Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Hawayen Jini by Yareema Shaheed

Ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi don aibata wani ko wata ba ko muzantawa ba, kuma ban yarda da a canja min labarina ko canja sunan wani abu daga ciki ko kwaikwayon labarin ba ba tare da izinina ba, yin hakan mutum zai fuskanci hukunci.

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ

Sanye yake da riga da wando na shadda kalar sararin samaniya (Sky blue) wanda ya yi masa matuƙar kyau, agogo ya ɗauko ya ɗaura a hannunsa na hagu tare da zura zoben azurfa a babbar yatsarsa na hannun dama sanan ya sa wula kalar sararin samaniya da takalmi.

Sallama abokinsa Mahfuz ya yi tare da shigowa ɗakin ya ce,

“Haba! Abokina Hamdan ka barmu a waje tun ɗazun muna ta tsimayen jiranka, ya kamata ace zuwa yanzu ka gama shiryawa domin mu samu damar halartar gurin bikin walimar da wuri.”

“Hmm! Mahfuz kenan duk saurinka dai ka bari na gama shiryawa a tsanake, domin yau yana daga cikin ranar da ba zan taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwata ba, don haka kaga dole na tsaya na kimtsa a tsanake domin faranta wa zinariyata Nuraida wadda za ta kasance matata gobe iwarhaka In Sha Allah (My wife to be).”

“Hmm! Duk na ji Hamdan amma ai dai ka bari goben ya yi ko a ɗaura domin gaggawa ai aikin shaiɗan ne.” Ya ƙarashe maganar tare da yin dariyar zolaya.

Hamdan da Mahfuz sun gama shiryawa tsaf. don haka suka nufi hanyar fita gidan. Suna dosowa daidai kofar falon suka ji ɗan hayaniya na tashi. Da sauri-sauri suka ƙarasa domin jin abin da ke faruwa.

Isarsu gurin ke da wuya Hajiya Mero ta zuba masu wani wawan kallo tare da ajiye nauyayyar ajiyar zuciya ta ce, “Hamdan dama yanzu zan aika a kira mun kai sai kuma ga shi ka fito faɗuwa ya zo daidai da zama.”

Jin haka ya sa suka samu guri suka zauna akan kujera mai cin mutum biyu, domin jin abin da ke faruwa.

“Ina za ku je ne naga kun sha ado tare da sa kaya iri ɗaya haka? Ji suka yi gabansu ya yanke ya faɗi, domin maganar Hajiya Mero ya yi matuƙar dukan zuƙatansu tare da basu mamaki, a tunaninsu ai ta san komai na shirye-shiryen bikin da za ayi gobe. Domin ita ce ke shirya komai da za a gudanar a bikin a matsayinta na uwar ango Hamdan.

Shiru suka yi suna kallon-kallon juna sun kasa magana.

“Ba da ku nake magana ba kuna jina kun yi kunnan shegu da ni kamar marasa gaskiya ?” A jiyan zuciya Mahfuz da Hamdan suka yi suka haɗa baki suka ce, “Hajiya za mu tafi Walimar ne mun ma makara domin karfe huɗu da rabi aka ce ga shi yanzu har karfe biyar har…”

Basu gama maganar ba sai ji suka yi Hajiya ta katsesu daga maganar da suke yi ta ce, “Uhm! ku yi mun shiru shashashen banza da wofi.

Gabansu ne ya yanke ya faɗi don jin furucin Hajiya Mero, “To wai mai yake shirin faruwa ne mai Hajiya ne nufi?” Duk wannan zancen sun yi shi ne a cikin zuciyarsu domin Hajiya ka dai za ta warware masu abin da take nufi.

Falon ɗaukar shiru ya yi kamar babu kowa a ciki na tsawon mintunan da ba za su gaza biyar ba. Miƙewa tsaye Hajiya Mero ta yi tare da yin safa da marwa a cikin falon hannunta na haɗe a bayanta magana ta fara ta ce,

“Hamdan! Hamdan!! Hamdan!!!?”

“Na’am Momy.”

Sau nawa na kira sunanka?”

Cikin sanyayyar murya ya ce, “Sau uku.”

“Hamdan sanin kanka ne duk faɗin duniyar nan ba ka da kamata haka ne?”

“E! Momy.”

“Da kyau! Hamdan bari in fada maka wasu abubuwa wanda ba ka sani ba, tun kana tsumma mahaifinka ya rasu ya barni da kai, lokacin ba za ka huce wata biyu ba a duniya, na fuskanci ƙalu bale daban-daban a rayuwarmu kafin ka girma, na shayar da kai na tsawon wata goma sha takwas tare da ɗaukar cikinka na tsawon wata tara, shin duk wannan abubuwan da na yi ma za ka iya biyana?”

“A’a Momy har abada ban isa na iya biyanki ba, ladanki na gurin Allah (S.W.A) mai kowa mai komai.”

“Da kyau! Yanzu ka yarda duk umarnin da na ba ka za ka yi min?”
“In Sha Allah! Zan yi miki Momy in dai bai saɓawa umarnin Allah ba.”

“Da kyau! Yau ka tabbatar min ni ɗin uwarka ce, don haka abin da nake so da kai shi ne, ka janye auranka da Raslima, yanzu-yanzu ba tare da ɓata lokaci ba ka kirata a waya ka ce ka fasa aurenta, domin har abada ba zan iya zama sirikarta ba.”

“Innalillahi wa inna ilaihim rajiun.” Duk illahirin mutanan da ke falon suka furta, domin a tunaninsu ba su taɓa tunanin Hajiya Mero za ta yanke irin wannan mummunar hukuncin ba.

Ta sowa Hamdan ya yi daga kan kujerar da yake zaune ya je ya zube a gaban Hajiya Mero tare da rike ƙafafuwanta ajiyar numfashi ya sauke cikin sassanyar murya mai kama da kuka ya fara magana tare da goge hawayensa da ke zubowa, “Momy me ya sa kike son rusa tubalin da muka daɗe muna ginawa ni da Raslima?” “Momy a iya sanina da tunanina kina matuƙar son Raslima amma yau kuma son da kike mata yana neman ya kowa ƙiyayya, zan so ki fahimtar da ni abin da ta yi mi…ki.”

Wanke Fuskar Hamdan ta yi da mari har guda uku tare da daka masa tsawa da hanɓare shi daga cikinta ta ce…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Hawayen Jini 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×