Skip to content
Part 74 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Safina da ta mayar da kanta wata kayan arha ga tsofaffin Samarin ta tamkar ba Aure NE akanta ba . Tunda ta kasa samun muhsin ta ke bin tsofaffin Samarin ta ana sheke Aya suna Bata kudi kuma ta dawo gida da sunan matar Aure.

Babu Wanda yasan hakan kasancewar kowa Yana abinda ya ke gaban shi shiyasa babu Wanda ya kula da halin da take ciki Sai fa yau din da Ubangiji yayi nufin tona asirin ta da Aikin ta inda ya kawo muhsin Wanda ya kama su ita da saurayin nata a turmi da tabarya a halin da suke ciki

Duk da ba wani so yakewa Safina ba sai da yaji wani Abu me kama da kishi don Haka da sauri ya fito ba tare da sun ganshi ba ya dafe Kai Yana mamakin wannan Al’amari

Ya kwashi takardun da suka kawo shi ya fice ya bar gidan. Fitowar shi tayi daidai da dawowar Alh Aminu Wanda ya tsayar dashi Yana bashi takardar sammacin Yana fada mishi shi ba zai samu damar zuwa ba.

Ya warware takardar yana dubawa gaban shi na harbawa baya ko shakka Daddyn nashi ne Alh Bello ke tuhuma ko Kara.

“Daddy kasan wannan mutumin ne dama?

“Ban San ko waye ba nasan dai ba zai Rasa masu Jin haushi na ba makiya kenan to in sunyi hakuri ma Ni ba siyasa Zan fito ba bare ayi tunanin Bata min suna don Haka wannan Ranar taka ce ka nuna min banyi wahalar banza ba Akan kudin da na kashe har ka tako wannan matsayin.

“Daddy fada min gaskiya kasan wannan Alh Bellon? Nine lauyan da ya dauka na Kuma yi mishi alkawarin tsaya mishi har sai an tabbatar mishi da hakkin shi nayi mamaki da yace fyade akayiwa Yar shi Kuma Kaine kayi ada ba Zan yarda zakayi hakan ba Daddy Amma a yanzu zuciya ta ta kasa Zama wuri Daya saboda abinda kayi min Akan Husna Daddy Al halin kasan nine mijinta Daddy Amma ka Raba Ni da ita.

Sai kuka ya kwace mishi ya kasa ci gaba da magana har sai da yayi kukan shi ya share hawaye kafin ya dubi uban.

“Daddy Ni yanzu bani da abinyi Akan hakan kaje kotun Ranar da Alkali ya nemi ganin ka shine mafita kawai idan Kuma kasan kayi laifin da mutumin can ke karar ka ka sauwakewa Shari a ka amsa ba tare da Anja zance ba Ni Kuma Zan tsayawa Alh Bello don ganin an bawa me hakki hakkin shi kaima sai ka nemi lauyan da zai Kare ka.

Wasu mahaukatan maruka ya ji saukar su a kumatun shi.

“Ashe har zaka iya kallon tsabar idona ka fada min Haka muhsin? Kana nufin Ni da Kai zamu tsaya a gaban kotun kana tutsiye Ni? Ashe Kai ba me Rufa min Asiri bane idan kaga ana kokarin tona min?

“Ba Zan Rufa Asiri Akan cuta ko karya ba Daddy. Gaskiya kawai zakayi na Rufa Asirin ka Daddy ba cuta ba idan har ya zamo da gaske kayi abinda mutumin can ke karar ka to Ni Babu abinda Zan iya don ban SHIGA Aikin Nan don abani kudi na danne hakki ba na SHIGA ne don na taimake Wanda ake dannewa hakki. Don Haka daddy kayi hakuri Babu abinda Zan iya akai. Da akwai Alfarma a Duniya da baka Hana Ni abinda Raina da zuciya ta ke muradi ba . Da akwai Alfarma a Duniya Nima da na nema maka ita ko ba kaina ba shima sai in akwai gaskiya a ciki.

Ya Mike ya fice ya bar Alh Aminu sake da Baki Yana bin shi da kallo inda ya Gane kishin abinda yayi mishi yasa ba zai waiga Kan Sha anin shi ba inda Kuma yaji ya Soma nadamar abinda ya aikata Akan yarinya Safiyya wadda abun ya Soma dawo mishi tamkar yanzu ne Yake faruwa.

Ya daga kanshi sama Yana kallon katafaren gidan nashi Wanda babu abinda ya Rasa sai kwanciyar hankali saboda Yana son shahara da tarin dukiya yau gashi ciki Anna kalubale ya zagaye shi ta ko ina kalubale da gara ace bashi da ko sisi indai Yana zaune lafiya. Amma yau gashi ga dukiya sai dai babu kwanciyar hankali babu lafiya babu Kuma ibada wadda lauje da Zubaina suka dakatar dashi

Yana zaune abin Duniya ya hade mishi Safina ta fito ita da saurayin nata bayan angama sheke Aya sukayi kicibus da Alh Aminu ya dubesu inda firgicin ganin su Bai boyu ba ga Alh Aminu Amma da Yake Yan Duniya ne sai Safina tace kanin mahaifin tane yazo dubata.

Wayar shi tayi Kara ya daukota da sauri Yana duba Kiran lauje Wanda Yake sanar dashi ya dawo don dazu da yaje Bai iske shi ba Wai wani uban gidan shi ne ya dauke shi yayo mishi aiki don Haka yace ya dawo

Da sauri ya nufi gidan Laujen Yana neman Karin bayani.

“Yau fa kwana biyar Kenan Zubaina Bata amsa Kiran da nake Mata ba Aminu Kuma duk cikin fushin ka ki cika musu alkawari ne har gashi wani Abu na neman aukuwa.

“Wani Abu name Kuma? Ya tari Lauje hankali a tashe.

“Waccan yarinyar Husna zata dawo ga Muhsin Kuma wancan yaron Mai Kano zai Auri yarka Amal Wanda ko baka da laifi wurin Zubaina haduwar wadan Nan ma auratan kadai ya Isa yasa kuyi hannun Riga da Zubaina da Kuma shahara har da tarin dukiyar ka don babu Hadi ai Kuma sun sanar da Kai hakan?

“Ba zaiyuwu ba lauje in na Rasa lafiya ta na hakura to ba Zan Rasa dukiya ta da shahara ta na hakura ba yanzu Kira min Zubaina Zan iya Bata jinin muhsin da Amal gara ace na sadaukar dasu Akan na rasa wadan Nan abubuwa biyun wallahi Zan iya Bata su har Uwar su ma in tana bukata.

“To da dai kayi Mana gata Kam don bana Zubaina abin nata babu mutunci wulakancin nata me kalar Ruwan Hoda ne. Lauje ya fada Yana rura garwashi sai kuwa ga Zubaina ta bayyana Amma fa a fusace take har tana fadin.

“Kufa Daina kirana in ba wani Bala in kuke Shirin jawo min ba.

“Me ya farune gimbiyar dodon kod’i? Lauje ya tambaye ta ta Kuma amsa a fusace.

“Me ye ma Bai faru ba?

“Ni da mijina da iyalaina mune a jikin Halima Kuma yanzu ana Mata magani Wanda har ya sa nayi Asarar wasu daga cikin iyalaina Wanda aka kashe har lahira Kuma sauran sun can suna jinya Kuma gobe suke cewa zasuyi Mata karatun Alkur ani Wanda in har na sake Rasa wani daga cikin iyalaina to Nima Zan Rama ne kawai tunda an maida mu bayi sai dai mu biya bukata mu ba a iya biya Mana tamu bukatar yanzu Haka Ni da mijina ne kadai ajikin Halima muma ba lafiya garemu ba idan har akayi Mana karatun Alkur ani muma kashe mu zasuyi don Haka indai hakan suke nufi to Dole zamu baro jikin Halima mu dawo Kan wancan mutumin marar alkawari don Haka Kar asake kirana ! Ta fada da karfi ta Kuma fice abinta Dole suka bi tagar da ta fice da kallo suna

“Yanzu lauje meye abin yi?

“Wane abinyi kake magana Kuma? Bakaji abinda tace ba?

Lauje ya fada a fusace don shima Yana ganin Rasa Zubaina shine mutuwar shi. Suka zubawa juna ido cikin Rashin makama kowa najin haushin kowa don Yana ganin shi yayi wasa da damar su Dole ya taso ya taho cikin mutuwar jiki da jiran ta inda sakamakon zai sauko.

Safina kuwa da ciwo yayowa sallama zazzabi da hararwa har ta kaita ga kwanciya a gadon Asibiti Dole Anty maimuna ta je don ance Dole sai Dole sai Kuma ta iske Wai ciki ne ke wahalar da Safinar abinda ya Bata haushi kenan har ta Kira haj wasila tana masifa Wai an bar Safina kwance a gadon Asibiti babu zuwa babu aike. Sai ta SHIGA zubar da Ruwan tijara tamkar tana jira ko dayake har jiran ma tanayi inda Kuma haj wasila tace ta nemi Muhsin taji abinda ya Hana shi zuwa ba ita ba . Safina dake kwance tana micincina idanu tana jin abinda Uwar ta ke yi tayi shiru tana hango yadda zasu Kare tsakanin muhsin dai da Anty maimuna dake neman layin nashi cikin masifa da son ta yage musu Rigar mutunci shi da uwar shi haj wasila. Cikin sa a kuwa ta sameshi har ya daga Yana gaisheta.

<< Hawaye 73Hawaye 75 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.