Skip to content
Part 1 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

A wani yammaci ne, me yalwan iska, yanayin garin yana da sanya nishaɗi, musamman a zuciyoyin ma’abota soyayya. Sai dai ba kowa ke cikin irin nishaɗin ba, kasancewar ba kowa ke ɗauke da wannan kundi na soyayya ba. 

A natse yake tuƙi yana jin kansa yana fizga, yanayin garin sam bai burge shi ba. Kallo ɗaya zaka yi masa ka gane baya ɗaukar raini.  

A bokinsa Jabir da ke gefensa ya ce, “Ji yadda hanyar ta cunkushe. Ko dai Gwamna ne zai wuce?” 

Mujaheed ya zare farin glas ɗin da yake ƙara ƙawata masa fuska yana duban Jabir, kamar ba zai yi magana ba, “Idan Gwamna zai wuce sai a ɗinga cutar da talaka?” 

Jabir bai kai ga amsawa ba, ya kula da abinda ya jawo cushewar hanya, “Jawaheer ce ashe ta fito a mashin ɗinta. 

Yau akwai matsala kenan. Wallahi duk abin hawan da ta samu sai ta daka. Ubanta ya ɗaure mata gindi tana wahalar da jama’a, ta buge wanda ta so ta taka wanda ta gadama. 

Nan da nan zuciyar Mujaheed ta hau zafi. Da mamaki yake duban Jabir, “Kana nufin wancan me hular kwanon mace ce? Waye ubanta da zata taka talakawa ta zauna lafiya?”  

Jinjina kansa ya yi, “Saboda ubanta kazo garin nan, saboda ubanta kake aikin nan, saboda ubanta ka mayar da kanka mahaukaci, ka juya ka koma likita, ka sake rikiɗewa ka koma ɗan dako. A takaice dai mahaifin Jawaheer Shi ne Alhaji Saleh Mu’azu Mai nasara.”  

Mujaheed ya lumshe idanunsa yana jin tsanar yarinyar a ransa, “Allah ya bata iko ta taka wani, ni sai na bi ta kanta da mota.”  

Jabir ya zaro idanu a kiɗime, “Walh da nace ban taɓa ganinka ba. Ta yaya kai da kake aiki akan gidan su zaka tonawa kanka asiri?”  

Bai kai ga magana ba ya ji andaki bayan motarsa yana leƙawa ta madubi ya hango ta zaune da isa akan mashin ɗin. Mujaheed ya ɓalle murfin motar, yana fitowa ya fizgo ta ta faɗi ƙasa, Allah ya taimaketa hular kwanon ya kare fuskarta. Wannan lamari ya jawo wurin ya cika kowa yana mamakin waye wannan mai ƙarfin halin da zai iya taɓa gudan junan Mai nasara? Tana tashi ta cire hular kanta ta ɗaga hannu da nufin marinsa, ya riƙe hannun cikin tsananin ɓacin rai ya wawwanke ta da mari. Daga bisani ya hankaɗeta ta faɗi ƙasa. Wannan ƙasƙanci ne da ba a taɓa yi wa koda mai aikin gidan su ba, bare ita kanta.  

Jawaheer ta ɗago cikin hawaye ta dube shi, a lokacin shima ya sake waigowa. Idanu suka zubawa juna, daga bisani ya ƙaraso gabanta, “Talaka yafi ubanki da kike taƙama da shi daraja. Ki koma ki gaya wa mahaifinki ya canza salon tarbiyya ba irinta iyayensa suka yi masa ba, a lokacin da yake zaune naira goma tana gagararsa. Mahaukaciya, kina ‘ya mace kina ayyukan maza. Idan baki tashi anan ba zan sa kan mota intake ki inga uban da zai tambayeni dalili.”  

Da gaske Jawaheer ta firgita da mutumin da bata taɓa gani ba. Haka ko a wasa bata taɓa zaton akwai me tsaurin idon da zai iya zaginta ba, bare akai ga duka. Jabir ya riƙe kansa yana Salati. Haka mutane da yawa Mujaheed ya share masu hawaye, don haka suka ɗinga yi masa kirari da Sadauki. 

Tana kallo ya shiga motarsa, a lokacin iska ya kwashi ɗan siririn gyalen da ta ajiye a hannun mashin ɗin, ya watsa shi akan fuskar Mujaheed, wanda ya yi dai-dai da tayar da motarsa ya yi gaba. Tare da sa hannu ya yaye gyalen me ɗauke da wani irin ƙamshi. 

“Mujaheed yaushe zaka daina wannan zuciyar taka? Ka rage! Ka jawo mana matsala, yau duk wani talaka ba zai yi barcin daɗi ba a garin nan.”  

“Ta yaya zaku zauna yarinya ƙarama tana taka ku? To idan mai nasara shi ne Gwamna, bai dame ni ba. Zan kuma isa gidan su gobe da ƙarfin ikon Allah.” 

A razane Jabir yake dubansa, duba ne yake masa irin na wanda yasha giyan wake. Yana son yin magana, yaga duk anzagaye motarsu, da wasu irin motoci baƙaƙe wulik!  

Tuni Jabir ya tsure dan yasan hakan zai faru, Jawaheer ba ita kaɗai take ficewa ba, dole akwai masu tsaronta ƙarfafa. A fusace Mujaheed ya kama murfin motar zai buɗe.  Jabir ya riƙe shi yana roƙonsa kada ya fito. Murmushi ya sakar masa, “Me yasa zan zama malalacin namiji? Ban taɓa jin tsoron wani halitta ba, shiyasa aka damƙa min aiki me wahala akan Mai nasara. Wa’innan ma zan iya da su.”

Kawai ya fice. 

Jawaheer 2 >>

2 thoughts on “Jawaheer 1”

  1. Masha Allah,labarin mai cike da basira da sarkakiya,labari mai cike da zalakar harshe da hikima,Allah ya karawa Alkalaminki kaifi teema zaria

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×