Skip to content
Part 78 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Gidan su Halima muhsin da Amal suka fara sauka don Dole ta can ne zasu fara don Alh Dan iron ya hada su da me maganin ba don Haka ba da muhsin Bai sauka a inda Husna tayi mazauni don in ya ganta Yana Jin tamkar ya Amaye zuciyar shi Amma Dole yabi Amal wadda Kai tsaye nan ta sani.

Halima ta gansu da Alh Aminu Wanda kamanin shi sun jirkice ga wani irin Baki da yayi tamkar an Rina shi yayin da jini ke fita Baki da hanci . Ta kadu matuka Gaya Amma tuno Abinda ya faru a baya yasa taji kamar Bai da kaico Amma zuciyar musulunci da Kuma mutuncin Ya’yan shi yasa ta nema mishi sauki a wurin Ubangiji kowa yayi nagari akan shi yake gani.

Husna ta shigo tayi Arba da Amal da Yaya muhsin ga Kuma daddy a wani yanayi da yayi masifar Bata tsoro. Tayiwa muhsin kallo Daya ta dauke kanta tana magana kasa kasa Wanda sai me kyakkyawan ji ne zai iya Jin abinda ta fada shi ma ya bita da wani kallo na kasan ido ya Riko hannun Amal suka wuce daki tana tambayar ta me ya samu Daddyn ne taga ya koma haka? Amal da ke dafe da kanta HAWAYE na Zuba ta Soma sanar da Husna Abinda Daddy ya shuka a Rayuwar shi na kauce hanya da tsafe tsafen Wanda yake Kan girbar abinda ya shuka a take Husna ta fahimci makasudin hakan duka dai don a tsira da abin Duniya Wanda bashi da tabbas din samuwa duk da bata so yiwa Alh Aminu ADDU A ba Dole ta tuna mutuncin Amal da musulunci don muhsin ma Bata jero shi a Wanda zata yiwa Kara ba musamman idan ta tuna keta Haddin da Daddyn yayiwa Uwar ta.

Dole me imani zaijj wani Abu a zuciyar shi idan yayi Arba da Alh Aminu a cikin Halin da yake kallo Daya zaka fahimce abin na shedanun aljanu ne Dole Halima ta Kira me gidan ta ya iso ta sanar dashi komai shima ya Kira shehun malamin ya karaso ya Soma duba Alh Aminu ya Fara da ayoyin Al kur Ani Mai girma da wankan zam zam da ganyen magarya sai dai me? Maimakon sauki sai lamari ya Kara Rikicewa Amma duk da Haka malam Bai fasa da bashi magani da Ruwan Rubutu ba.

Jin abin na gaske ne yasa zubaina yin magana tun kafin ayi mishi rukiyya inda Malam ya Gane komeye ya samu Halima wannan mutumin ne Kuma aljanar da tayi wa Halima mugun Aiki itace tayi kaikayi koma Kan mashekiya ga Wanda ya yi turen. Don haka sai ya bude alkur Ani Yana me yin karatu kafin zubaina ta Soma kuka tana Rokon ya Daina Amma Bai Daina ba sai da ya dire inda ta cika dakin da kakari tana fadin ya kone ta yace In ma Bata fita akan shi ba haka yake nufi tunda tayi alkawari ta karya ba ita bace yayiwa gargadi akan ta kyale musulmi ba ta Daina cutar su? Tace ai wannan shine ya cuce ta ya kone Mata miji ya Kuma kone Mata Ya’ya shine Kuma yasa ta tayi mishi Aiki ya samu duk wata shahara Amma ita baya cika Mata nata muradun . Malamin ya tambaye ta wane irin muradu kike so ya cika Miki? Ai kuwa ta Soma Rattaba mishi abubuwan da take saka Alh Aminu irin su soke sallolin farilla kamar asubahi da juma a da la asar da isha I da Kuma fyade wa kananun Yara.

Muhsin da Amal kuka suke kamar zasu Amaye zuciyar su Jin abinda uban nasu ya bar musu a matsayin bakin gado. Malam ya yiwa zubaina kashedin ta fita daga kanshi tunda itace babbar shaidaniyar da ta batar dashi ta Hana shi manyan ibadoji tace ai ya fita shaidancin tunda ita Bata Kira shi ba shi Kuma Kiran ta yake tana bashi abinda zai Kara mishi shahara Kuma Wallahi ba zata fita a kanshi ba sai ta kone shi kamar yadda ta kone ubangidan ta lauje shima sai tayi mishi haka kafin ta juyo ga duk wani Ahali nashi sai ta shiga Rayuwar shi ta kassara su kamar yadda ya kassara Mata ZURIA da miji Kai ko sanin shi kayi sai na watsa ka . Malam yace to ba zakiji Rarrashi ba kenan? Tace Eh ai kuwa ya Soma karatu tun batayi magana ba har ta Soma kuka tana kururuwa har ta Soma fadin Wallahi zan fita don ALLAH ka kyale ni Amma Malam Bai kyale ta ba sai da yaji muryar ta ta Soma yin kasa kasa kafin hayaki ya Soma fita ta bakin Alh Aminu Wanda suffar shi ta Soma komawa yadda yake Alamar zubaina ta bar shi sai dai jinin da yake fita Baki da hanci ya sake ballewa.

Malam ya dubi Alhaji Dan Iro ya Kuma dubi Mai Kano da muhsin Yana fadin sai dai ayi hakuri Amma zuciya tayi Aikin ta Banda Allah ya kiyaye hakan to kamar yadda aljanar Nan ta fada zatayi ta bibiyar ZURIA ta wannan bawan Allah Amma yanzu alhamdulillah tunda ta kone Allah ya kawo karshen ta Allah ya tsare Mana imanin mu inda Malam ya Dora da nasiha ga me Kano da muhsin akan duk yadda Duniya tayi Dadi tana da karshe duk dadin Haram kuwa abarta ayi hakuri da Halal duk kankantar ta inda a karshe yace a Kai Alh Aminu Asibiti Allah ya bashi lafiya.

Alhaji Dan iro ya sallami malam da kudi me yawa ya tafi aka dauki Alh Aminu zuwa Asibiti muhsin shi ke wurin shi inda ya farko cikin wani irin Hali duk da ya dawo hankalin shi Amma Yana Jin kwanyar shi tamkar ana hura mishi wuta a ciki.

Amal da Husna suke kaiwa Yaya muhsin abinci a Asibiti inda a Rana ta uku da kaishi Asibitin ya bude Baki ya Riko hannun muhsin Yana fadin Ina Amal take muhsin? Yace tana gida a Kira maka ita ne? Yace Kira min ita har da mahaifiyar ku don Allah ka Tara min su har da Ahalin mu Azu don Allah ka Kira min su

Ai kuwa muhsin ya Tara dukkan Ahalin guda biyu hatta haj wasila dake katsina sai da muhsin ya Kira ta dab da magaruba kowa ya iso dakin Asibiti inda ciwon Alh Aminu ya yi tsanani. Amma Cikin ikon Allah ya ce muhsin ya tada shi zaune ya tada shi ya Soma duban Halima Yana fadin Halima ban San Abinda zan ce Miki ba Amma don girman Ubangiji kiyi min gafara kece na cuta fiye da zato ke da Ahalin ki Duniya ta Rude ni har nayi Abinda nayi don Allah ke da mu Azu da Ahalin ku ku yafe min a yau nayi nadamar kasancewa a wannan turba da na tafi na barwa ZURIA ta bakin tarihi ko yanzu na bar musu abin kunya Amma don Allah don ANNABI nasan ku duka nayi muku laifi ku yafe Ni ku kuma tayani Rokon ALLAH ya yafe min wasila dake da muhsin da Amal me Kano Kai da Husna don girman Allah ku yafe min kafin na fuskanci Ubangiji da tarin laifin da nayi mishi.

Kuka ya kaure a dakin Asibitin Halima tace ta yafe Mai Kano ma yace ya yafe su duka suka ce sun yafe yayin da hajiya wasila take Rungume dashi akace tsakanin miji da Mata sai ALLAH Alh Aminu daban yake a zuciyar ta sai yau da ta ganshi a gargarar mutuwa taji tana son abinta kuka take tana fadin ta yafe Allah ya bashi lafiya sai dai Ina bakin Alkalamin ya bushe domin kuwa zubaina ta bar mishi abinda ba zai barshi ya Rayu cikin lafiya ba don kamar yadda ta fada duk wani Wanda ya shafi Ahalin shi da ta Rayu da ba zata taba barin su zaman lafiya ba da taga malamin ya kone ta sai tayi mishi ajiya a cikin kanshi Wanda Ubangiji ya kaddara yazo daidai da karar kwana a wannan Rana ta juma a Ubangiji yayiwa Alh Aminu cikawa ya mutu Yana me tuba a wurin Ubangiji inda dakin ya sake daukar sabon kuka Amma ya za ayi da hukuncin Allah? Kowa jiran tashi yake sai dai fatan Ubangiji ya Dora mu akan turbar gaskiya don haka aka dauki gawar zuwa katsina akayi mishi sutura Zuwa gidan mu na gaskiya.

Su Mubarak da zaidu ma sun iso akayi zaman dasu Husna da Amal me Kano da muhsin har aka share makoki aka watse aka bar Ahalin da Yaya za ayi? Amal da muhsin suka sama wa kansu mafita bakin su yazo Daya akan dukiyar da mahaifin su ya bar musu gado akan su Gina massalatai da gidajen marayu su duka suka Aminta da haka Haj wasila Bata sa musu Baki ba don tana ganin hakan da sukayi sunyi daidai Kuma Uban su zai samu sauki akan abinda ya shuka idan ya samu hakan da Ya’yan sukayi Arziki na ALLAH ne.

Halima da tazo wa Haj wasila gaisuwa kunya ta hana ta duban idon ta Suma Nan Haj Wasila ta nemi gafarar Halima akan abinda tayi Mata yau gashi Wanda ya hada ya Raba suka yafi juna Halima ta ajewa hajiya Sha Tara ta Arziki tana ta saka Mata Albarka tana cewa Alh Aminu gara da ALLAH ya kama shi ai Allah yayi mishi me sauki tunda ya kashe shi.

Sai dai me? Mai Kano ya kasa zaman lafiya Amal ta yi mishi tsaye a Rai Dole ya neme ta ya na tambayar ya fa shirya wani farin ciki ya mamaye zuciyar ta tace zata sanar da Haj wasila kome kenan zata fada mishi ai kuwa tuni magana ta tashi Kan kace me sai ga Amal a gidan me Kano a matsayin Amarya inda gidan kowa daban ita da Salma abinda ya tadowa masoyan biyu Miki wato muhsin da Husna wadda ta kure daki tana kuka muhsin kuwa bacci ya Soma gafarar shi Babu abinda yake dawainiya dashi sai kishin mahaifin shi Wanda yake ganin Husna ce ta cuce shi da ta yarda har daddy ya sameta.

Kowane cike yake da tarin damuwa inda a wannan halin ne muhsin ya nemi Alh Bello mahaifin safiyya ya Kuma fada mishi komai akan Daddyn nashi ya bukaci da ya fada mishi abinda yake so zaiyi mishi in ma shi yake son ya karbi hukuncin mahaifin shi duk zai karba.

Alh Bello yayi shiru don Jin mutuwar Alh Aminu Kuma Wai shine Uban lauyan da yake son ya tsaya wa marigayiyar yarsa safiyya don haka yace ya yafe tunda har Rai yayi halin sa inda muhsin ya so biyan shi diyya Amma yace ba zai karba ba muhsin yayi mishi Godiya suke zumunci duk da Yana matukar Jin kunyar Alh Bello Wanda uban shi yayiwa Yar sa fyade har ta Rasa Ranta duk cikin Rudin Duniya.

Amal ta Kira wayar Husna tana tambayar ta Wai sis ni fa banji bayanin komai akan ki da Yaya Mai Kano ba me kuke jira ne? Husna tace Anty Amal ai munyi hannun Riga da yayan ki Baki kula ba ne halan? Kai haba dai wasa kike Husna tace Wallahi kuwa Anty Amal ai ni har hakura ma wani kawai zan tsayar.

Ban yarda ba Husna ALLAH wasa kuke indai fada kukayi bari yanzu na kirashi na sasan ta ku.

Ta katse wayar tana neman layin Yaya muhsin ya dauka suka gaisa tana tambayar shi Haj wasila yace tana lafiya. Tace Wai Yaya fada kukayi ne da Husna har yanzu banji komai ba? Wani Abu ya tsaya mishi a zuciya yace to Amal me zakiji bayan Wanda kikaji? Ai Husna ta cuceni Amal duk fa kaunar Nan da nake mata sai da ta yaudare ni Baki San har da ita daddy ya nema ba ? Lokacin da ake ta cigiyar Nan fa suna tare kuma ni da idona Naga Yana Rungume ta to ta Ina kuwa zakiji wani Abu? Amal tayi maza tace Kai Anya kuwa Yaya muhsin bana tunanin wani Abu a tsakanin su yace koma dai meye Amal ni fa na hakura da Husna zan koma wurin Safina.

A’a Yaya kar kuyi haka yanzu Nan mukayi waya da Husna take fada min wai ta tsayar da wani ne.

Ya yi hanzarin tarbar ta waye Husna ta tsayar? Tace Nima ban sani ba Amma kuwa idan kukayi haka da kungana bada masoya Wallahi ba ta tsaya jiran me zaice ba ta kashe wayar don ta lura ta kunno shi ai kuwa a Ranar ya yi shiri ya nufi Legos.

Husna dake kuka tana sharbe HAWAYE har Halima ta shigo dakin ta tsaya akanta Bata sani ba sai da ta dafats kafin ta dago suna kallon juna Halima tace fada min Abinda ke damun ki na kula kwana Nan kina cikin damuwa Amma Baki fada min ba wani Abu ne?

Bata boyewa mahaifiyar ta komai ba akan su da muhsin Wanda ita Bata San Abinda tayi mishi ba.

Halima tayi murmushi tana cewa bari mai Kano yazo sai asan yadda za ayi ai da Baki boye min ba da tuni nasan abinyi.

A gidan Mai Kano muhsin ya sauka inda suka hadu har da me Kano ana tauna maganar wadda suka taho Gaba Daya wurin Halima inda aka Gane muhsin kishi ne ya Hana shi neman Husna itama Bata boye Rayuwar da sukayi da Alh Aminu ba wadda ya so cimma mugun burin shi akan ta ta hanyar shafa kwallin sihiri har ta kamu da kaunar shi sai dai ana dab da cimma buri me Kano ya yi mishi yankan da ya kassara wancan buri don haka Babu komai tsakanin ta da Alh Aminu inda su duka kunya ta kama su Halima Kuma tana musu Dariya Amal Kuma na fadin da an bada masoya.

A take aka saka Ranar tariyar Husna wadda aka Mika garin katsina inda zuciyar muhsin ke cike da kokonto Amma a Daren ya tabbatar da abinda yake zargi Bai faru ba sai tattali da riritawa.

Yayin da safina ta haife cikin ta Wanda ya Raba gardamar waye uban shi wato murtala sai dai duk yadda suka so Mika mishi yaron yace Bai San zancen ba inda suka dire har gaban alkali Wanda ya barwa safina yaro yace danta ne Dole kuwa suka Rungume kaddara Anty maimuna taji kamar ta Kori safina da danta Amma ya ta iya.

Ita kuwa Adama abin nata sai ya zama hauka kullum cikin dure duren Ashar take ita kadai ma bare taji motsin mutum hauka tuburan inda Salma ke kawo Mata agaji har dai daga karshe Adama ta tuke a gidan masu tabin hankali.

Shekara guda da Auren Amal da me Kano ta haifo katon danta me kama da mu Azu uban Mai Kano Wanda Halima tace suyi Mata Alfarmar sakawa yaron sunan mu Azu haka kuwa akayi suna Kiran shi da Halifa.

Husna kuwa sai da tayi shekara biyu kafin ta haifo yarta me kama da muhsin Wanda aka sakawa suna wasila suna Kiran ta walida yayin da Salma ce dai shiru bats samu nata Rabon ba inda Mai Kano ya dauki halifa ya bata kyauta Amal kuwa ko ta Daga Kai ta duba don ita kanta tasan Salma ba kishiya bace yar Uwa ce.

Ta ko Ina dai Zaman lafiya da kauna da soyayya ya wanzu yayin da Mubarak da zaidu suka gama karatu suka samu aiki kowa Yana kokarin farantawa Halima Rai sulaiman ne dai Bai Kare karatun ba sai da ya dawo ya samu labarin Rasuwar Alh Aminu yayi jimami ba kadan ba don Bai manta soyayyar da ya nuna musu ba dama haka abin yake Babu abinda Daya da ke zama a Duniya komai yayi farko to zaiyi karshe kamar yadda labarin HAWAYE ya zo karshe a yau Allah Ubangiji ya amfanar damu alherin rubutun kuskuren ciki Kuma Ubangiji ya yafe har kullum makasudin Rubutun ba Wai a karanta ayi Raha ko nishadi ba A a darasin ciki shine abin duba Allah ya yafe Mana kuskure ladar Kuma ya amfanar damu Godiya ga Dubun dubatar masoyan rubutun gidan Allah ya kara kauna da soyayya da haka nake cewa mu sake haduwa a cikin wanta sabuwar firar me taken FARIN CIKI wanda nake fatan tabbatuwar FARIN CIKI a gare mu duniya da lahira.

<< Hawaye 77

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.