Dama tun kafin samuwar cikin kullum a ƙorafi yake akan me ya hanata yin wani cikin har yanzu, ita kuma sai ta ce ai dama shine mai bada cikin sai yazo ya saka mata shi idan ya isa, sosai yake ƙin yarda da ita, sun sha zuwa asibiti likitoci suna tabbatar masa da cewar babu ciki a jikinta. Kuma bai taɓa kawo cewar tayi tsarin iyali bane, kuma bai isa yace ko bata aihuwa bane domin kuwa ta haifa ya gani. Kafin samun wannan cikin har magana yake gasa mata na cewar da yake cikin shege ne ai ta. . .