Skip to content
Part 9 of 32 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Halima ta raka Alhaji Aminu da idanu lokacin da yake ficewa daga gidan bayan ya gama fada mata zai saki Auren HajWasila akan ya aure ta.

Sai taji ta soma nadamar sanin shi a rayuwar ta. Me yake zato ? Akanta zai saki matar shi? Ai ko babu kome a tsakiya bata jin zata aure shi. Don har ga Allah bata taba son wani mutum a rayuwar ta kamar yadda taso Mu’azu ba. Shi yasa ma take Jin ta rufe kofar Aure a Duniya. Asalima Alhaji Aminu bai yi mata ba don ta san kadan daga halayen shi wurin matar shi Wasila musamman yadda yake bawa dukiya muhimmanci da kuma rashin maida kai ga bautar Ubangiji. Kuma ko ba wannan ba ita dai Mu’azu kawai ta taba so a duniya kuma a yanzu ma ba za ta yi mishi kishiya ba. Aure kuma ba zata yi ba.

Ta mike tana hararen kayan da ya kawo mata inda taji tsanar kayan har ma ta yanke shawarar daina karbar komai daga gareshi tunda Ubangiji ya rufa mata asiri a cikin sanaar ta guda biyu makarde da kuma zobo da kunun Aya har da ruwan leda dasu ne take hidimar karatun su Mubarak da su Husna.

Ranar asabar da sassafe tana kicin tana hada abin karin kummalo Alala ce da kunun tsamiya yayin da Husna da Sulaiman ke tsakar gida sai jiyo sallama tayi inda taji yaran sun kaure da hargowa ta fito sai kawai tayi karo da Mai Kano cikin shiga ta burgewa sai kamshi yake yi.

Murmushi tayi tana kallon shi cikin mamaki don wata uku kadai amma sai taga har girma ya kara girman da ya zarce shekarun shi.

Ya aje jakar shi yana rungume da Husna da Sulaiman, Halima kuma tana murmushi.

“Ikon Allah Mai Kano yanzu kake tafe? “Wallahi kuwa Mama na matsune nazo na ganki. Husna ta kawo mishi kujera Sulaiman na taba agogon shi. Yana fadin yana son irinta. Halima ta koma kicin ta sauko abin karin tana fadin. Kamar na san kana hanya yau nayi mutuniyar ka Alala….

“Ai kuwa Mama nayi rashin traditional cooking din ki . Ta zuba mishi Yana ci kannen shi nata jeho mishi tambayoyi.

“Yaya Mai Kano rannan Mama tayi ta kuka tana fadin bata san halin da kake ciki ba. Cewar Sulaiman.

Ya dubi Halima wadda ita bata san ma Sulaiman din yaji abinda take fada ba.

“Kiyi min afuwa ayyuka na samu suka sha kaina. Wallahi dake nake kwana na tashi jiya dai nace yau sai nazo na ganki yanzu Haka ma sai da nayi da gaske kafin na samu na taho. Mutumin da nabi dan nan garin Katsina ne shine ya daukeni yaron shi tun ina nan yake bamu kudi mu samo mishi kayan karafa, yanzu haka ma a karkashinsa nake. Kuma yana biyana hakki na yanzu ma ya biyani dukkan hakki na kingan su dubu dari biyu da hamsin a ciki ne nayi muku wannan siyayyar. Ya jawo jakar ya bude Yana fito da kayan kaf dangin shi babu wanda bai siyowa kayan salla ba kasancewar yau ne duban farko na watan Ramadan.

Halima tayi godiya ta kuma yi mishi fatan alheri a rayuwa tare da kamanta gaskiya a cikin harkokin shi. Ya amsa da in Allah ya yarda zai kamanta. Kwanan shi biyu ya juya ya koma Legos inda ya bawa Halima nomber wayar shi don yayi waya. Don Haka kullum zai Kira ta ya gaishe ta ya Kuma tambayi lafiyar su ya kuma Roki ta saka shi ADDU A Akan duk abinda ya saka gaba. Ita kuma tayi mishi Adduar dacewa da duk abinda Yake so Yake nema. Tsayin lokaci bata kuma sake ji daga Alhaji Aminu ba har tayi fatan yayi zuciya ya rabu da ita.

Saura sati guda salla Amal take fadawa Alhaji Aminu sarkar gold din da yace zai siya Mata Bai siyo Mata ba.

“Anyi haka Amal shiryo muje ki zabi wadda kike so ki kuma fadawa uwarki itama tazo muje ta zabo kayan sallar ta.

Haj Wasila dake zauna tana jin su tamkar dai ta maida bakar maganar ba ta bukata sai kuma ta tuna salla ke tafe don haka ta hadiye tsegumin ta tayi shiri suka fice inda Amal ke cewa Daddy Yaya Muhsin fa banda shi zamu je? “Ai shi na sallame shi Amal tare aka yi mana dinkuna . Don Haka suka fice Kalamu Waheed shopping Mall suka yi ta jidan kaya tamkar ba kudi ake sawa a siya ba. An kuma siyawa Amal sarka ya gold irin ta garari inda Kuma Alhaji Aminu ya ce duk abinda Wasila ke so ta dauki bibyu komai kala biyu. A zaton ta gata yayi mata don haka komai ta dauko biyu aka yi lissafi ya tura kudin ta account suka taho bayan ya siyi wasu kayan daban.

Sai da suka Zo gida yace ta Raba kayan biyu ta dauki ta bashi dayan. Ta dube shi a mamakance.

“Ban Gane in Raba biyu ba?

“Eh ki ba ni sauran akaiwa iyalan Mu’azu, ba ki san suna da hakki a kaina ba ko don Amincin dake tsakani na dashi ba?

Ta dafe kugu tana kankance idanu…

“Fito min a mutum sak Aminu ba sai ka fake da Aminci ba. Idan ma hakkin ne kamar yadda ka ce ni zaka hada kafada da ta Halima akan komai namu ya zamo iri daya? Na fa gama gano inda ka sa gaba kyale ka kawai nayi. To Kar ka kure hakuri na ka bar Halima a matsayin da take dashi na matar mamacin abokin ka idan kuwa ka shirya saka kudin ka ka siya Mata tashin hankali to Bismillah kaya Kuma ka kwashe har da nawa ka bawa Halima bana bukata. Ta fada a fusace tana shigewa daki inda ya kinkimi kayan ya fice . Ta fito don ga mamakin ta ba zai iya daukar gatsen da tayi mishi ba. Don Haka da sauri ta biyo bayan shi inda taga fitar shi a motar ta Kuma tabbatar da gidan Halimar ya nufa…..

Sai taji kamar tabi bayan shi amma sai ta share ta barshi har ya dawo.

Ya karaso gidan Halima kanshi tsaye ya shigo ya sameta zaune ta bude littafin hisnul muslim tana dubawa da sauri ta rufe tana mishi sannu da zuwa amma fa fuska a hade.

Ya yi murmushi Yana Kare Mata kallo. “Halima kenan kwana biyu banji daga gareki ba? Tayi shiru bata tanka mishi ba.

Ya dire mata kayan jibgi guda. “Ga Kaya Nan keda Husna kuyi fitar salla. Ga kuma na yarana suma .

“Gaskiya ba zan karbi kayan ka ba Alhaji Aminu matukar ba janye maganar nan kayi a tsakanin mu ba.

Ba kuma zan iya janyeta ba Halima sai dai kiyi hakuri dani gaskiya tunda na gane babu wata hujja da tasa kike kin aminta dani sai Wasila. Da ace wata hujjar Kika kawo min tun farko ba Wasila ba wata na aminta dake. Don Haka ga Kaya Nan kiyi amfani dasu ko ki kone su Ni dai na Baki ko ba komai zanji dadi na bawa wadda zuciya ta ke marari. Kuma zanje masanawa wurin Hajiya in fada mata yadda muka yi nasan ita zata fahimci abinda ke kika kasa fahimta.

Yana gama fadar hakan ya fice ya barta da dukan kirji don tasan zuwan shi ga Hajiyar tamkar yayi nasara ne akanta musamman idan tayi duba da yadda Hajiyar ke da kulafucin kudi da yayi mata yayyafi ya gama siye imanin ta kafin ta uzxura Mata da lallai sai ta Auri Aminun.

Ya koma gida ya iske tijarar Wasila dake dakon jiransa.

“Ai kai da kanka ka dade da sanin ko zan yarda ka kawo wata mace da sunan matarka a gidan nan to ba dai irin su Halima ba wallahi. Macen da na santa na san ko wacece ita. Matar da na taimaka da zanin daurawa ka ce itace kishiyar da zaka yi min kyauta da ita har kana hada matsayi na da nata. To na rantse maka zanga ta inda hakan zata yuwu sai dai ko bayan raina wallahi.

“Sai ayi bayan ran naki, ko nayi miki alkawarin in kin mutu ba zanyi Aure ba? To maida hankali ki kureni na rantse miki za ayi babu ke don haka ki daina kallon Halima a wadda kika taimaka ki kalleta a me daura zanin da kike daurawa. Bi ni a sannu in ke kanki hayaki yake fitarwa ni nawa wutar ce ke fita. Kaya Kuma tunda baki so na kaiwa Halima sai menene? Mota ma zan siya mata irin taki sai menene?

Ta bi shi da kallon mamaki don ta san duk abinda ya fada zai iya aikatawa. To ina mafita?

<< Hawaye 8Hawaye 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×