Mujaheed ya sake kallon mahaifiyarsa a karo na barkatai. Wannan karon kunyarta ce ta kama shi. Neman hanyar waskewa kawai yake yi. Cike da ƙwarin guiwa ya ce, "Yauwa gara da kika zo Umma. Wai yarinyar nan akan faɗan da kuka yi mata shine wai sai na bata takardarta. Ni kuma inhar zata iya rabuwa da ni saboda haka sai ta gaya min cikin waye. Idan har ta tabbatar ni ne uban, to babu inda zata je."
Duk da Umma tsintar maganar tayi sama-sama, maganar ɗanta bai isheta sauraro ba, bare har ya shigeta. Don haka kawai ta. . .