Muhsin ya ci gaba da cewa, "Duk halin da ɗan'adan ya tsinci kansa ya kamata ya miƙa lamurransa ga Ubangiji, Shi Zai yaye masa dukkan damuwarsa." Ya tsahirta yana sake kallon ta kafin ya ɗora da, "Ummita don girman Allah ki kwantar da hankalinki, ki fita sabgarsu, ki nuna tamkar ba ki san abin da ke faruwa ba. Ki mayar da komai ba komai ba."
Tsit ɗakin har aka ɗauki wasu daƙiƙu ba tare kowa ya ce ƙala ba, kafin daga bisani Hajiya Amina ta ja numfashi tana ɗorawa da,"Na sani ɗan Hajiya, har yanzu. . .
Ma Sha Allah ƙawata Allah Ys ƙara zakin hannu
Allah ya Kara basira
Allah yakara basira muna godiya