Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Ina Matsalar Take? by Rahma Sabo

A tsaye ya ke a gaban rariya, hannunsa ɗauke da soso da kuma ruwa ya na fama dirza wani ɗan matsakaicin laulawa na kamfanin HAMILTON. Nesa da shi kaɗan matashiyar mace ce zaune a kan tabarma, gabanta kuma tire ne cike da shinkafa ɗanya ta na na tsincewa. Cikin matuƙar kula soyayya da shaƙuwa ya kalle ta ya ce.

“Mama ni fa yanzun na canja shawara na fasa zama likita, soja na ke son zama.”

“Soja?” Ta yi hanzarin katse shi ta hanyar watsa masa tambaya cikin sanyin jiki.

“Soja na ke son zama mama, burina a duniya na yi ƙoƙarin na ga na dakatar da wannan balahirar da ke abkuwa a ƙasar nan. Jiya abokina ke ba ni labari wai an yi garkuwa da ƙanin Innarsa a wani gari, mu na fama da tsananin matsalar tsaro a ƙasar nan.” Bakinsa kawai ta ke kallo tunda ya fara magana, kai ka ce da wani su ka zauna ya rubuce yankuma tura masa a ƙwaƙwalwa shi kuma ya haddace su tsab.

Ƙwaƙwalwarsa na da tarin abin mamaki, tamkar ƙwaƙwalwar zinare ko ta azurfa haka ta ke. IQ ɗinsa ya na aiki sosai dan a ƙalla zai kusa kaiwa 70%100, tunaninsa sak irin na manya ne aiyyukansa ma irin na manyan mutane ne.

“Mama na ga kin zuba idanu ki na kallona, ko sojan ne ba kya buƙatar na zama?”

Girgiza masa kai ta yi, sannan ta ce.

“Kokaɗan Safwan ina mamakin yadda Allah ya azurta ka da kykkyawar ƙwaƙwalwa, mai zurfafa bincike da hangen nesa ne. A burina ni kuma ka tsunduma harkokin siyasa domin na fi ta’allaƙa matsalar tsaro da rashin kyakkyawan shugabanci.”

“Mamana matsalar ƙasata na da yawan da idan aka baje ta a faifai, kare ma ba zai doshi gurin ba. Mu mu na da namu laifin a matsayinmu na mabiya; shuwagabanninmu ma akwai nasu laifin na wancakali da nauyin sauke haƙƙi (sense of responsibility).
A al’adar rayuwa akwai abinda ake kira da division of labour, Allah tun kafin ya halicci kowane bawa sai da ya fara fitar da division of labour. Mace za ta bada fili ko kuma wani wadi bayan ta gama tsabtace shi ta hanyar fitar da jinin haila inda ta tanaji ƙwayaye wanda cikin hikima da Buwayar jallah sarki zai aiko da ɗa namiji ya shiga wannan wadin ya fasa waɗancan ƙwayaye nata ya zuba tasa ajiyar.

Tun daga ranar da ya fasa waɗancan ƙwayayen, shikenan ya kammala nashi aikin daga ranar mace za ta fara nata. Kullum cikin ƙunci da rashin walwala ina son wancan ina kuma ƙin wancan har ɗan’am ya iso duniya ya na sha ne daga jinin jikinta ta wani ɗan tantani da a Turance a ke kira da umblical cord, ya na rayuwa ne daga abinda ta samu ta ci.

Mu saka batun haihuwa a mala mu ɗauki batun division of labour na shugabanci, tabbas a nawa kallon da kuma hangen a matsalar ƙasar nan za ai 50%50 ko kuma 80%50. Wannan ɗan wani sauƙaƙƙen arisimeti ne, manufata ita ce gwamnati laifin gwamnati da na mabiya zai iya yin kunnen doki ko kuma na mabiya na gwamnati zai iya yin sama na biya ya yi ƙasa.”

“Anya kuwa? Talakawa za su iya kunnen doki da shuwagabanni a ƙasar nan, gurin ɗaukar alhakin duk wata balahira da ke faruwa?”

“Tabbas za su iya”. Ya bata amsa cikin murmushi, bayan ya dakatar da dirza laulawar da ya ke yi ya ce,” misali mu ɗauki division of labour a nan gidan, baba shi ne shugaba ni da ke mabiya ki na ganin ba za mu iya kuskuren da za mu iya kamo baba ba?

Wataran ma mu na aikata kuskure sama da nashi kuma ya jureda a ce shi ne zai aikata kuskure sama da namu da tuni gidan nan ya shiga halin-ha’ula’i. Almuhim dai shi shugaba duk ranar da nashi laifin ya rinjayi na mabiya to guri watsewa ya ke domin shi shine turken da ke riƙe da kowane gini muddin turaku su ka zube to daga ranar gini ya tashi a aiki.

Ba wai ina son na sanar mi ki ga gurin da matsalar ta ke ba ne, amma wataran ko bayan ba na kusa da ke da kanki za ki karantu za kuma ki gane a ina matsalar ta ke.”
Lallai gamsassun bayanai daga bakin nagartattun mutane su ke fitowa, idan Allah ya so sai ya baka tarin ‘ya’ya da za su zamo maka taron kwari da hama. Idan kuma ya so sai ya azurta ka da samun nagartacce kuma kimtattsen ɗa ɗaya tilo wanda kowa zai gani ya yaba. Ita kam ta wannan bigiren sai dai ta kawai ta rinƙa aikawa Buwayi gagara ƙirga tarin shukura, da ya azurta ta da samun Safwan duk da kicimillin rayuwa da ta fuskanta kafin a bata shi ɗin. Ba za ta taɓa manta yadda rayuwa ta zo mata tun daga ranar da ta buɗi idanu ta fara fahimtar me ke wakana a duniya, ta ke fuskantar tarin ƙalubale cukurkuɗaɗɗu masu matuƙar sanya mutum ruɗani da kuma jefa shi a wani baƙon yanayi muddin ya gaza yarda da a gurin Allah kunfayakunu kaɗai ta ke.

Kallonshi ta yi cikin tsananin so da ƙauna, irin na ɗa da uwar da ke tsananin kula da juna ta ce.

“Shikenan idan ka samu aikin soja, za ka tafi bariki ka tare za ka bar zama da ni ko?”
Girgiza mata kai ya yi ya ce,” a’a ina tare da mamata, ɗauke ki zan yi na kai ki barikin mu cigaba da rayuwarmu tare.”

Katse shi ta yi ta ce,” ni fa tsorona Allah tsorona shigarka ƙasar nan, da ran talakawan cikinta daidai ya ke da na bayi lokacin mulkin mallaka. Sojan ƙasar nan bai da wata ƙima ko mutunci bare a sa ran bashi kariya, kullum sojojin ƙasar nan cikin ƙaƙuzanci su ke haɗi da mayar da hankali gurin aiki burinsu su kai ga ƙasar nan tundun mun tsira, amma ita ƙasar haka za ta wancakalar da rayukansu ta tursasa su zuwa gurin da idan su ka je sun yi bankwana da duniya sai dai a naɗo su a tutar ƙasa a je a haɗu a yi musu jana’iza ba a ko damu da sai danginsu sun ƙaraso sun musu kallon ƙarshe ba.” Kalaman dariya su ka bashi, duk da ya san gaskiya ta faɗa amma kuma mazantakar na nan a zuci cikin dakiya ya ce.

“Mama kin manta sadauki ki ce min tun ina tsumma? Don me yau ɗaya za ki sare da sadaukinki? Duk inda aka tura ni ko da turin je ka mace a ka min, ki sanya a ranki cewar sadaukinki zai dawo har gabanki ɗauke da tutar ƙasa maimakon a naɗo ni. Ina raira taken ƙasarmu haka zan zo na ɗaura mi ki tutar ƙasar da na hidimtawa da dukkanin lokacina.

Ki dai taya sadaukinki da addu’a mamana.”

Nisawa ta yi daga zuzzurfan tunanin da ta shiga, haɗi da sakin siririyar ajiyar zuciya. A fili ta furta,” ko’ina sadaukina ya shiga? Ko da wa zan yi hira mai ma’ana da za ta maye min gurbin ta sadauki? Ba ni da kowa ba ni da komai sai Sadaukina, sadauki ka dawo gare ni.”

“Ki na da Amina, ke fa ‘yar dangi ce ta ko’ina, a na sonki ana ƙaunarki amma kin yi fatali da so da kuma ƙaunar da ake mi ki. Kin zaɓi ki zauna cikin kaɗaici da rashin larewa kin zaɓi ki rungumi ƙaddarar rayuwa da ƙasƙantaccen bawanki. Ki yiwa kanki tunani mai kyau Amina.” Da waɗan nan kalaman ya yi sallama, domin tun daga ƙofar gida ya ke jiyo gunji da kuma sambatunta. Tada ta zaune yayi daga durƙushen da ta ke, ya ce.

“Amina lokacin da za ki fuskanci gaskiya ya ƙarato, lokacin da za ki gane cewa annabi ya faku ya yi. Lokacin da za ki juya zuwa ga ƙaddarar da ki ka fito fa ya cika; ya kamata a ce wa’adin da ki ka kwasarwa kanki ya ƙare ki hankalta.

Yanzun kuɗi su ne mutunci da cikar daraja, ki koma zuwa ga suturarki, ni’ima da jin daɗinki ki bar wannan rayuwar ta fatara da talauci.”

“Ba na jin cewar lokacin da zan koma, zuwa ga rufaffiyar ƙofar da na rufe da hannuna ya yi. Ba na jin ina da ƙumajin da zan tunkari akuyar da na kora a baya da sunan neman yafiya ba, ba na jin cewar fitilar da na watsawa ruwa zan iya kunnata a loton da na ke ra’ayi.

Dama shine makamin da na ƙera na ke kuma tunanin zan iya yaƙar koma wani irin ƙalubale ne, wannan makamin ya salwanta farin cikina ya ƙaura ya koma inda ya fito ban jin zan ƙara ƙera wanda ya kai shi daraja.

Ka sanar da ni nasarar da ka samo mana a fitarka ta yau don kawai.”

“Babu wata nasara sai ma ƙarin faɗuwa sama da kullum.”

Kafin ya ankara sai ganinta ya yi ta yi warwas a tsakar gidan, taɓata ya shiga yi haɗi da kiraye-kirayen sunanta ƙiƙam ya sojan da ke tsaron bakin boda haka ya ga ta yi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ina Matsalar Take? 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.