Mujaheed ya kasa magana, haka ya kasa daina dubansu.
"Jabir meyasa baka gaya min kana son Jawaheer ba? Meyasa ka zaɓi kayi mata ciki tana gidan ɗan uwanka? Jabir kai ɗan uwana ne, duk abinda kake so a duniyar nan dole zan tayaka sonsa ko menene. Na gode Allah da nake renon ɗan ɗan'uwana. Haka zan shige maka gaba akan komai insha Allahu."
Jabir yana girgiza kai, Jawaheer tana girgiza kai, amma tuni Mujaheed ya fice daga gidan gaba ɗaya. Daga dukkan alamu Masallaci ya wuce.
Jabir ya nemi wuri ya zauna saboda yadda ƙafafunsa suka gagara ɗaukarsa. . .