Skip to content
Part 11 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Mujaheed ya sake kallon mahaifiyarsa a karo na barkatai. Wannan karon kunyarta ce ta kama shi. Neman hanyar waskewa kawai yake yi. Cike da ƙwarin guiwa ya ce, “Yauwa gara da kika zo Umma. Wai yarinyar nan akan faɗan da kuka yi mata shine wai sai na bata takardarta. Ni kuma inhar zata iya rabuwa da ni saboda haka sai ta gaya min cikin waye. Idan har ta tabbatar ni ne uban, to babu inda zata je.”

Duk da Umma tsintar maganar tayi sama-sama, maganar ɗanta bai isheta sauraro ba, bare har ya shigeta. Don haka kawai ta dubi ɗanta ta girgiza kai.

“Allah ya baka lafiya Mujaheed, domin kana buƙatar addu’a.”

Juyawa tayi ta fice daga gidan, kada ta cigaba da ganin abin haushi.

Tana ficewa suka saki ajiyar zuciya a tare.

“Zaki gaya min wanda ya yi maki ciki ko kuwa?”

“Don Allah ka rufa min asiri ka barni. Zuciyata zata iya bugawa. Idan ta buga zan iya mutuwa.”

Ji ya yi gabansa ya faɗi, sai dai kuma lamarin ciki abu ne mai matuƙar ɗaga hankali. Duk yadda zai ɗauki lamarin abin ya fi hakan.

“Jawaheer zan je insiyo maganin zubar da ciki inbaki. Idan cikin ya zube kin ga zan huta da ke, iyayena za su bani izinin rabuwa da ke. Dama wannan ne babban burina. Ni ki barni da iyayena nasan yadda zan shirya da su.”

Juyawa ya yi da nufin ficewa ta riƙe ƙafar wandonsa jikinta yana rawa, “Ka taimakeni kada ka rabu da ni. Idan ka barni babu shakka zan iya mutuwa. Ka taimaki zuciyar Naylaa don girman Allah. Ban san meyasa nake jin idan na rabu da kai zan iya zama gawa, a kowani irin lokaci ba.”

Yadda jikinta ke ɓari, abin yaso ya firgita shi. Da gaske take yi zata iya mutuwa.

Hannunsa yasa ya cire nata daga jikinta, a karo na farko ta hango tausayinta a cikin ƙwayar idanunsa. Sai dai baya son tausayin ya rinjaye shi. Juyawa kawai ya yi, har ya kusan fita ya juyo ya ce, “Na dai gaya maki, ba zaki haifa min ɗan shege a gidana ba.”

Rufe idanunta tayi, tana jin ina ma zata mutu? Da ƙarfi ta rintse idonta cikin kuka take cewa, “Allah ka ɗauki raina inhuta! Allah don girmanka ka kasheni inhuta. Allah don darajar Annabinka ka kashe ni inhuta!”

Yana daga falo yana jin irin addu’ar da take yi. Ya yi yunƙurin shiga a ƙalla ya kai tashi uku, yana fasawa. Kalaman Naylaa suka sake dawo masa kwanya, kamar yadda a tun lokacin da aka ce Jawaheer tana da ciki, kalaman suke cigaba da yi masa kuuwa a kunne, kamar a yanzu take maganar.

“Nidai sai anjima tunda abun haka ne. Allah ya raya abinda ke cikin Jawaheer. Ku maza idan mace ta haihu sai ku rage sonta. Kada ka wulaƙanta Jawaheer kaji? Kada wata mummunar ƙaddara ta sameta ka ce zaka gujeta. Ina sonka Aboki.”

A fili ya maimaita, “Naylaa wannan ne ƙaddarar? Idan ya tabbata abinda na gani a mafarkina gaske ne, na kwanta da Jawaheeer, har nayi mata ciki meyasa har cikin ya bayyana kansa? Dama ana gane ciki akwana biyu ne? Kai inaaa ba mai yuwuwa ba ne. Haka ban sha wani abin maye ba, bare ace bana cikin hayyacina ne.”

Mujaheed ya riƙe kansa da ƙarfi yana Salati. Ya rasa meke masa daɗi. Anan doguwar kujerar ya kwanta shuru yana duban sama. Ji yake kamar maganin matsalarsa tana shimfiɗe a saman ne, don haka yake karanto su.

A haka suka kwana babu wanda ya yi gigin neman wani abu, da nufin ya zuba wa cikinsa. Gari na wayewa wanka kawai ya yi ya sa kayansa ya fice Office.

Yana isowa ya bada umarnin mutanen da za su wuce su kamo sauran mutanen da Alhaji Musa ya ambato sunayen su. Yana isowa gun Alhaji Musa, ya kalle shi da kumburarran fuskarsa ya ce, “Don Allah ka taimake ni ka barni, don Allah kada ka sa a kashe ni.”

Mujaheed ya damƙe shi, kawai ya hau duka. Daga bisani ya dube shi ido jajir.

“Banda cutar da ni da kayi? Kake son inyi maka afuwa? Kai ne dalilin aurena da Jawaheer, yarinyar da na tsana fiye da komai! A lokacin da Naylaa take roƙonka kada ka kashe ta, ka taimaki mijinta ka bar masa ita, ka dubeta? Ka ji ɗigon tausayinta a zuciyarka? Kayi kuskure Musa! Ka riga ka cutar da rayuwata! Ko ka bar duniya ban rama kwatankwacin abinda kayi min ba, har sai na ƙarar da danginka gaba ɗaya! Ubangidanka ba mai kuɗi bane? Maza ka kira shi yazo ya yi amfani da kuɗinsa ya hanani miƙawa kotu kai, ta kashe min azzalumi! Yanzu ne lokacin da miliyoyin kuɗin da ka ci na kashe Naylaa zasu yi maka amfani. Ina tabbatar maka duk wanda ya yi gigin sa hannunsa a case ɗinnan, sai na kashe shi da wannan bindigar tawa.”

Mujaheed ya ƙarashe tare da fiddo bindigar yana mai saita ta, a dai-dai ƙirjin Alhaji Musa. Hakan ba ƙaramin sake tayar masa da hankali ya yi ba. A take firgici ya shige shi, wanda ya yi sanadiyyar sumewarsa. Mujaheed ya dube shi yana ƙara jin tsanarsa.

“Ni zuciyata ka kashe! Ni rayuwata ka ɗauke, ka bar ni da gangar jikina.”

Mujaheed ya duƙar da kansa kamar mai tunani, sai kuma ya fice kawai ya bar yaransa a ciki.

A Office ya zauna shuru, “Jawaheer waye ya yi maki ciki? Don Allah ki gaya min.”

“Wacece kuma ke da ciki?”

Jabir da shigowarsa kenan, ya ja kujera ya zauna yana ƙarewa Mujaheed kallo. Ya koma kamar lokacin da Naylaa ta rasu. “Ko sai yaushe Mujaheed zai fita daga irin wannan damuwar oho?”

Jabir ya cigaba da kallonsa yana neman ƙarin bayani. Duk da fushi yake da Jabir, amma kuma ya ji daɗin zuwansa, ya tabbata zai ɗan sami natsuwa. A hankali ya fitar da maganar, kamar sabon mai koyan harshen Hausa.

“Jabiru, Jawaheer ɗin da kake ta yabo, yau dai tana ɗauke da ciki, cikin da babu wanda yasan wanda ya yi mata. Sai ita kaɗai ita kuma taƙi faɗa. Yanzu haka ina cikin matsala da su Abba.”

A natse ya warware masa yadda suka yi da su Abba. Shi kansa Jabir ya yi matuƙar firgita. Dubansa ya sake yi, kasancewar shi ƙwararren likita ne, ya ce “Mujaheed! Da farko ya zama dole ka zama mai haƙuri da jajircewa. Ya zama dole ka zama cikakken musulmi. In da musulunci ya ƙara bambanta da kafirci kenan wato kayi imanin sai Allah ya jarabceka. Ka kuma kasance mai yarda da ƙaddara mai kyau ko akasin hakan. Kada kayiwa Allah butulci mana Mujaheed. Ya baka lafiya, ya barka da iyayenka, ya baka sutura ya rufa maka asiri. Don kawai ya jarabceka ya ɗauke matarka sai duk ka mance wa’innan ni’imomin da ya yi maka? Kalli yadda ka koma kamar ba Mujaheed ɗin da na sani ba. Dubi kayan da kasa ka fito gun aiki da su! Mutumin da kowa ya sanka baka maimaita kaya? Idan kasa yau sai ka share shekara kafin ka sake waiwayar kayan, amma dubi kayan nan babu ko tambaya jiya su ka sanya, idan aka duba yadda suka cukurkuɗe. Anya Mujaheed kai ne kuwa? Ina ilimin islaman da iyayen mu suka bamu? Ko ƙamshi baka yi, bacin ka sani idan zaka shiga wuri turarenka ke fara yin sallama, kafin isowarka. Meyasa haka Mujaheed? Naylaa tafi buƙatar addu’arka fiye da wannan shirmen. Idan damuwarka ka kama Alhaji Musa ai ka kama shi ko? Gaskiya ba zan ɓoye maka ba, kana barin mu, mu ‘yan uwanka a cikin damuwa. Haka yaran aikinka yanzu suke ta yi min ƙorafi akanka. Dukkan su basa cikin walwala. Oganka da kansa ya ɗaga waya ya kirani yana gaya min irin matsalolin da  suke fuskanta adalilin rashin baiwa aikinka mahimmanci. Kai ne idan aka baka aikin bincike kake gaggawan kawo masu abinda suke nema.”

Jabir ya yi ƙasa da murya kamar wanda baya son wani ya ji abinda yake son faɗi,

“Mujaheed, ya zama dole ka zama cikakken musulmi, ba wai muna musulmi ba. Ka dubi abokina Aminu, wulaƙanta jama’a kawai yake yi yana nuna shi wani ne. Mutane suna kuka da shi, ma’aikatansa suna wayyo-wayyo da shi. Ya tsani talaka! Abokanmu na Makaranta yaƙi ya dube su, a ganinsa talaka ne. Kasan me ya same shi yanzu?”

Mujaheed da jikinsa ya gama yin sanyi ya girgiza kai, ba tare da ya iya furta komai ba.

“Aminu dai ya ruguzo. Ya koma talaka likis! Ya zama abin tausayi. Shi arziƙi riga ne na aro, a kowani irin lokaci Allah yana iya karɓewa, tunda ba da shi ka zo ba. Haka ita rayuwar take. Ka godewa Allah sai ya ƙara maka. Yau da yaran aikinka basu jin daɗin aiki da kai, yadda ka sami matsalar nan Allah shi ƙara kawai za su yi ta maka. Matsalar nan ba akanka aka fara ba. Iyayen mu suna kasa barci a samakon yadda suke ganinka.”

Kalaman Jabir sunyi matuƙar tasiri a zuciyarsa. Ya kuma ji tsoron abinda ya sami mutum kamar Aminu. A kalaman Jabir babu na zubarwa. Ya shafi kansa.

“Yanzu Jabir maganar cikin fa? Ya fi damuna.”

“Ka fara gyara mu’amalarka da iyayenka, yaran aikinka, uwa uba Oganka. Don Allah Mujaheed kayi aikin da idan ka bar wuri za ayi ta yabonka ba wai a zagaya ana zaginka ba. Zagin wanda ka cutar zai iso gareka wataran.”

Shuru ya yi, kamar yana son yin jayayya da maganar Jabir, domin gani yake matsalar matarsa ta fi komai tashin hankali, yana ganin kamar yana da sauran lokaci da ya kamata ya gyara abubuwan da Jabir ya gaya masa daga ƙarshe. Dole zai gwada amsar shawarar ɗan uwansa domin ta hakane ƙila ɗayan matsalar ta zama tarihi.

“Shikenan Jabir. Ta ina zan fara?”

“Ka fara da tsaftace kanka, ka shiga kasuwa kayi wa iyayenka siyayya. Domin duk kuɗin iyayenka suna buƙatar naka, hakan zai sa su gane ɗan su bai mance da su ba. Kuma za su sa maka albarka, wannan albarkar ita zata yi ta tafiya da kai, har ka sami warwarewar dukka matsalolinka. Wasu mutane suna ganin kamar wayo ne, ka samu ta hanyar halas ka hana iyayenka. Mutum mai wayo da dabara shi yake aikata abin alkhairi agun iyayensa domin samun babban rabo. Ka saki fuska, duk wasan da ka saba yi masu idan kaje ka kwatanta hakan. Zaka zo ka bani labari. Matsalar Jawaheer zamu zo mu zauna. Amma don Allah ka rage wannan tsanar da kake yi mata. Babu kyau tsanar ɗan adam irin haka, idan ka tsaneta ka raina ta, Allah zai iya jarabtanka akanta kuma kasha wahala. Mutum ɗan adam daraja gare shi, domin Allah da kansa ya karrama ɗan adam.”

Anan ma shafa kansa ya yi, yana jin ba laifinsa bane, laifin zuciyarsa ce da ta hana shi amsar ƙaddararsa. Shuru ya yi ba tare da ya bashi amsa ba. A dai-dai lokacin ya miƙe suka fito a tare.

Har Office ɗin ogansa suka shiga ya ɗan saki jiki, wanda hakan ya yi masa daɗi, har ma ya ƙara da yi masa ‘yar nasiha. Sai dai da ogan yasan menene a cikin zuciyar Mujaheed da ya daina murna da ɗan sakin fuskar da ya samu daga Mujaheed.

Sai Magriba ya dawo gida, ya yi wanka tare da alwala ya wuce masallaci. Har akayi Isha’i bai fito daga Masallacin ba, sai da ya gabatar da Isha’i sannan ya fice ba tare da ya waiwayi gidan su ba.

Ya jima zaune a falon bai ji motsin Jawaheer ba, ya sha ruwan tea yana jin natsuwa a tare da shi, fiye da jiya, da yake zaton ajalinsa ne ya zo. Ya jima yana kallon ɗakin Jawaheer, tambayar da yake yawan yi wa kansa wa ya yi mata ciki? Ya kasa barin ƙoƙon ransa. Meyasa Naylaa ta zo a Mafarki ta gaya masa abinda ga shi nan a zahiri sun faru, koma ya ce suna kan faruwa.

A dogon kujera barci ya kwashe shi, sai ƙarfe biyu na dare ya farka. Addu’ar tashi barci ya gabatar kafin ya tsoma ƙafafunsa ƙasa kamar mai tsoron taɓa ƙasan. Muryarta ya ji cikin kuka tana rera karatun Alqur’ani, da muryarta mai daɗin saurare. Haƙiƙa babu abinda ya kai sauraren karatun Alkur’ani daɗi.

Tashi ya yi ya shiga banɗaki ya kama ruwa tare da ɗauro alwala.

Yana da buƙatar keɓewa da Mahaliccinsa domin shi kaɗai ne zai iya warware masa dukkan matsalolinsa. Ya jima yana kai kukansa agun Allah, sannan ya buɗe Al-qur’ani ya ya fara rerawa, cikin gwanance da kira’a mai saukar da natsuwa a zuciyar mai saurare. Sai da aka kira Sallah sannan ya rufe, ya sake alwala ya fice zuwa Masallaci yana tafe yana Istigfari.

Yana nan zaune yana ambaton Manzo, cikin Salatinsa, har gari ya yi haske. Kai tsaye banɗaki ya nufa ya yi wanka tare da gyara jikinsa ko ta ina. Ya dubi kansa a madubi yana jin sanyi a ransa. Tsafta tana da daɗi, haka ya aminci tsafta tana daga cikin yankin imani.

Yana fitowa ya fiddo da sabon kayansa daga cikin sabbin da bai taɓa sawa ba. Suit ce mai tsananin sheƙi, ko nawa aka ce maka kuɗinsa babu yadda za ayi ka iya ƙaryatawa.

Ƙamshinsa ya ɗauka ya ƙurawa idanu yana tuna wasu abubuwa da yawa. Daga baya ya fesa kawai ya fice. Kai tsaye ya nufi Office. Tun daga bakin gate ya fara ganin kallon mamaki daga gun ma’aikatansu. Haka ya gaggaisa da mutane yana ƙaƙalo fara’a yana masu. Yaransa kuma suka ɗinga sara masa, tare da rufa masa baya. Kai tsaye office ɗin ogansa ya nufa ya sara masa sannan ya ɗan zauna yana duba file ɗin da ogan ya tura masa. Bayanai ne akan mutanen Alhaji Musa, da kuma irin manyan mutanen da suka nemi shiga cikin maganar, haka kuma ya tabbatar masa ya tura su kotu, ranar Monday za a shiga idan Allah ya basu aron rai. Bayanai dai kala-kala wanda ya kula Mujaheed ya ji daɗin su ƙwarai. Haka ogansa ya burge shi, da kuɗi basu rufe masa ido ba. Godiya ya yi masu ya miƙe dauke da files ɗin yana buƙatar sake nazarin su.

Sai da yaje ya ga mutanen, haka ya ga likitan da ya ƙwaƙwale masa zuciyar Naylaa yasa aka kai shi wuri na musamman, ya ɗinga azabtar da shi. Sai da ya ga baya motsi sannan ya ƙyale shi. Tuni ɗan farin cikin da ya fito da shi ya neme shi ya rasa. Komawa office ɗinsa ya yi, ya kifa kansa yana huci.

“Meyasa Naylaa? Meyasa baki tsaya na nuna maki irin ƙaunar da nake maki ba? Meyasa?”

A take nasihar Jabir ta karyo masa don haka ya ɗinga faɗin Astagfirullah!

Da Misalin ƙarfe huɗu,  bayan ya fito daga Masallaci ya koma gida. Ya Sake watsa ruwa, ya shirya tsaf cikin dakakkiyar shaddarsa fari ƙal, ya ɗora baƙin hula baƙin agogo, baƙin takalmi. Sai ƙamshi yake tashi.

Kai tsaye ya fito har ya kai bakin ƙofa wani tunani ya zo masa. Komawa da baya ya yi, sannan ya shiga ɗakinta. Tana nan kwance akan dadduma, gefenta kuma ruwan shayi ne da tasha kusan rabi ta bar sauran.

“Ke!” A ɗan firgice ta tashi tana dubansa. Ya yi mata kyau fiye da kowani lokaci. Wani irin sonsa ya sake kanainaye zuciyarta. Sunkuyar da kanta tayi, tana jin kamar ta je ta shige jikinsa.

“Lafiya kika tsare ni da ido? Ki tashi ki je kiyi wanka ki gyara fuskar nan, kiyi shigar mutunci ina son zamu shiga kasuwa daga nan mu wuce gidan Abba. Ina fatan zaki aro fara’a ki mannawa fuskarki, kamar yadda akasan yadda akayi aka aro zuciya aka manna maki?”

Sunkuyar da kanta kawai tayi tana duban yatsunta.

“Ki tashi na baki minti ashirin ki gama dukka abubuwan da na ambata. Kada kiyi amfani da turare. Ina jiranki a falo.”

Ya ambaci kada tayi amfani da turaren ne don yasan idan ta tashi sanya turaren irin na Naylaa zata saka.

Ita kuwa kukan farin ciki zata yi ko kuwa godiya ga Allah? “Alhamdulillahi, Alhamdulillah.”

Jiki na kyarma ta faɗa banɗaki ta watsa ruwa. A gurguje ta shirya, kawai fauda ta shafa da man baki. Sai gata ta fito fes! Bakin nan sai walƙiya yake yi. Doguwar rigar shadda tasa, mai kalar milk, wanda ya kusa sajewa da fararen kayansa. Baƙin gyale ta tafa, ta sa baƙin takalmi ta ɗora baƙar jaka.

Dubanta ya yi, bayan ta fito kamar zai yi mata magana ta je ta sauya kanyata sai kuma ya ƙyaleta. Kai tsaye kasuwa suka shiga suka yi siyayya a wani ƙaton super market. Ma’aikatan suka kwashi kayan suka kai masu mota.

Shi dama fuskarsa a ɗaure yake don haka suna fitowa ta dube shi, “Aboki ka siya min Ice Cream.”

Juyowa ya yi ya kafeta da ido. Tunda ake faɗin kyanta bai taɓa yarda ya gani ba,sai yau. Ya ɗan Kauda kansa ya ce, “Idan kuma ban gadama ba fa?”

“Kayi haƙuri Aboki kaji? Ai ka ce min komai nake so zaka yi min ko?”

Wuce wa ya yi da sauri yana jin ƙirjinsa yana harba masa da sauri da sauri. Yana shiga motar ya rintse ido. “Anya zan iya kuwa?” Ya furta da ƙarfi kamar mai magana da wani.”

A sanyaye ta ƙaraso. Tana son ta ɗinga kauda kanta akansa, ta daina yi masa shisshigi amma ta kasa juran hakan.

Tana rufe ƙofar ya fizgi motar da ƙarfi, hakan yasa ta riƙe hannunsa a ɗan sorace. Tana ɗagowa suka haɗa ido suna duban juna. Ya Kauda kansa yana cigaba da tuƙin, sai dai ya rage gudun. Haka itama ta cire hannunta a jikinsa.

Suna isowa gidan, suka fito a tare sannan ya kira mai gadi ya ce ya kwaso kayan. Hannunta ya ɗan riƙe haka suka ɗan saki fuska.

Abbansa da dawowarsa kenan yana zaune a falon daga shi har Umman basu da walwala. A zahiri tausayin ɗansu da ke ƙoƙarin zama mahaukaci da ƙarfi da ya ji yake damun su.

“Assalamu alaikum.” Suka yi sallama a tare suka kutsa kai. Sai kallo ya koma gun su, duk da dukkansu sun rame sosai, hakan bai hana Abba da Umma jin wani sanyi a cikin ransu ba. Abba ya miƙe ya ƙaraso gaban Mujaheed mamaki kwance a fuskarsa.

“Mujaheed kai ne yau haka? Kai Masha Allah. Ku ƙaraso ku zauna.”

Mujaheed ya saki jiki sosai, ya ci abinci, ya kuma ɗinga taƙalar iyayensa da hira. Duk da babu wani sakewan da suka yi, da Jawaheer hakan bai sa ya damu ba. Ita kanta Jawaheer ta sami natsuwar cin abinci sosai.

Umma sun ji daɗin abinda Mujaheed ya siyo ya kawo masu, don haka ne ya sha albarka. Haƙiƙa Mujaheed ya farantawa iyayensa rai. Ce masu ya yi yana zuwa, ya sa kai ya fice. Sweet ɗin da ya siyo ya fito waje ya ɗinga kiran Almajirai yana basu tare da kuɗi. Kafin ka ce me? Yaga suna ta ɓulɓulowa. A take Naylaa ta faɗo masa.

“Idan baku bi a hankali ba zan fasa baku in yi shigewa ta.”

A hankali ya yi magana, “Ku yi wa Naylaa addu’a kun ji?”

Ɗaya daga cikin su ya ce, “Kullum sai mun yi mata addu’a, malamin mu yana tara mu duk bayan mun gama karatu ya ce muyi mata addu’a.”

Shuru ya yi yana duban su. Yana gamawa kawai ya koma gida yana girgiza kai.

“Umma zan ɗan kwanta na gaji kwana biyu da case ɗin su Alhaji Musa ranar Monday za a wuce da du kotu.”

Gaba ɗaya suka jinjina kai suna yi masa kyakkyawar fata.

Bai damu da rashin ganin Jawaheer ba, ya shiga ɗakinsa ya kwanta shuru. Yana ambaton Hasbunallahu wani’imal wakil. Ya kasa barcin, sai juyi kawai yake yi. Dole ya miƙe da littafi a hannunsa ya wuce cikin lambun don samun natsuwa.

<< Jawaheer 10Jawaheer 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×