Bakin window tazo ta tsaya har sai da ta hango shigowar Abi. Tana tsaye a gurin har ya fito daga motar tasa ya shiga cikin gidan shima tayi masa kallon ƙarshe ba tare da ta sani ba. A hankali ta buɗe ƙofar dakin ta, ta sanɗa a hankali har ta bar palon, sannan ta zagayo ta bayan motoci guda ukun dake cikin gidan. Tana zuwa bakin get ɗin gidan ta tura ya buɗe sannan tasa kafarta a waje. A hankali ta juyo tana kallon gidan nasu da hasken wutan lantarki ya haskaka shi sosai. Duk taku ɗaya. . .