Fitar haj wasila Babu jimawa muhsin ya shigo Wanda ya Soma jiyo sautin muryar mahaifin shi Yana kakari da kwarara ihu.
Da sauri ya haura sama inda Yake jiyo muryar Daddyn Kuma ga mamakin shi Bai ji motsin kowa ba a gidan babu Amal babu Mami.
Ya shiga dakin inda ya samu Alh Aminu cikin wata muguwar Kama don gaba Daya halittar jikin shi ta juye ta jirkice yayin da fuskar shi tayi Baki harshen shi ya zazzago idon shi Kuma Yana fitar da jini.
"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un din da Yake fada Yana maimaitawa itace tasa. . .