Skip to content
Part 13 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

A gajiye likis ya dawo aikin, kasamakon tattara Jawaheer da ya yi, ya watsar da ita. A falo ya sameta, ta dube shi kawai ta yamutsa fuska ta kauda kai. Wannan abu ya yi masa ciwo, sai dai kuma baya jin ta ishe shi kallo.

Ya zauna tare da sauya tasha yana kallon labarai. Miƙewa tayi tsam, ta kama hanyar shiga ɗaki. Ƙugunta ya bi da kallo yana al’ajabin rashin kunyar da yarinyar take son ta fara yi masa. Cigaba ya yi da kallonsa yana nazarinta.

*****

Cikin hukuncin Allah andamƙa Alhaji Musa a kotu, da shi da likitocin da suka taimaka masa. A shiga ta farko, aka ɗaga. Ganin alamun samun nasara yasa Mujaheed samun sauƙin raɗaɗin da ke cinsa.

Yau yana saurin zai shiga gida, ita kuma ta fito cikin adonta. Ita kanta tasan tayi kyau. Cin karo suka yi hakan yasa ta kusa kaiwa ƙasa. Da sauri ya kamota, ta riƙe shi sosai don ta tsorata. Kallon juna suka tsaya yi, ido cikin ido. Ya  Kauda kansa ba tare da ya sake dubanta ba.

“Ki ɗinga tafiya a cikin hayyacinki.”

Lumshe idanunta tayi, ta luma su a cikin nasa. Mamakin irin ramar da tayi ya fi tsaya masa a rai. Bata ce masa komai ba, ta raɓa gefensa.

A cikin tsakiyar daren, Mujaheed ya kasa rintsawa, wani abu mai kama da almara ya cigaba da damunsa yana azalzalarsa. Da ƙarfin tsiya yake son ƙaryata abinda zuciyarsa ke gaya masa.

Sannu a hankali hoton haɗuwar jikinsa da Jawaheer yana dawo masa cikin ƙwaƙwalwa fes! Kamar yanzu abin ke faruwa. Sai dai kwartonta yana taka rawa wajen ruguza dukkan wani ginin da ya yi nisa a cikinsa.

Sannu a hankali zazzaɓi mai zafi ya shige shi, hakan yasa ya kasa tashi.

Misalin ƙarfe takwas na safiya tana zaune, bayan ta kammala cuccusa dankalin da ta soya, ta kora da ruwan zafi. Ita dole sai ta mance Mujaheed ta koyi sabuwar rayuwa. Hawaye ta ji a idanunta a lokacin da ta tuna akwai yaro kwance a cikinta. Shafar cikin tayi, tana jin ko yaron bai da uba, ita zata zame masa uwa da uba.

Sallamar Umma da likita yasa ta ɗago tana dubansu. Sunkuyawa tayi tana gaida Umma. Ita kuwa Umma kallon kayan karyawan take yi tana mamakin yadda Mujaheed yake kwance yana jin jiki amma ita ko a jikinta. Dakta ya dubeta ya ce, “Hajiya a ina yake kwance?”

Gaban Jawaheer ya faɗi, ta hau kame-kame. Umma ta ce, “Zo muje kaji Dokto.”

Jawaheer ta biyo su a baya kamar ɓarauniya. Ganin irin halin da Mujaheed yake ciki, duk ya ɓata jikinsa da amai yasa Jawaheer shiga ruɗu. A take dabara ta faɗo mata, cikin kuka take magana,

“Ka ga sai da nace maka ba zan fita ba, amma ka nace sai na fita ka ga irinta ko?”

Umma ta dubeta cike da zargi, sai dai bata ce mata komai ba, suka shiga bashi taimakon gaggawa.

Bayan anyi masa allurai, Umma tayi masu sallama akan zata sake dawowa. Ɗakin ya rage daga ita sai shi. Zuba masa idanunta tayi, tana sake jin kamar ana ƙara mata sonsa. Hannu ta kai bisa goshinsa, zuwa wuyansa, har ƙirjinsa.

Yana jinta, haka da zata kula da kyau da ta ji yadda numfashinsa ya sauya bugu.

Dai-dai fuskarsa ta sunkuya tana magana a hankali cikin kuka. “Allah ya baka lafiya aboki.”

A zuciyarsa ya amsa da “Ameen.”

Yunƙurawa ya yi, alamun zai tashi, tayi maza ta kama shi tana yi masa sannu. A gurguje ta faɗa kichin ta haɗo masa tea, ta dawo kan gadon sosai ta zauna ta yadda jikinta yake haɗuwa da nasa jikin.

Ta ɗibowa  a cokali ta sa masa a baki. Sau uku ya karɓa ya kawar da kansa. Girgiza kanta tayi, “Kayi haƙuri nasan baka sona, amma yanzu lalura ce kayi haƙuri intaimaka maka.”

Dole ya ɗinga karɓa, sai dai fuskar nan babu rahama. Da daddare yana kwance yana tunanin zuci, ya ji shigowarta. Tana sanye da rigar barci mai kauri, ta haɗe gashinta wuri guda. Idanu ya sa mata yana son ganin ikon Allah. A ƙasa ta sa filo ta kwanta.

Gaba ɗayan su sun kasa barci sai juye-juye suke yi. Da ƙarfin addu’a Jawaheer ta sami barci. Saukowa ya yi, ya  ƙaraso gabanta, tare da zuba mata idanu. Ya kai hannu bisa fuskarta ya ɗauke gashin da ke barazanar rufe mata idanu.

Ɗaukarta ya yi, ya shimfiɗe akan gadonsa, tare da jawo mata bargo. Idan yana tunawa da cikin da ke jikinta sai ya ji kamar ya shaƙeta, kowa ya huta. Kamar ance masa ya fita, yana fitowa ya ji motsi, cikin sauri ya biyo bayan motsin. Mutumin ya sake gani ya fice daga gidan da gudu.

Mamaki yasa ya zubawa ƙofarta idani, a zahiri dai yasan tana cikin ɗakinsa a kwance, me kuma yasa yanzu ya ji motsin mutumin? Ɗakin ya shiga, ya tsaya turus yana kallon ikon Allah. Bra ɗinta ne a yashe a ƙasa, irin dai alamun da ya saba gani idan mutumin ya shigo.

Ya yi nisa a cikin tunani, ya zama dole ya kama ko waye, yana son sanin meke shirin faruwa a cikin gidansa, haka waye yake son kawo masa ruɗani?

Jawaheer tayi juyi, kawai ta hango shi zaune ya kifa kansa, hakan yasa ta tashi a ruɗe. Tasa hannu ta ɗago shi tare da tallabo fuskarsa.

“Jikin ne?” Ta tambaye shi jikinta yana rawa. Bai bata amsa ba, haka idanunsa suna kafe a fuskarta. Ya rasa wani irin yanayi ne haka yake shiga a ‘yan tsakanin nan? Sai tambayar kansa yake yi, abubuwan da shi kansa yasan ba shi da amsarsu.

Hannayenta ya kama ya cire su daga fuskarsa, “Kije ki kwanta, bana cikin wata matsala.” Yadda ya yi mata abin ya ɗan bata tsoro, hakan yasa ta koma shuru ta kwanta.

Sun jima babu wanda ya iya rintsawa, kowa da irin saƙe-saƙen da ke zuciyarsa. Da Asuba bayan ya yi Sallah ya tashe ta, ta shiga banɗaki, tana tashi ya kafe zanin gadonsa da idanu, da jini ya ɓata zanin. Ware idanunsa ya sake yi yana mamakin me kuma ya haɗa mai ciki da al’ada? Tana fitowa itama ta zubawa inda yake kallo idanu. Dukkansu suka yi, shuru sakamakon zuciyoyin su tambayoyi ne cike, babu kuma mai iya basu amsa.

Tashi ya yi ya fice falo, hakan yasa tayi sauri ta gyara wurin, ta koma ɗakinta tana tunanin zuci.

Sai da gari ya yi haske sannan ya kira Doctor ya ce ya sake duba masa Jawaheer, bayan ya koro masa bayani. Doctor ɗin ya bashi amsa da masu ciki sukan yi jini duk wata, wannan ba sabon al’amari bane. Mujaheed ya fice yana ƙara bashi umarnin ya duba masa Jawaheer kada yazo cikin ne ke son ficewa.

Yana nan zaune a bakin Gate ɗin, Doctor ya ƙaraso yake gaya masa, cikinta yana nan lafiya lau, kawai kamar yadda ya gaya masa ne a farko. Suka yi sallama ya fice. Yana nan zaune ya ƙurawa ƙasa idanu, gaba ɗaya yana jin kamar ya bar garin ko zai sami sassauci.

Mai gadin ya ƙaraso gurinsa ya miƙa masa wata takarda ya ce wani ya kawo ya ce a bashi. Babu dogon tunani ya buɗe takardar tare da ware idanunsa akan rubutun.

“Nasan zaka yi mamakin wannan rubutun nawa. Kayi haƙuri da shigar maka gida da nake yi, har nayi wa matarka ciki, hakan ya faru ne a sanadiyyar gayyatoni da tayi a karo na farko, take gaya min mijinta bai damu da ita ba. Daga gani bata saba da iskancin ba, don haka nazo a karo na farko ta amince da ni, haka a karo na biyu ban sha wahala ba. A karo na uku ne bayan ta gama lasa min zuma a baki take ƙoƙarin guje min, ni kuma a ganina ba abu bane mai yuwuwa. Shiyasa na cigaba da zuwar mata idan tana barci, wataran ma har maganin barci ina zuba mata. Kayi haƙuri ba zan iya rabuwa da ita ba, abu mafi sauƙi shi ne ka sake ta in aureta ko don mu kula da tarbiyyar yaron mu da ke ɗauke a cikinta. Matarka tana da daɗi.”

Mujaheed ya miƙe hannunsa na rawa, ya rasa wani mataki ya kamata ya ɗauka. Ɗakin ya koma yana ƙwala mata wani irin kira, wanda yasa ta fito agigice. Gashin kanta ya kama da ƙarfi yana huci.

“Karanta takardar nan.” Ya damƙa mata a hannu, wanda azaban riƙon da ya yi, mata yasa ta kasa duba takardar sai ma rintse idanunta da tayi da ƙarfi,

“Don Allah ka sakar min gashi, sai inkaranta zafi nake ji.”

Hawaye suka gangaro mata, dole ya sassauta riƙon da ya yi mata, saboda yafi buƙatar ta karanta ɗin ya ji ko tana da abin kare kanta? Ya fi buƙatar ta samo abinda zata kare kanta ɗin, ko don zuciyarsa ta huta da raɗaɗin da take ciki.

A hankali ta tsoma idanunta a bisa takardar tana karantawa, idanunta suna ƙara girma. Wani duhu ya gilma mata tun kafin ta kammala, ta zube ƙasa a sume.

Duk da sumewar da tayi hakan bai sa zuciyarsa ta huce ba, hakan bai sa ya dawo hayyacinsa ba, hakan baisa ya ji cewar zai iya tausaya mata ba. Amsarta kawai yake nema a yanzu ba sai anjima ba. A gaggauce ya nufi frij ya ɗauko ruwa, ya kwara mata. Tana sakin ajiyar zuciya haɗi da sakin wani irin marayar kuka, yasa hannu ya fizgota jikinsa yana tsuma.

“Yanzu ba lokacin kuka bane, lokaci ne na warware min abinda ke ɓoye. Ki gaya min wane ne wannan mutumin? Ban damu da abinda kika aikata ba, damuwata insan waye ya iya tsallakowa har cikin gidana ya aikata ɓarna? Ki gaya min! Idan kuma kika ci min musu, sai nayi mugun yi maki illa Wallahi! Idan anyi maki magana kin iya kuka, da faɗin Allah a baki. Ashe wani ƙato kike shigo min da shi cikin gidana. Akan me? Ina ƙyaleki ne darajar Naylaa, da ba haka ba, bana jin zaki ƙara yin minti biyar a cikin gidana.”

Jawaheer ta dakata da kukanta cak! Tana dubansa, duba irin na tsoro da mamaki. Haka ta hangi tsanarta kwance a ƙwayar idanunsa.

“Ka kasheni Mujaheed! Don Allah ka kashe ni kada ka barni da rai! Na gaji, da wahalar da zuciyata da kake yi. Kullum ina tsoron gari ya waye saboda masifarka da tsangwamar da kake yi min. Ina da gidan iyayena wa’inda suke matuƙar sona, ba wai a bola ka tsinto ni ba, bare kullum ka ɗinga yi min gorin gida. Kai ka sani, idan banda darajar zuciyar da ke jikina, bana jin ka isheni kallo bare har in aureka. Saboda duk abinda kake ji da shi nima ina ji da irinsa. Kuma duk wanda ya yi min ƙazafin zina ba zan taɓa yafe masa ba. Mutumin da kake magana akansa ban san shi ba! Ban taɓa ganinsa ba!! Kayi duk abinda ka gadama.”

Wani wawan mari ya ɗauketa da shi, wanda ya ɗauke dukkan ganinta da kuma jinta na wasu ‘yan daƙiƙu. Kuka mai ƙara ta sa, tana dafe da wurin, haka bata daina dubansa ba.

“Kin yi kaɗan ki ɗinga gaya min maganganun da suka zo bakinki. Wanda ya fi ki ma ya yi kaɗan bare kuma ke, ƙanwar-ƙanwar bayana. Ki gaggauta gaya min mutumin da ke shigo min gidana tun kafin lokacin danasaninki ya tsaya.”

“Mujaheed ka ji tsoron Allah. Na gaya maka ka daina zafafa ƙiyayya. Jawaheer wuce ɗaki kinji?”

Jabir da shigowarsa kenan ya jefi Mujaheed da wa’innan kalaman kuma ya tura Jawaheer ɗakinta.

Mujaheed ya juya da nufin ficewa Jabir ya cigaba da maganar da tasa ya tsaya yana dubansa.

“Ina jin tsoron ranar da Allah zai jarabceka akan Jawaheer, ranar da zaka yi ta danasani mara amfani. Meyasa zaka ajiye yarinyar nan kana gasa mata duk wata magana da ta zo bakinka? Kamata ya yi, ka mayar da hankali wajen ganin ka kama mai zuwar maka gida ba wai kullum kayi ta cin zarafinta ba.”

Mujaheed ya ɗauki takardar nan ya damƙa shi a hannun Jabir yana dubansa, “Jabir karanta takardar nan sai kuma ka sake samo hanyar kareta.”

Jabir ya karɓa ya karanta, sannan ya ɗago yana dubansa, “Ƙiyayya babu abinda baya sawa, da ace kana son Jawaheer da idanunka ba za su rufe har ɗan wannan bayanin ya dameka ba. Kai kasan ko wasu ne suke son su ga sun raba ku? Kai kasan ko ta taɓa wulakanta wani saurayi ne, yake son ya rama abinda tayi masa? Naje na sake yin bincike akan Jawaheer antabbatar min ko hannunta bata yarda namiji ya taɓa, bare akai ga jikinta. Ya kamata ka dawo hayyacinka, ka gane akwai wanda yake son ya kawo maku ruɗani a cikin zamanku ne. Ka daina saurin yanke hukunci.”

Mujaheed ba zai iya tsayawa yana sauraran rainin wayon Jabir ba, don haka ya fice kawai. Jabir ya ƙarasa ya kira Jawaheer da ke kuka kamar ranta zai fita, ya yi mata ‘yan tambayoyi, ya umarceta da ta share hawayenta, insha Allahu shi zai samar mata ‘yancinta agun Mujaheed.

Sharce hawayen tayi tana duban Jabir,

“Ka taimakeni don Allah, ina son intafi gidanmu ne. Na gama auren Mujaheed ko soyayyarsa zata kashe ni ne. Ko mutum na kashe masa iya izayar da zai yi min kenan.”

Jabir ya girgiza kai, “Kiyi haƙuri Jawaheer, tunda kun riga kun haɗu, ki daure ki ƙarasa ladanki don Allah. Ki saurareni sosai, zan gaya maki abubuwan da zaki yi, insha Allahu sai kin bani labari da kanki. Amma sai kin daina wannan kukan.”

Jikinta na rawa ta goge idanunta, domin a wannan gaɓar mafita kawai take nema. Jabir ya zauna ya yi mata doguwar magana mai ɗauke da abubuwa masu mahimmanci, wanɗanda suka kasance masu sauƙi, kuma masu wahala. Ta ji daɗin shawarar nan a karo na biyu, kuma ta ci burin yin amfani da su in har za su kawo mata mafita.

Mujaheed ya yi nisa a hanyar ya ji hannunsa ya taɓa takarda, don haka ya ɗauka yana kallo tare da kallon titi duk a lokaci guda. Ganin zai raba hankalinsa biyu ne, yasa ya ajiye da nufin sai ya iso office.

Yana ajiye motar ya ware takardar tare da fara karantawa.

“Mujaheed sarkin zuciya. Zuciyarka ita ta jawo Naylaa ta rasa rayuwarta. Haka a wannan karon ma zuciyarka ita ta sake jawo maka matsalar da ta haifarwa matarka samun ciki. Jawaheer tana da kyau, da jikin mata, amma da yake kai makaho ne, baka taɓa lura da hakan ba. Ka gaggauta rabuwa da Jawaheer don samun sassaucin halin da kake ciki. Idan kuma ka ƙi sakinta, hakan yana nuna alamun ka kamu da sonta kenan, wanda hakan zai zama abin kunya, ka auro mace wani ya yi mata ciki, kuma ka cigaba da rainon cikin a cikin gidanka. Zan cigaba da lalubarta, kai kuma ka cigaba da ajiye min ita a cikin gidanka.”

Jujjuya takardar ya ɗinga yi, daga baya yaga anrubuta,

Daga kwarton matarka

Mujaheed ya ware idanunsa, yana son da ƙarfi da ya ji ya hana kansa damuwa da abinda wani ɓangare na zuciyarsa ke kira da shirme. Ya kula so suke su haukata shi. A shirye yake da ya rabu da Jawaheer, don ya gwada wa ƙaramin mahaukacin can, bai taɓa jin ɗigon son Jawaheer a zuciyarsa ba. Kawai ya bar Jawaheer ne saboda kalaman Naylaa, da tayi masa a cikin mafarki ana gobe wannan matsalar zata faru. Idan ba haka ba, Jawaheer ba kowa ba ce agurinsa.

Duk da haka gara ya rabu da ita, ko zai samu kwanciyar hankalin da ya rasa tun ranar da ta shigo rayuwarsa. Zai barwa kwartonta, ya ƙarasa abinda ya fara.

Ko da ya koma gida ya gagara aikata abinda zuciyarsa ke gaya masa. Haka bai sake neman Jawaheer ba. Gaba ɗaya ya sake komawa gidansa na jiya. Wasiƙun da ya karɓa sun yi matuƙar razana shi.

Yau ya ci burin ko wanene mutumin nan sai ya kama shi, don haka ya haramtawa kansa barci. Motsi kaɗan Mujaheed zai ji, sai ya leƙa, kamar mafaraucin da ke jiran isowar ɓera. Sake leƙawan da zai yi, ya ɗauki lemu mai sanyi ya kaiwa maƙoshinsa. Cikin minti goma da shan lemun ya fara hamma babu kakƙautawa. A lokacin ne kuma idanunsa suka hasko masa mutumin da har abada ba zai taɓa mance kamanninsa ba. Mutumin da yake da matuƙar mahimmanci a tare da shi. Duk da irin yadda idanunsa ke son rufewa da ƙarfi da yaji, hakan bai hana shi ware idanun ta ƙarfin tsiya ba.

Kafin yasan abin yi ya nemi jinsa da ganinsa ya rasa su. Barci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.

Sanyin asuba ya yi sanadin farkawan Mujaheed, a lokaci guda abubuwan da suka faru suka shiga dawo masa kai, sai dai ya kasa tuna fuskar waye ya yi arba da shi, a wancan lokacin. Abinda zai iya tunawa dai yasha lemu, bayan yasha ne ya rasa komai na tunaninsa. Takura kansa ya ke kokarin yi da ƙarfi da yaji sai ya tuno abinda ya gani a wancan lokacin, amma hakan ya gagara.

A daddafe ya tashi da nufin shiga ɗakin Jawaheer, a lokacinne kuma ya ci karo da mutum, hakan yasa ya riƙe shi sosai. Ganin bai yi ninyar ƙwacewa ba, yasa ya juyo da shi da nufin ganin waye? Gabansa ne ya faɗi da ƙarfin tsiya ya ware idanunsa da suka yi masa nauyi yana duban Jabir.

A lokacinne kuma Jawaheer ta fito tana bin bango tana shessheƙan kuka. Jabir kawai duban Mujaheed yake, yana jiran ya yi masa dukkan hukuncin da ya gadama. Ba zai taɓa yunƙurin kare kansa ba, domin kuwa yasan ko da ya yi hakan aikin banza ne! Haka zalika yasan Mujaheed sarai da fushi, ba kasafai yake iya yiwa mutum uzuri ba.

Jawaheer ta ɗora hannu akai tana aikin rusan kuka, tasan tata ta ƙare yau. Shi kansa Jabir bai san lokacin da hawaye suke ziraro daga idanunsa ba. Sunan Allah kawai yake ambata a zuciyarsa yasan shi kaɗai ya isa ya kuɓutar da shi.

<< Jawaheer 12Jawaheer 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×