A gajiye likis ya dawo aikin, kasamakon tattara Jawaheer da ya yi, ya watsar da ita. A falo ya sameta, ta dube shi kawai ta yamutsa fuska ta kauda kai. Wannan abu ya yi masa ciwo, sai dai kuma baya jin ta ishe shi kallo.
Ya zauna tare da sauya tasha yana kallon labarai. Miƙewa tayi tsam, ta kama hanyar shiga ɗaki. Ƙugunta ya bi da kallo yana al'ajabin rashin kunyar da yarinyar take son ta fara yi masa. Cigaba ya yi da kallonsa yana nazarinta.
*****
Cikin hukuncin Allah andamƙa Alhaji Musa a kotu, da shi da. . .