Skip to content
Part 71 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Amal da ta taho da sauri ganin Mai Kano ya zuba Mata idanu yasa ta kusa hardewa ta Fadi saboda tsinin da idon shi yayi Mata har cikin jinin jikinta da bargo takejin kallon.

“Amal kiyi min Rakiya Mana saboda Ina da bukatar ki? Ta sunnar da kanta kasa.

“Ni baiwar soyayyar ka ce Yaya Mai Kano umarni kawai ya kamata ka bani ba shawara ba abinda yafi Haka ma zanyi maka shi matukar Bai Saba da Shari ar mahalicci ba ta fada tana kallon shi.

Har abinda ya Saba da Shari ar sai kinyi ubanki ne ya ja Maki za Kuma ki dawo mishi da Ribar soyayyar ki ! Ya fada Aran shi.

“Ok to shigo muje tunda har nayi sa a ke baiwar soyayya ta ce.

Ya fada Yana Mata wani yaudararren murmushi Wanda yasa ta fada Napep din tana Jin yau Kam kamar acikin Aljannah take.

Alh Aminu kuwa da Mai Kano ya fadawa zai dauki Amal ya bato Mata Rayuwa har da tsarabar cikin da zai Bata ya firgita shi kwarai don ko Babu komai yadda yake son Amal ko kanshi baya kauna Haka zai iya kiyaye Amal da dukkan karfin shi Koda kuwa zai Rasa tashi Rayuwar ne bare Kuma ace yau anyi ma Amal din ciki zuciya kawai zai hadiye ya bar Duniya don hakan yafi asaka mishi bakin bindiga a sakar mishi harsashi daci da Bakin ciki.

Kuma ko Babu komai haduwar su jinin shi da na Ahalin mu azu ai shine mutuwar shi duk da agefe guda Yana Jin dadin yadda Husna ta manta da Muhsin bare har ta kaisu ga hada makwanci sai dai Kuma ga wani tarnakin da ya doke wancan.

“Ina ! Ba zai yuwu ba ! Ya fada da amon murya, Ya Mike Yana SHIGA wani daki sai gashi da bindiga fistol Yar k’arama ya fito Yana Fadin.

“Kashe ka kawai zanyi don na kula hakan kake kokarin yi min to gara duk ku mutu har Yar Uwar taka tunda Bata da wani Amfani a gareni Kuma ba zanso ta Amfani muhsin ba ko ba yau ba in nayi hakan ai sai Naga gidan uban da dayan ku zai hadu da Ahalina.

A guje ya bar gidan Yana sharara gudu kamar zai tashi a sama tun a hanya Yake Kiran layin Amal akan Kar ta sake ta yarda Mai kano ya yaudara ta Amma sai ya samu layin akashe don Haka ya koma Kiran muhsin Wanda haushi da kishi ya Hana ya dauki wayar Yana kallon Kiran Yana shigowa Amma yaki pick haushi ya turnuke shi Dole ya hakura da Kiran ya karso gidan Yana Danna horn Amma sadin Yana ban daki shiyasa yayi jinkirin bude mishi get din sai da ya fito ya shigo Yana son ganin sadin don ya faska mishi Mari amma ya hango shi yana fitowa daga bandaki sai kawai ya wuce cikin gidan Yana kwalawa Amal Kira Amma shiru ta bashi amsa ya fito Yana tambayar Sadi inda Amal ta tafi.

“Yanzu kuwa ta fita me gida Bata Jima da fita ba.

“Ita da wa ta fita? Ya tari hanzarin sadin, “Ai ita da Husna ne sai Kuma wannan Dan uwan Husna inajin Mai Kano sunan shi.

Wasu Marika ya bashi guda biyu masu yaji Sadi har wata wuta yaga ta gilma yayi maza ya dafe kumatu.

“Ubanwa ya sa ka Bari suka fita? Ya fada Yana son shake sadin, “Me gida ban San inda zasuje bane da ban Bari suka fita ba Amma Bari na bi bayan su yanzu.

Ya fada Yana kwatar kanshi da kyar inda Alh Aminu ya Rigashi ficewa zuwa tashar mota Amma duka Bai samu ganin su ba wurin dawowa ne ya tuna da lambar Mai Kano yayi maza ya jawo ta ya doka Kira Amma Mai kano ya na ganin Kiran yaki dauka saboda suna dab da shiga jirgi Wanda yayi musu biking su uku. Husna na like da Amal wadda batajin ko dar Akan bin Mai kano sai ma wani farin ciki da takeyi na yau Wanda take so ya nemi Alfarmar ta duk da taso sanar dashi ta manto wayar ta agida Amma ta share har jirgin su ya sauka a garin Legos cunkus dakin tsumma Kai tsaye Kuma Mai Kano ya wuce dasu gidan da Yake zaune Akasin gidan sodangi

Komai Akwai na bukata ya Kuma cewa Amal ta kula mishi da Husna ko bandaki zataje ta Raka ta in ma zasu Bata to su Bata tare da Haka ya fice zuwa gidan sodangi ya dauko Halima ya Kuma shaidawa haj Laila ya kawo wadan da zasu kula da Halimar duk da zuwa yanzu Halima tana yiwa kanta komai sai dan abinda ba za a Rasa ba da Haka yayiwa haj Laila godiya ya Kuma yiwa Alh sulaiman Dan sodangi godiya shi da Alh Dan iro Wanda shine ya dauki nauyin maganin Halima kaff.

Suka taho Halima na tambayar shi haj ya sanar da ita tana nan lafiya Amma a zuciyar shi antakawa hajiyar Ashar Yake.

Halima taga Amal da Husna Amal kuwa ta Rungume Halima tana murnar ganin ta tana Mata barka da Arziki duk da Bata San komai Akan Halima ba abinda kawai ta sani ta Bata sai tayi zaton ko gano ta da akayi ne yasa Yaya Mai Kano kwaso su.

Ita kuwa Husna da kuka ta rungume Uwar ta kuka Kuma na ciwo biyu ciwon son Alh Aminu da Kuma Rabo su da Yaya Mai Kano yayi Amma Bata sanar da Halima hakan ba sai dai shi Mai kanon ne ya nemi taimakon malamin dake taimakon Halima ya Kuma Soma taimaka Mata da ayoyin Allah Wanda zasu maido ta cikin hankalinta.

Alh Aminu kuwa da ya gama Rudewa ya Rasa abinda zaiyi sai kawai ya nufi gidan Alh Hassan Yayan haj wasila da son ya dawo da ita su hadu su fiddo Indo daga rogo.

Haj Wasila ta dubeshi fuskar ta fall da masifa.

“Ban fa ji abinda kake cewa ba? Anya ma Kaine kuwa ? To in ma Kaine kila dai dimuwa kayi ko ko ka Fara Shan wani Abu Amma Ni yaushe zaka ce Wai na dawo gidan ka alhalin Kai ka fada min baka bukata ta kusa da Kai? To kenan yanzu bukatar ce ta taso shine ka nemeni? To Albarka ban siyar ba don Haka ja jiki Kar ka Kuma zuwa inda nake Kuma Bari na sanar dakai ma don ka hutar da kanka Ni an kusa daura min Aure don Haka ka manta ka taba sanina a Rayuwar ka.

“Da iddar tawa Zakiyi Aure? Ai Ina lissafe da cikar iddar ki don Haka na mayar da Auren mu in Kuma Zakiyi Aure da igiyar Aure nane to sai mu gani har gaban Alkali Zan iya Kai ku ke da shegen da ya Aure ki don Haka zanje Zan Kuma dawo in dauke ki mu tafi sai ki shaidawa Alh Hassan na mayar da Auren mu in ma shine me daure Miki kugu duk zanyi maganin ku wallahi.

Da Haka ya juya ya barta sake da baki don ganin ya gama da ita tunda ya furta ya mayar da ita ta Kuma San ta maidu Amma ta Yaya zata shaidawa yayan ta hakan Wanda ke kullace da zuwan wannan ranar da yake son haife nashi rashin mutuncin?

<< Hawaye 71Hawaye 70 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.