Halima ta raka Alhaji Aminu da idanu lokacin da yake ficewa daga gidan bayan ya gama fada mata zai saki Auren HajWasila akan ya aure ta.
Sai taji ta soma nadamar sanin shi a rayuwar ta. Me yake zato ? Akanta zai saki matar shi? Ai ko babu kome a tsakiya bata jin zata aure shi. Don har ga Allah bata taba son wani mutum a rayuwar ta kamar yadda taso Mu'azu ba. Shi yasa ma take Jin ta rufe kofar Aure a Duniya. Asalima Alhaji Aminu bai yi mata ba don ta san kadan daga halayen shi wurin matar. . .