“Lallai wuyanka ya isa yanka Hamdan. Yau har ni kake tsarewa da tsabar idanuwanka akan sai na faɗa maka dalilin da ya sa na yanke wannan hukuncin ko?” “Alhalin ka yi min alƙawarin yi min biyayya tare da bin umarnina, duk ina tarin alƙawarin da ka ɗaukar min?”
“Momy wannan hukuncin da kika yanke ya fi ƙarfin tunanina, ban taɓa kawo irin wannan buƙatar za ki nema ba a gurina ba, ki tausaya min Momy wallahi zan iya faɗawa damuwa a ƙarshe ya haifar mun da ciwon da zai yi wuyan warkewa, Don girman Allah ki yi haƙuri Momy.”
“Hmm! Hamdan?” “Na’am! Momy?” “Bari na ɗauko ma wayana maza ka amsa, ka kira Raslima yanzun nan ba tare da ɓata lokaci ba, ka ce mata ka fasa aurenta ta nemi wani.” Gabansu ne ya yi mugun faɗuwa tare da miƙewa tsaye dukkansu suna alhinin irin abin da Momy ke shirin alkatawa.
Mahfuz ne ya taso ya zo daf da inda suke, domin tun da aka fara hatsaniyar kasa cewa komai suka yi tare da mutanan da ke falon.
“Don girman Allah Momy ki yi haƙuri abi komai a hankali, domin a samu mafita domin kanmu a ɗaure yake, ba mu san dalilin ki na cewa ba za a yi auren nan ba Momy.”
“Don Allah dakata Mahfuz! Na riga na gama yanke hukunci in dai ni na haifi Hamdan to aure an fasa yinsa ba zan iya haɗa zuri’ata da Raslima ba na janye har abada, ɗana ba zai auri gawa taƙi rami ba.”
Tana gama maganan ta zage zip ɗin jakarta ta ɗauko wayarta ta miƙa masa, babu yadda Hamdan ya iya sa hannu ya yi ya amsa a kasale, hannunsa ɓari yake ta yi tare da bugun zuciya, ji yake ina ma ace mafarki yake yi ba a gaske ba ne ba. Kira ɗaya wayan Raslima ya fara (Ringing) ƙarar ƙararrawa.
*****
Gidan cike yake da mata da maza ‘yan walima, Amarya Raslima na zaune a kan kujerar falonsu ita da ƙawayenta, sun yi ankon hijjabi kalar ruwar foda (Pink color) suna jirar isowar Ango Hamdan tare da abokansa, domin ƙawayen na ta sun fara zaƙuwa da rashin zuwan nasu har yanzu ga shi magariba ya fara halartowa.
Wayan Raslima ne ya fara ƙarar kururuwa, babbar ƙawarta ce Hajara ta miƙa mata wayan domin dama ita take riƙe da wayan nata. Raslima ta ce, “samin wayar a (Hands free) a lasifika.” Ta faɗi haka ne ba tare da ta duba mai kiran ba.
Ɗaga wayar ke da wuya suka ji an ce, “Assalamu alaikum.” Cikin shasshekar kuka duk da cewa ya yi koƙarin ganin ya danne damuwarsa amma abin ya faskara. Wannan shi ake kira ranar wanka ba a ɓoyan cibi. Zuciyar Raslima ne ya yi mugun faɗuwa, domin ko a mafarki ta ji muryar masoyin nata ko da nishinsa ne za ta iya ganewa bare kuma sallamarsa, cikin ɗauriya da faɗuwar gaba Raslima ta ce, “Subhanallah! Hubbina me ke da munka ne ba ka da lafiya ne?” Hamdan fashewa ya yi da matsanancin kuka mai shiga ran mai sauraro, ya yi ƙoƙarin ganin ya danne kukan nasa amma abin ya faskara, jin hakan ne ya sa hankalin duk ƙawayen nata ya dawo kan wayan da suke yi.
Jugum-jugum suka yi su na sauraron wayar nasu, Raslima ƙara rikicewa ta yi tare da goge wahayen da ya fara ambaliya daga kumatunta. Cikin karyewar murya Hamdan ya ce, “Ras….li….ma! Ina mai baki haƙurin abin da zan faɗa miki wallahi bayin kaina ba ne.” Saurin magana ta yi ta ce.
“Wani ne ya mutu Hubbina?” Don Allah ka faɗa min abin da ke faruwa ko hankalina ya kwanta.” Fisge wayar hannun Hamdan Hajiya Mero ta yi ta kara a kunnata ta ce, “Ke Raslima! Ki saurare ni da kyau da kunnan basira. Ni Hajiya Mero mahaifiyar Hamdan na soke aurenku ke da ɗana Hamdan har abada.”
Tana gama faɗa ta katse wayar.
“Innalillahi wa inna ilaihim rajiun! Duk illahirin mutanan da ke tare da Raslima su ke cewa.
Raslima kam in ban da ambaton sunayen Allah babu abin da take yi, nan da nan magana ya bi ya karaɗe illahirin gidan bikin cewa an fasa auren Raslima. Masu tsegumi na yi masu alhini na yi.
Hajiya Salma ce mahaifiyar Raslima, suke zaune a uwar ɗaka (Bed room) ita da ‘yan uwanta tare da Raslima da take kwance akan gado, tun lokacin da abin ya faru ba ta ƙara yi ma kowa magana ba sai dai kallon-kallo take ma mutane, hawayenta har yanzu ci gaba da fitowa yake.
Hajiya Bilkisu ƙawar Hajiya Salma ta ce, “Ai wannan cin mutuncin da me ya yi kama, a ce sai ana gobe biki ga shi duk anfara shagali yanzu an tozartamu, nifa ta shi za mu yi mu je har gidan mu mayar da martanin tozarcin da aka yi mana, kuma ai ɗa bai fi ɗa ba wallahi.”
“A’a! Hajiya Bilkisu mu barsu da halinsu, Allah ya nufa ba mijinta ba ne shi ya sa mu yi haƙuri.”
“Duk da haka yana da kyau mu je mu ji mai ya haddasa hakan.” To shi kenan ku shirya ku je amma don Allah kar ku biye masu ata da fitina.
Ko da suka je gidan su Hamdan, sun sami Hajiya Mero zaune ita da wasu matan, bayan sun gaisa ne suke tambayar Hajiya Mero dalilin da ya sa ta ce ɗan ba zai auri Raslima ba. Miƙewa Hajiya Mero ta yi ta ce, “ku ba ni minti biyu ina zuwa.” Bayan ta shiga ɗakin ba ta fi mintuna uku ba ta fito ɗauke da wani takarda a hannunta.
Miƙa masu Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Ku karanta ku gani da ma kunsan ‘yarku na ɗauke da irin wannan cutar da baya jin magani kuke son ɗana ya auri alaƙaƙai?” To anyi gwajin aure duk da cewa Hamdan ya ɓoye min ya gumma ce ya aure gawa taƙi rami. Shigansa wanka ne na je domin mu tattauna, shi ne na samu yana wanka sai idanuna suka hango min wannan takardar akan teburinsa. Don haka babu ni babu haɗa zuri’a da ku, ku tashi ku bar min gida gayyar na ayya.”