Skip to content
Part 73 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Alhaji Hassan baija ba ya fada wa haj wasila cewa Dole tayi hakuri ta koma don sun Gama Zama Daya ita da Alh Aminu Wanda Amal da muhsin suka gama hadawa Dole kuwa ta dawo tare da Rakiyar haj sa ade matar Alh Hassan

Mai kano kuwa da shaidan ya gama kitsawa makircin daukar fansa Akan Amal tuni ya nemi tazo suje wani wuri Bata kawo komai a Ranta ba ta biyo shi suka fice zuwa wani lodge Wanda ya Kama suka SHIGA inda Amal ta bishi da kallo na neman Karin bayani ya kuwa gimtse fuska Yana kwabe Rigar shi Amal na kawar da fuska zuciyar ta na fada Mata wani Abu Amma ta basar tana shillawa Duniyar tunanin abinda Mai Kano Yake nufi da kawo ta lodge har Yana kwabewa Agaban ta.

Bata Kai karshen tunanin ta ba taji saukar hannun Mai Kano Yana zagaye ta da hannuwan shi ta dago da sauri tana kallon shi shima ita Yake kallo kallo Kuma irin na tsakiyar ido. Suka tsurawa juna ido HAWAYE na keto idon Amal Mai Kano yasaka yatsun hannun shi Yana dauke Mata hawayen ta.

“Alfarmar da nake so kenan gareki Amal nasan kuwa zakayi min ita idan har son da kike min gaskiya ne.

“Kar ka kawo kokonto akan son da nake maka Yaya Mai Kano tunda na baka KYAUTAR ZUCIYA ta ban taba nadamar hakan ba . Kar ka manta Ni din baiwar soyayyar ka ce ba Zan taba juyawa soyayyar ka baya ba Amma Zan Roki kayi min wata Alfarma guda Daya Tak! Shima sai in Ranka ba zai baci ba. Na tabbatar kaima baka taba gwada hakan ga kowa ba kila sai akaina . Wallahi tallahi ban taba gwada Koda Rike hannun wani namiji ba kaima nasan baka taba kebewa da wata mace ba sai Ni Kuma ta iya yuwa mahaifina yaja min hakan to na Roke ka da kayiwa LAHIRA ta gata Kar na zamo daga cikin mazinata kaima Kar ka zamo daga cikin su tunda bamu taba yin hakan ba Amma hakan zata farune idan Ranka ba zai baci ba in Kuma hakan kake so Zan kyautata wa zuciyar da na bawa komai nawa !

Sai ta Soma cire Dan kwalinta tana cire Yan kunnen ta har ta fara fidda Rigar ta yayi saurin Runtse idanun shi Yana Jin wani Abu na zagaye kwanyar shi tare da tunano kalaman Amal wadda ko baya kaunar Allah Dole yayi Mata Adalci musamman akan biyayyar da tayiwa soyayyar shi umarnin shi Anya kuwa idan yayiwa Amal Haka Ubangiji zai kyaleshi ? Ba Amal ce abin daukar fansa ba Uban ta ne Wanda yankan da yayi mishi shine daidai da matakin da ya Soma dauka Amma ko a LAHIRA laifin wani baya shafar wani Kuma yadda Amal ta bashi KYAUTAR ZUCIYAR ta idan kuwa yayi Mata Haka tun a Duniya sai Allah yayi Mata Sakayya tunda ta sanar dashi ko hannunta wani namiji Bai taba Rikewa ba Alh Aminu shine abin daukar fansa Akan shi ba Ahalin shi irin Amal me bada kyautar da Bata karbewa ba.

Bai Kai karshen tunanin shi ba yaji Amal ajikin shi inda yaji wani feeling Mai Kama da Jan wutar lantarki abinda yaso tafiya da nutsuwar shi ga mamakin shi sai yaga kwalla na bin fuskar Amal. Da sauri ya Kori shaidan makiyin Al ummar ANNABI Adama A S ya jawo katon blanket ya Rufe Amal Yana zare jikin shi daga nata Yana ambaton sunan Ubangiji da jero istigifari ya Kuma dafe kanshi HAWAYE na bin idanun shi.

Amal ya sake ji ajikin shi tana fadin, “Kayo hakuri idan magana ce ta Bata maka Rai Ni din baiwar soyayyar ka ce na yarda na Amince in har hakan zai faranta Ranka Kar ka damu da kukana nasan Ubangiji zai yafe Mana.

Shima cikin hawayen ya Riko kafadunta suna kallon fuskokin juna

“Amal ban taba Jin kin burgeni a Rayuwa ta ba irin yau yau din ma yanzu. Na karbi soyayyar ki Zan Mata mazauni na musamman a Rayuwa ta don kin nuna min kece irin macen da ya Dace ta zamo Uwar yarana me karbar umarnina ko Bata so ba me son abinda nake so me afuwa a kullum me Kuma fahimta a komai. Amma ki sani duk da karbar soyayyar ki da nayi ba zai hana na dauki fansa Akan mahaifin ki ba soyayyar ki daban wurin da na aje mahaifin ki daban Babu ma Ruwan ki da duk wata harkalla da Zaki ji ko gani kinajina?

Ta gyada kanta wasu hawayen farin ciki na sake tsinkewa a fuskar ta ya Soma dauke Mata su da yatsun hannun shi

Da Haka suka baro lodge din Kuma Wai sai ya SHIGA kunyar hada idanu da ita itama Haka NE don tanajin ba KYAUTAR ZUCIYA kawai tayi mishi ba har da KYAUTAR KANTA tayiwa Mai Kano saboda kauna.

Bai San ya kamu da soyayyar Amal ba sai da ya kwanta yayi ta mafarkin suna ta tsinkar furen soyayya shi da ita.

Da ya farka ma tsarin halittar ta yayi ta mishi gizo har Yana tsaya mishi Arai inda ya Gane so na kaunar kasancewa tare yakewa Amal yayin da ita Kuma Salma tausayin ta Yake Amma Kuma duka Yana son su. Irin kulawar da Amal ke bawa Halima yasa ta tako wani matsayi a wurin Halimar dama ko can tana sonta Kuma abinda Uwar ta da Uban ta sukayi Mata Bai sa ta kalli Amal din da laifin iyayen ta ba don Haka Halima tace da anyi Mata Rukiyya a gobe jibi zasu koma katsina.

Husna dake zaune tana kallon su tana Jin zuciyar ta kamar ba Tata ba sai ta dauko Alkur ani tana karatu kafin ta dauko Ruwan Rubutu ta Sha har taji nutsuwar ta ta Soma dawowa inda Kuma Amal ta ambato sunan Yaya muhsin sai Husna taji wani Abu me kama da Wanda ta manta har taci gaba da nanata sunan Yaya Muhsin

Shi kuwa Yaya muhsin da ya mayar da hankali Akan cas din Alh Bello sai ya nemi ganawa da Alh Bellon har ya nemi address din Alh Aminu Wanda Alh Bellon ya sanar dashi gidan shi na sardauna Estate inda yace to ya Bari zuwa Monday za a Rubuta sammaci a aika mishi in yaso Ranar da Alkali zai zauna Shari ar sai su hallara tare.

Ranar Monday kuwa Alh Bello ya biya kudin yankar sammaci aka aikawa Alh Aminu da takardar sammaci inda kuma ta riskeshi cikin tarin fargaba da Rudani domin kuwa lauje ne ya kirashi a waya Yake sanar dashi duk abinda ya faru dashi shi ya siya tunda har yau wa adin Zubaina ya cika Bai aikata ba don Haka karma yace yasan shi kowa tashi ta fisshe shi don yasan shima ba fita zaiyi ba Bala’i ne dai ya riga da ya jawo musu.

Ya mike da wayar a kunnen shi bakin shi na rawa ya kasa cewa da Laujen komai saboda tsabar rudewa ya fito Yana Shirin ficewa zuwa gidan lauje sai yayi karo da sakon sammaci ya karba inda Dan Aiken ke sanar dashi Ranar laraba Sha biyar ga watan alkalin ke son ganin shi sai ya Kuma SHIGA wani Rudanin na ubanwa Kuma ne ya kaishi gaban Alkali? Tunowa da muhsin dake matsayin lauya yasa yaga Bari kawai ya kirashi ya wakilta shi akan shine tsayawa akan Shari ar Amma Kiran Duniya muhsin din yaki dauka.

<< Hawaye 70Hawaye 74 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.