bata shigo ba sai ya fito ya Kuma iske wurin wayam babu kowa sai zuciyar shi ta kimsa mishi cewa muhsin ne ya dauke ta suka wuce katsina sai Ran shi ya Kara konewa ya dawo ciki Yana Zama gaban Halima dake cin abinci cikin nasarar da Aiki Yake yi zuwa yanzu komai nata yasoma komawa irin na mutane masu hankali maganar ta da ayyukan ta inda malamin yace duk wannan Yana daga cikin nasarar samun lafiyar ta Amma Kuma ba zai Hana ayi Mata Rukiyya ba saboda Raba ta da bakaken iskokin dake kanta shine zai Hana su waiwayo ta Amma idan ba ayi ba to ko yaushe suna iya dawowa. Halima ta dubi Mai kano tare da malamin tana gode musu da yi musu fatan alkhairi.

“Mai kano Wai Ina Yan uwan ka ne su Mubarak da Zaidu da Husna da sulaiman? Ya Bata amsa da su Mubarak dai suna can bautar kasa yayin da sulaiman Yake can Dutsin ma Isa kaita Husna Kuma tana can katsina.

“Ai kuwa Nima da an gama karatun Nan kamata yayi na koma can katsina ko? Ta fada tana kallon shi.

“To mama duk yadda kikace Haka za ayi Amma Ni zanfi son zaman ki anan garin.

Tayi murmushi tana fadin, To Mai Kano idan hakan kake so sai na zauna ai Amma to ka dauko Husna ka kawo min don ta taimaka min da wasu abubuwan kafin muga abinda Allah zai yi.

“In Sha Allah gobe zanje na dauko miki ita ya fada yana bare mata ayaba yana Bata ta karba tana saka mishi Albarka har ya gama ya Kuma Bata Ruwan Rubutu ta Sha ya Kuma shafe Mata kafafun ta da magani saboda katafun sun farfashe saboda tafiya da Tasha a kasa

Washegari ya nufo katsina da son keta Muhsin da Uban shi da har yanzu Basu kiyaye shi ba. Ya Kuma shigo garin Kai tsaye ya nufo gidan da zaton Nan zai samu Husna Amma sai Amal ta tabbatar mishi da tazo Amma Bata Nan wata Kil tana masanawa. Har ya juyo zai fito don muhsin Yake zargi da dauko Husna inda Amal ta biyo shi tana tsaida shi Amma Bai tsaya ba ya fice inda sukayi kicibus da muhsin din.

“Ina Husna take? Ya tari muhsin din da wannan tambayar.

“Wallahi Nima nemanta nake Amma nafi zaton suna tare da Daddy. Maganar gaskiya Husna Bata cikin hankalin ta Dole mu San abinyi Mai Kano.

“Zan nemeka kawai ya fada Yana wucewa don tunanin shi ya hasko mishi gidan Alh Aminu na sardauna Estate don Haka da sauri ya nufi can inda Kuma ya iske kofar get din abude ya tausa kanshi a ciki ya Kuma hango Husna tana ta jera kayan abincin da ta girka batayi aune ba taji saukar Mari a fuskar ta kafin yayi kwallo da ita ita da kayan abincin da take jerawa.

Ya dubi Alh Aminu Yana zare idanu.

“Yankan da nayi maka Bai gamsheka bane sai nayi maka ta yanke ta gundile? Ai Kai da wata mace sai dai ka kalleta wlh kuma ka sani yadda ka keta min haddi Nima Zan Rama wlh ba ka San cewa duk abinda kayi wa Yar wani kaima sai anyiwa taka ba? To ka Soma lissafi tun a yau daga Nan Kuma daga yanzu da na fita daga gidan Nan zanje na dauki Amal irin abinda kayiwa mahaifiyata Nima Zan dau fansa akanta Kuma har Riba sai na ci sai nayi Mata cikin da zata haife shi a gidan ka in yaso ka Rika kalla kana tunawa Dani da abinda kayiwa mahaifiyata abinda kayi min Nima zanyi maka.

Ya finciki hannun Husna suka fita zuwa gidan su Amal wadda bata yi gardama ba da yace zatayi mishi Rakiya da dokinta ma ta biyo shi.

<< Hawaye 69Hawaye 72 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.