Skip to content

Ina So 1

Part 1 of 1 in the Series Ina So by Muntasir Shehu

A gurguje Halima ta shiga bayi ta watsa ruwa ta fito ta shige ɗakinta, atampa ta zaɓo cikin kayanta ta sanya, ta ɗora zumbulelen hijabinta a sama sannan ta kawo niƙab ta yafa. Baƙin tabarau ɗinta dake ajiye a saman drawer ta ɗauko ta sakaye idanunta, sannan cikin sauri-sauri ta ɗauki agogo ta ɗaure tsintsiyar hannunta na hagu da shi.

Wayarta da ‘yar karamar jakarta ta hannu na yashe a saman katifarta ta sunkuya ta ɗauka sannan ta zura takalmanta marasa tudu da suka sha wanki da mai sai sheƙi suke yi.

Ta fito daga ɗakin a hanzarce, daidai lokacin Umma ita ta fito daga ɗakinta, tsayawa ta yi tana ƙare mata kallo.

“Da gaske dai wai Halima ba za ki tsaya ki karya a gida ba?”

Sake duba agogon hannunta ta yi, ƙarfe takwas har da mintuna uku, ta girgiza kai. “Umma lokaci ya ƙure sosa, takwas har ta wuce, gwara in tafi da breakfast ɗin na ci a can, in na ce zan tsaya ci lokaci zai ƙara ƙure min, na san kafin in je ma sai wajen takwas da rabi.”

Gyaɗa kai Umma ta yi cikin sallamawa ta ce. “Shikenan na sa Auta ma ta haɗa miki komai a cikin kula, bari in ɗauko miki.” Ta juya ta koma ɗakin, jim kaɗan ta fito riƙe da wata madaidaiciyar kula ta miƙa wa Halima.

Cikin girmamawa Halima ta karɓa tare da yi wa Umma sallama. “Na wuce Umma.”

“To Allah ya tsare ya ba da sa’a.”

“Amin Umma na gode.”
“Kar ki manta ki yi addu’a kafin ki fita.”

“In sha Allah Umma.”
Ta fice tana sauri.

Allah da ikonSa ba ta sha wahalar samun abin hawa ba, tana tsallaka titi mai adaidaita na tsayawa, matar da take ciki ta sauka ita kuma ta hau ta yi masa bayanin inda za ta sauka.

Duk gudun da mai adaidaita sahun yake yi sai take ganin kamar tafiyar kunkuru ake yi, ji take kamar ta yi fiffike ta tashi ta isa inda take son zuwa kafin ta ƙara makara sosai.

Tun kafin a ƙarasa gurin ta zaro adadin kuɗin da za ta biya mai adaidaita ta riƙe a hannunta, Allah ya taimake ta canji ne a hannunta don haka tana sauka ta miƙa masa ta gaggauta tsallakawa ta nufi katafaren gingimemen shahararren babban kantin da babu ce kawai ba a sayarwa a cikinshi.

PRINCE ALI HADI KARMA SHOPPING MALL shahararren kanti wanda kusan kaf faɗin jihar nan babu wani kanti da ya kai shi girma da kawo kaya na gani a faɗa, suna da manyan rassa a garuruwa daban-daban cikin faɗin jihar nan. Amma wannan shi ne babban shalkwatarsu.

Cikin saurin da ta kwaso tun daga gida ta isa cikin kantin bayan ta gaishe da securies. Tun daga ƙofar shiga ta fara shan jinin jikinta sakamakon abin da idanunta suka gane mata, gabanta ya ɗan faɗi kaɗan, ta shiga waige-waige da hange-hange daga nan inda take a tsaye.

Ba komai ne ya saka ta shiga wannan yanayin ba face ganin dukkan ma’aikatan kantin a tattare a waje ɗaya, gabansu kuma wani matashi ne zaune a kan kujera ya tasa su a gaba.

A ‘yar tsayuwar da ta yi ta ga ma’aikatan sun fara gabatar masa da sunayensu da kuma matsayin aikin da suke yi a kantin, duk wadda ko wanda ya faɗa sai ya ba shi umarnin ya wuce.

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke sannan a hankali cikin ɗari-ɗari ta fara taku zuwa ciki. Kafin ta ƙarasa ta ƙara tsayawa gabanta na faɗuwa, ta soma addu’a a cikin ranta. Karaf ta ji muryar wata abokiyar aikinta ta yi mata magana da cewa.

“Ki ƙaraso mana Sadiya!”

Wannan magana ita ta saka ta zabura da sauri ta taka ta ƙarasa, shi kuma saurayin da sauri ya yi wani irin juyi don ya ga wadda aka yi wa maganar.

A hankali idanunshi suka sauka a kanta, mamaki ya kama shi nan take sakamakon yanayin shigar da ya gani a jikinta. Kafin kowa ya yi magana tuni ya buɗe nashi bakin da muryarshi mai karsashi ya ce.

“Ke kuma fa?”

Kasa yin magana Halima ta yi, sai wannan abokiyar aikin tata mai suna Ladidi ce ta yi saurin cewa “Ranka ya daɗe ita ma ma’aikaciya ce, ita ce sabuwar cashier.”

A zabure ya ƙara kai dubanshi gare ta, sama da ƙasa ya fara kallon ta, ya zare baƙin gilashin dake idanunshi tare da miƙewa tsaye, agogon hannunshi ya duba sannan ya ɗago ya sake tsare Halima da kallo da daskararrun idanunshi masu matuƙar sanya tsoro a zuciya.

“Sai yanzu kike zuwa aiki? Ƙarfe nawa agogonki ya ce?”

Da sauri ta duba agogon hannun nata, Tara saura mintuna uku. Ta yarfe hannaye. Duk da ba ta san kowaye shi ba da matsayin shi a kantin amma a abinda idanunta suka gani ya tabbatar mata lallai mai naira shi yake luntsuma hannu ya ɗauko alkakin ƙasan kwano, don haka ba ta san lokacin da ta fara zuba ba.

“I’m sorry Sir. Makara ba ɗabi’ata ba ce, yau ma matsala aka samu ne, ina roƙon a yi min afuwa…” Ta ƙare maganar da ajiye kular abincinta sannan ta haɗe tafukan hannayenta biyu ta ɗora su a saman haɓarta, alamun roƙo.

Kallon ta kawai yake yi har ta gama, ya ƙara ɗaure fuska tamau ya ce. “Tabbas na san irin ku masu wasa da aiki da ƙin bin dokokin aiki… Saboda irin ku dama na dawo ƙasar nan don in ga yadda kuke tafiyar min da dukiyar mahaifi, ga shi a karon farko na fara kama ki da laifi.”

Halima ta ƙara rikicewa ta shiga roƙon shi tana tabbatar mishi wallahi kowa zai ba da shaidar ba ta makara, sannan in an duba register duty ta kullum ma za a gani ba ta makara.

Matse kafaɗa ya yi cikin halin ko’inkula ya ce shi sam wannan bai dame shi ba, shi dai ya kama ta da laifi kuma kar ta kuskura ya sake kama ta a karo na biyu.

Cike da murnar ta kuɓuta ta juya da sauri da nufin isa mazaunin aikinta, kwatsam ta ji ya daka mata tsawa.

“Dawo ban sallame ki ba!”

Ta koma ta tsaya cikin matuƙar jin haushi, tun tafiya ba ta yi nisa ba ta fara jin haushin gayen nan, haka kawai tana aikinta lafiya-lafiya zai zo ya fara kawo mata tarnaƙi.

Sai da ya gama sallamar kowa saura ita kaɗai, jikinta sai ɓari yake don ba ta san me zai kuma ce mata ba.

Ya waiwayo gare ta sosai.

“Cire wannan glasses ɗin da wannan abin da kika saka a fuska.”

Gabanta ya faɗi sosai yadda har sai da ta ji zafi a ƙirjinta saitin zuciyarta. Nan da nan ta fara karanto Innalillahi da hasbunallahu tana maimaitawa.

Ganin har kamar mintuna biyu da ba ta umarnin da ya yi kuma ba ta cika ba ya sa ya ƙara ɗaga murya.

“Cewa fa na yi ki cire wannan glasses ɗin da wannan abin munafurcin da kuke rufe fuska da shi ku ba larabawa ku ba ‘yan tawaye ba!”

Hawaye ta soma ji na taruwa a idanunta, muryarta da rauni sosai ta yi ƙasa zuwa gwiwoyinta.

“Ka yi hakuri don girman Allah, ba zan iya cire glass da niƙab ɗin fuskata ba, a haka aka yarda aka ɗauke ni aiki a haka kuma nake aikin… Ina roƙon don son da kake yi wa mahifinka kar ka matsa min a kan sai na cire…”

Duk suka yi shiru, ita tana haɗiyar kukan da ke ta hanƙoron taso masa shi kuma mamakin furucin nata ne ya kashe shi.

Suna a wannan yanayi har tsawon wasu daƙiƙu, miƙewa ya yi daga kan kujerar da yake zaune ya taka ya isa gabanta.

“Kina iya tashi ki tafi.”

Tuni ta miƙe cikin sauri ta fara tafiya.

“Wannan ba naki ba ne?” Ya faɗa yana nuna kular da ruɗewa ta saka ta mantawa da ita. Ta dawo da sauri ta ɗauka ta bar gurin.

Ya ɗan jima a tsaye a nan yana aika mata kallo inda ta je ta zauna, gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi ta kasa kataɓus ɗin komai sai kame-kame da danne-dannen computer take yi.

Kiran wani masinja ya yi ya sa shi ya janye kujerar da ya zauna shi kuma ya nufi escalator ya hau zuwa sama ofishin manaja.

Manajan ya tashi da sauri ya miƙa masa gaisuwa.

“Barka da shigowa ranka ya daɗe!”

“Yawwa Malam Jafar.”

“Bismilla ga guri ka zauna.”

Bayan ya zauna ya dubi manaja. “Akwai wata ma’aikaciya cikin ma’aikatan nan wadda take aiki da fuska a rufe?”

Gyaɗa kai Malam Jafar Manaja ya yi. “E ranka ya daɗe, akwai ta, Halimatu Sadiya Ibrahim. Tana da larura ne a fuskar tata, dalilin da ya saka ba ta iya buɗe fuskar kenan.”

“A hakan kuma kuka ɗauke ta aiki?”

“Ranka ya daɗe Alhaji ne da kanshi ya ba da umarnin a ɗauke ta, saboda duk cikin ma’aikatan da suka nemi aikin takardunta sun fi kyau, kuma mun jarraba ta tana da experience sosai.”

Ya yi shiru yana juya wasu zaren zantuka a zuciyarshi. Zuwa can ya miƙe ya karkaɗa kafaɗa sannan ya ce. “Shikenan.”

Ya juya ya fice, Malam Jafar Manaja ya bi shi da addu’ar Allah ya tsare.

A can ɓangaren Halima kuwa ta yi ƙoƙarin sanyawa ranta nutsuwa, ta tash ta nufi common room ta buɗe kular abincinta don ta karya kafin customers su fara yawa don an fara shigowa sayayya.

Wainar gero ce mai kyau da Umma ta soya musu, wainar ta tashi sosai ta yi tulu-tulu sai ƙamshi take, miyar gyaɗa ɗin da aka dafa don cin wainar tare ita ma sai zuba ƙamshi take.

Ladidi ta taso daga kujerarta ta nufi ɗakin ita ma. Fuska cike da murmushi ta karasa ga Halima.

“Haba Sad-baby, kin sani sarai yadda nake mugun son wainar Umma shi ne za ki taho ki ci ke kaɗai.”

Halima ta yi guntun murmushi ta ce. “Ni kuwa ina zan kai wannan uwar wainar ni kaɗai? Ita kanta Umma don ta san za ki ci ne ya sa ta zubo da yawa.”

Ladidi ta zauna suka fara cin wainar tare a gurguje. A sannan ne Ladidi ta fara tsegunta mata labarin Ali da wasu daga cikin halayen shi da ta ji ana labari.

Halima ta girgiza kai. “Sai da na ayyana a raina cewa duk yadda aka yi wannan gayen sunanshi Ali, na ga izzarshi da taƙamarshi sun yi yawa.”

“Ai kaɗan ma kika gani, yadda ake bayar da labarin shi wallahi an ce ba ƙaramin tantiri ba ne, ga gadara da taƙama da kuma shegiyar izza da girman kai… Ke dai ki shirya takun saƙar ku da shi tun da kun fara, don an ce ya dawo kenan, shi ne ma zai cigaba da kula da wannan gurin.”

“Sai yanzu na fahimci wani abu Ladidi, wato sunanshi ma aka sanyawa wannan kanti kenan.”

Cikin murmushi Ladidi ta ce. “E mana, sunanshi ne.”

“To a ina ya samo PRINCE ɗin da aka maƙala a sunan?”

Dariya Ladidi ta tuntsire da ita har da tuntsirawa kafin kuma ta ce. “Ki bari in ya fito sai ki tsayar da shi ki tambaye shi.”

Suka cigaba da hirarsu har suka cinye wainar, suka wawwanke hannu sannan kowacce ta koma bakin aiki saboda tuni mall ɗin ya fara cika da masu sayayya.

**

Koda Halima ta koma gida sai da ta labartawa Umma abin da ya faru da ita yau a gurin aiki, suna zaune a ɗaki da dare bayan kammala cin tuwon dare take ba ta labarin.

Ran Umma ya sosu sosai, a duniya in akwai abin da ta ƙi jini to bai wuce a wulaƙanta mata zuri’a ba, musamman babbar ‘yarta bango abin jinginarsu baki ɗaya. Don haka muryarta babu sauti sosai ta ce. “Irin yaran nan ne masu mugun hali masu amfani da ɗarfin ikonsu suna ƙuntatawa mutane.”

Halima ta kai hannu ta kaɗe wani mayataccen sauro da yake ta kawo mata farmaki ta ce. “Sosai kuwa, a yadda Ladidi ta ce ta samu labarin shi ma har shaye-shaye yake, riƙaƙƙen tantiri ne dai.”

“To Allah ya yi mana tsari da sharrin sa, ke kuma sai ki yi taka-tsan-tsan ki mayar da hankali a kan aikinki.” Umma ta ce cikin bayyanar damuwa a allon fuskarta.

“In sha Allah zan kiyaye duk sanadin da zai haɗa ni da shi ma.”

Suka cigaba da hirarsu mai daɗi har dare ya fara yi sosai suka kwakkwanta saboda su tashi da wuri gobe.

***

A ɓangaren shi Ali kuwa yana can tare da abokinshi Sadiq ya labarta masa abin da ya faru a ɗazu da ya je Mall dinsu.

Cike da mamaki Sadiq ya dube shi. “To kuma kai meye na damun kanka a kan batunta? Kawai ka share ta ka cigaba da sabgoginka kar ka ce ma za ka yi sakacin da ma’aikatanka za su raina ka.”

Girgiza kai Ali yake yi ya ce, “Inaaa ai wallahi dole ko ta halin yaya sai na ga fuskar yarinyar nan, sai na ga abin da take ɓoyewa a fuskar tata.”

Dafa shi Sadiq ya yi. “Ka rabu da batun nan my man, tun da ka ce Manaja ma da kanshi ya ce ba su taɓa ganin fuskar tata ba to a kan me kai zaka matsa dole sai ka gani? Ba ka tsoron ka je ka ganewa idonka abin da zai tayar maka da hankali?”

“Daga yanayin muryarta na fahimci lallai fuskarta dole za ta kasance tana da wani abu da zai fusgi hankali, shiyasa nake son ganin larurar da tauye mata fuskar ta tilasta mata sakaye ta a kodayaushe.”

“Mai yiwuwa ma gatsorin haƙora gare ta shi ne take ɓoyewa ko kuma irin matan nan ne da suka yi bilichin ya babbake musu fuska shi ne take wannan sinƙe-sinƙen!” Cikin sigar kashe gwiwa Sadiq ya yi furucin.

Kai tsaye shi ma Ali ya ce. “Ko kuma wataƙila Zabiya ce ma.” Sai kuma ya girgiza kai da sauri ya warware tunanin ya ce. “Kai ba za ta kasance zabiya ba don na ga fatar hannunta, ga alamu ma ba ta da hasken fata sosai.”

“To dai ka san babu yadda za a yi mace ta dinga ɓoye kyawunta, dole wani mummunan abu ne take sakayewa.”

“Shi ne dalilin da ya sa na ji ina matuƙar son ganin me take ɓoyewa ɗin.” Fuskarshi ta nuna furucin daga ƙasan zuciyarshi ya fito.

“Ni raini nake guje maka a wajen ƙananan ma’aikata, kai ba ka taɓa yin aiki da cuɗanya da mutane irin haka ba shi ya sa nake guje maka shiga sabgar ƙananan ma’aikata.”

“Kai ka san babu wata ‘ya mace da take da zarrar da za ta raina ni, da ƙarfin ikona kawai zan yi amfani in tilasta mata ta buɗe min fuskar tata in gani… Na rantse da buwayar ubangiji kwanaki uku ba za su zo su wuce ba ba tare da na ga fuskar yarinyar nan ba!”

Sadiq ya zaro idanu sosai cikin matuƙar ta’ajibi. “Me ya yi zafi haka har da saurin cin alwashi? Kar fa ka sa in fara wani tunani daban kan wannan al’amari!”

“Tunanin na kamu da son ta ko?” Ya saki malalacin murmushi. “Shirme ma kenan, kawai ƙarfin ikona zan nuna wa yarinyar… Haka kawai jikina ya ba ni yarinyar irin masu iyayi da kankanba ne da son nuna isar ba a isa ba, don haka sai na nuna mata irin nawa salon izzar, daga gobe za ta fara sanin wane ne Prince Alee Hayder!”

Gyaɗa kai Sadiq ya yi da alamun shakku a fuskarshi.

Ali ya yi murmushi. “Na san zuciyarka cike take da inkari a kan hakan, amma ka sani za a yi kuma za ka gani…”

Bookmark

No account yet? Register

Share |

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.