Washegari Innai ta tashi da mugun zazzaɓi ga ciwon ciki, hankalin Baabaa Mero in yayi dubu to ya tashi.
Hana ta zuwa makaranta tayi tunda bata da lafiya ta huta, amma Innai ta tirje sai taje dan suna da test.
Sai da Magaji yazo da kansa kaman zai mata duka tukunna ta haqura da maganan zuwa makarantan amma idanuwanta har da qwalla tana tunanin test na yau da zasu yi.
Baabaa ta kalleta tace "ja'irar yarinya shawaragiya wai ace baka da lafiya ka huta zuwa boko hakanan ka sanya mutane a gaba kana sheshsheqa da gulmammen kuka dan. . .