Skip to content
Part 15 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Yau weekend babu aiki, don haka ya gama kintsawa ya fito falon ya zauna tare da kunna TV. Sai kallon kawai yake yi a zahiri bai san me ake cewa ba. Ƙamshin girki ya cika ko ta ina na ƙofofin hancinsa, a take yunwar ta motsa. Amma sai ya sake tamke fuska yana cigaba da kallonsa.

A gabansa ta wuce, kai tsaye ta nufi gaban TV ɗin ta zauna tana duba kaset. Ya zura mata ido, yana jin kamar ya jawota jikinsa. Wannan wacce irin ƙaddara ce? Shiyasa babu kyau zurfafa ƙiyayya domin Allah yana iya jarabtarka a kowanne irin lokaci. Shi kam har yanzu ƙaryata kansa yake yi, babu dalilin da zai sa ya so Jawaheer. Rintse idanunsa ya yi, yana fatan Allah yasa ta tashi daga wurin da take zaune.

Kamar ta shiga zuciyarsa ta miƙe ta nemi wuce wa ta gabansa, ya fizgo ta gaba ɗaya ta zube a jikinsa. Abinda ya yi ninyar yi mata ba hakan ya yi ba. Domin murɗe hannunta ya yi, sai da ta yi ƙara ya ce, “Idan kika sake zuwa ina kallo kika tsaya min a gaba sai na cire maki rashin kunyarki. Ƙazama kawai!”

Duk da zagin ya sa mata takaici, haka soyayyarsa kamar yanzu ake shimfiɗa mata shi a zuciya, sai da ta sami daman ba shi amsa, “Naji ni ƙazama ce, a haka ɗina aka kasa barina.”

Fizgewa ta yi, ta runtuma da gudu, a ya yin da ya rufa mata baya, yana jin babu abinda zai hana shi karya yarinya yau. Tana shiga ɗakin tana ƙoƙarin rufewa ya banko ƙofar, hakan yasa ta rungume shi tsam, tana faɗin, “Kayi min rai kayi haƙuri.” Yadda take maganar cikin shagwaɓa yasa shi tsayawa cak! Yana ƙare mata kallo. Da gaske ta tsorata idan akayi duba da yadda jikinta ke kyarma. Yana da buƙatar lashe wannan man bakin da yake ta walƙiya. Wasu abubuwa da ke kwance a cikin jikinsa suka miƙe, babu abinda yake buƙata sama da ‘ya mace a kusa da shi.

Maza kenan mutanen mu! Kamar ba ita ce ya tsana yake wulaƙantawa ba. Idan ni ce Jawaheer sai na gwara kansa sannan zan bada kai

Ture ta ya yi, bayan ya tabbatar da ta gama mutuwa a tsaye. Ya mutsa fuskarsa ya dinga yi yana sake dubanta, “Kin raina ni da yawa, amma zan yi maganinki.”

Zura masa ido kawai tayi, sai kuma ga hawaye. Ta dinga girgiza kanta alamun tana shanye dukkan wulakancinsa. Shi kansa jikinsa ya yi sanyi, ta yadda ya kasa haɗa idanu da ita. Ficewa ya yi, abin yana cigaba da damunsa. Yana cigaba da dukansa. Yana jin tabbas ya daɗe yana aikata kuskure a cikin rayuwar aurensa. Sai dai kuma yana tunanin ya sakko da kai, Jawaheer ta raina shi. A duniya babu abinda ya tsana sama da raini, baya son yarinya ƙarama ta raina shi. Duk yadda ya shagwaɓa Naylaa bata taɓa raina shi ba, komai ya ce mata to ne kawai babu wani musu.

Abu kamar wasa ƙaramar magana tana neman ta zama babba, Mujaheed ya rasa dukkanin natsuwarsa, musamman yadda Jawaheer tayi masa yajin ƙarfi da ya ji, ta hana idanunsa ganinta. Gaba ɗaya ta daina zaman falon, sai ta tabbatar da ya fita sannan take fitowa ta gama hidimominta cikin gaggawa ta rufe ƙofarta.

Mujaheed ya kasa fassara a irin duniyar da yake, farin ciki ko baƙin ciki? Natsuwa ko rashinta? Kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar da ya sauya, haka ya rame. Sai dai tambayar duniyar nan idan zaka yi masa akan abinda ke damunsa, baya taɓa bayar da amsa, sai dai ya ce babu komai. Yana jin kunyar ya ce wai kamarsa ya faɗa tarkon son Jawaheer. Idan har yana son Jawaheer ina soyayyar Naylaa? Kai yana ji a ransa in har ya yi hakan bai kyauta wa Naylaa ba. Ya tabbata idan shi ne ya mutu ya bar Naylaa a duniya, ba zata taɓa kusantar aure ba. Meyasa shi zai so wata?

A lokaci guda ya yi fatali da wata soyayyar Jawaheer, kawai ya fuskanci aikinsa. Da ƙarfi yake danne damuwarsa akanta, sai dai abinda Mujaheed ya mance ita zuciya baka isa kayi mata dole ba. Kana iya sarrafa komai da ke jikinka, amma banda zuciya.

Yau Jabir ya kawo masa ziyara har ofishinsa. Mamakin ramar da ya yi yasa ya zura masa idanu,bayan sun gaisa.

“Ya na ganka duk ka lalace?”

Jabir ya buƙata yana mai gyara zama. Mujaheed ya ɗan sosa kansa yana lumshe idanu,

“Babu komai ayyuka ne kawai suka sha min kai.” Jabir ya taɓe baki,

“Idan tayi wari zamu ji. Ya maganarsu Safina? Ansake su ko?”

“Eh iyayenta sun zo akayi ta bani haƙuri. Sai da Abba yasa baki sannan na ƙyaleta. Amma ai tasha wahala a hannuna.”

Jabir ya jijjiga kai.

“To ya maganar Jawaheer? Ina fatan zuwa yanzu komai ya daidaita?”

“Tukunna dai! Ina sake nazarin yarinyar tukun.”

Jabir ya dube shi, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce, “Tana tantanceka ko kana tantanceta? Duk wanda ya ganka Mujaheed ba sai ya tambaya ba, ka faɗa tarkon so, kuma dama na gaya maka, ka daina zafafa ƙiyayya, haka ka daina zafafa soyayya. Yau da wasu idanun zaka dubi Jawaheer ka gaya mata ka faɗa tarkon sonta? Idan ma raini kake gudu ai kai ka siya da hannunka.”

Mujaheed ya yi shuru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce, “Yanzu kana nufin ina son Jawaheer? Gaskiya ban yarda ba. Idan na so Jawaheer ita kuma Naylaa fa?”

“Naylaa da sonta zaka mutu, amma tabbas ka faɗa tarkon soyayyar Jawaheer. Kowanne kuma yana ɗauke da nasa ɓangaren. Mujaheed ka dage da addu’a.”

Mujaheed sarkin kafiya, ya dage kuma ya kafe akan shi sam baya son Jawaheer hasashe ne kawai Jabir ke yi. Dole ya haƙura ya ƙyale shi.

Yau yana dawowa aiki ya ganta zaune a tsakar gida ta harɗe tana karatu. Fuskar nan babu fara’a. Shi kansa sai da ya ji gabansa ya faɗi. Haka ya tsinci kansa da kasa fitowa a cikin motar, kawai ya zauna ya zuba mata idanu. Shi bai taɓa sanin haka take ba, sai kwanan nan da giyar ƙiyayyar ta sake shi. A karo na farko ya ji kunyar mahaifinta ya kama shi. Ido da kunya ace mutumin da ya gama tijarawa yau ya koma yana son ‘yarsa. Ya zama dole ya fara zuwa ya gyara mu’amalarsa da iyayenta. Ƙila ta hakan za su sami zaman lafiya.

Fitowa ya yi daga motar ba tare da ya sake dubanta ba, haka itama bata dube shi ba. Har zai shige ya dawo da baya, da nufin gasa mata magana. Sai kuma ya yi wani tunani kawai ya wuce abinsa.

Da sassafe ya shirya yana sauri ya kama hanyar Kaduna, ya ji muryarta cikin taushi take masa magana, “Ina son zuwa gidan iyayena.”

Ji ya yi gabansa ya faɗi da ƙarfin gaske, ya yi ta maza ya waiwayo, “Me zaki je yi?”

“Na gaji da zama a gidan nan, ina son ka sallameni kawai in tafi.”

Da ace Mujaheed zai yi wani yunƙuri, babu abinda zai hana shi bai zube anan ba. Sai dai namijin gaske ne, don haka ya sake tamke fuska,

“A lokacin da naso ki tafin ai baki tafi ba. A yanzu kuma sai na gadama zan rabu da ke. Idan kika kwantar da hankalin kina zaune zaki ga abinda kike buƙata. Daga ƙarshe ki koyi ladabin magana kafin ki furta min.”

Ficewa ya yi da sauri yana jin tsanar kansa. Yana mamakin yadda har yanzu zuciyarsa ta kasa koyon yadda ake lallashin mace.

Kai tsaye Kaduna ya nufa, ya fara ɗaukar Jabir sannan suka wuce gidan Mainasara. Cikin sa’a suka same shi a gida. Tun daga kan irin gaisuwar da Mainasara ya gani agun Mujaheed mamaki ya kasa barinsa. Har zuwa lokacin da yake neman afuwarsa, a matsayin mahaifinsa ne ya turo shi ya bashi haƙuri.

Haƙiƙa da za a leƙa zuciyar Mainasara da antsinci farin goro a ciki, saboda farin ciki. Cike da fara’a ya tabbatar masu da babu komai. Har suka ɗan taɓa hira suka ci abinci, yana jan su da hira kamar wani abu bai taɓa faruwa ba. Haka ma mahaifiyar Jawaheer ta fito suka gaisa sosai.

Haka Mujaheed ya tafi ya bar farin ciki a zuciyoyin mutanen gidan. Haka Mom ɗinta ta kirata a waya take gaya mata dukkan abinda ya faru. Mamaki yasa Jawaheer ta ce, “Mom Mujaheed fa kika ce? Kai gaskiya ba shi bane.”

Mom ta sake maimaita mata abinda ta gaya mata da farko, kamar wacce take son ta haddace kalaman. Jinjina kai Jawaheer ta ci gaba da yi, tana sauraren huɗubar mahaifiyarta. Godiya tayi mata suka yi sallama.

A gajiye ya dawo, daman tana tsaye a windo. Tana ganin ya kusan shigowa ta fasa ƙara tana duban ƙafarta. Da sauri ya ƙaraso gabanta shima ya riƙe ƙafar a gigice yana tambayarta abinda ya faru? Girgiza kai tayi tana cijewa,

“Bugewa nayi.”

“Ayya sannu. Bari insami ruwan zafi sai a gasa ƙafar kada tayi tsami.”

Tana nan zaune ya miƙe. Da kallo ta bi shi, tana mamakin mutumin da bai iya kulawa ba? Ina ya samo wannan sabon ilimin akan nuna kulawa?

Da roba ya dawo ya ɗinga gasa mata ƙafar, wanda a zahiri babu abinda ya sameta, kawai huɗubar mahaifiyarta take bi. Yana gamawa, ya sauya fuska ya miƙe ya barta agun. Sau tari da ya fara bata kulawa Naylaa ta faɗo masa a rai komai ya lalace kenan, sai ya koma jin haushinta.

Tashi tayi, ta bi bayansa a hankali ta leƙa ɗakinsa. Sosai ya bata tausayi, yana gaban hoton Naylaa ya zura mata ido yasa ɗan yatsarsa yana shafar hoton.

“Naylaa.. Babu ranar da garin Allah zai waye rana ta faɗi, ban yi maki addu’a ba. Insha Allah zamu haɗu a Aljannah, a matsayin miji da mata. Baki yi gaggawa ba, ni kuma ban yi jinkiri ba. Ina addu’ar Allah ya gajarta min zaman duniyar ta hakane kaɗai zan sami sassaucin halin da nake ciki.”

Jawaheer da hawaye ya shiga kwararowa ta ƙaraso ta dafa bayansa. Hakan yasa ya dakata da maganar da yake yi, ya kuma juyo ya dubi fuskarta da hawaye ke kwance, hakan yasa ya sunkuyar da kai.

“Ka yarda da ni aboki, har yanzu ina raye. Gangar jikina ne kawai yake kwance a ƙabari, amma kuma zuciyata har yanzu tana raye.”

Mujaheed ya miƙe cikin wani irin fushi. Idan Jawaheer tana tuna masa da zuciyar nan sai ya dinga jin tsanarta a zuciyarsa. “Har abada ba zaki taɓa zama Naylaa ba. Fice min a ɗaki!”

Ya faɗa cikin ɗaga murya. Jikinta na rawa ta fice da gudu tana kuka. Riƙe kansa ya yi da ƙarfi, wani gefe mai rauni daga cikin zuciyarsa yana tuhumarsa dalilin da zai sa ya dinga yi wa Jawaheer haka. Meyasa yake jin zafinta da yawa? Ya zama dole ya je ya bata haƙuri,ya kuma lallasheta.

Duk da zuciyarsa tana hana shi isowa gareta, dole ya yi ta maza ya bi bayanta. Sai dai tuni ta sawa ƙofarta makulli. Girgiza kai kawai ya yi ya koma falo ya zauna shuru.

Daga inda yake yana iya jiyo shessheƙan kukanta. Haka kowani saukar kukan yana cin nasarar tarwatsa dukkan wata na’ura da ke aiki a sassan jikinsa. Ji yake kamar ana bin duk wani wuri da ke ɗaure a jikinsa ana kwance shi.

Da ƙarfi ya riƙe kansa kawai yana salati. Daga bisani ya fice daga gidan gaba ɗaya.

Ita kuwa Jawaheer kuka kawai take yi, ta rasa ko sai yaushe zata sami ‘yancin kanta kamar yadda Najeriya yau take murnar samun ‘yancin kai?  Tana tunanin duk ranar da itama ta sami ‘yancin kanta dole zata sa kore da fari, domin nuna nata farin cikin.

Kwananta biyu ta ƙi fitowa, hakan ya tsorata Mujaheed ƙwarai da gaske. Gashi ta ƙi buɗe kofar. Tsoron abinda zai iya faruwa da ita, yasa ya ɓalla ƙofar.

A yashe ya sameta, a tsakanin matacciya da kuma rayayya. Ɗaukarta ya yi cak! Ya rungumeta a ƙirjinsa yana magana kamar wanda ya fita hayyacinsa, “Jawaheer! Kema tafiya zaki yi? Meyasa zaki illata kanki da yunwa? Meyasa Jawaheer? Idan nayi maki laifi abinci babu abinda ya yi maki.”

Shimfiɗeta ya yi akan gadon ya wuce kitchen. Dawowa ya yi da zazzafan tea ya ɗago kanta yana bata. A hankali take karɓa hawaye na sauka bisa fuskarta. Ajiye kofin ya yi ya sa hannu yana ɗauke hawayen.

“Sorry Dear. Bana son kukan nan.”

Bata tanka masa ba, haka bata daina kukan ba. Tunanin hanyar da ya kamata ta hora shi kawai take yi. Tana son ta gane Mujaheed yana sonta ko kuwa? Idan har ya tabbata baya sonta, tayi alƙawarin rabuwa da shi, na har abada. Ko da kuwa hakan yana nufin rasa rayuwarta ce gaba ɗaya.

Kiran Jabir tayi, ta gaya masa ƙudurinta, ya bata goyon baya, ya ce ta zo gidan iyayensa ne, domin shi kansa ya gaji da girman kai irin na Mujaheed. Bayan ya fita aiki ne, ta kwashe kayan sawanta, ta ɗan yi masa rubutu a farar takarda, ta ajiye yadda zai gani ta fice sai tasha, daga can ta ɗauki shatar mota tayi hanyar Kaduna.

Sannu a hankali Jawaheer ta fayyacewa Umman Jabir duk abinda ke faruwa, hakan yasa Umman ta sanyata ta kira iyayenta ta gaya masu tana wurinta. Haka Baba Ma’aruf yana dawowa Umma ta maida masa komai. Shima ya ɗaga waya ya kira Abban Mujaheed suka tattauna. Don haka Mujaheed ne kaɗai bai san halin da ake ciki ba.

Yana dawowa ya kishingiɗe akan doguwar kujerarsa idanunsa suka hasko masa ƙofar Jawaheer a buɗe, don haka ya miƙe ya nufi ɗakin. Gabansa ya faɗi da ƙarfi ya shiga nemanta yana ƙwala mata kira, amma babu ita babu dalilinta. ‘Yar takardar ya ɗauka yana duba wa.

Na tafi wani wuri mai nisa, soyayyar Naylaa a zuciyarka tayi ƙarfin da babu mahaluƙin da ya isa ya cire maka ita, sai wanda ya ƙagoka. Idan nace zan zauna a hakan watarana zaka zo ka sami gawata kwance a gidanka. Na tabbata baka da asara iyayena kaɗai zaka bari da ciwon zuciya. Ka sani, ba ni ce nace a dasa min zuciyar matarka ba, ban san lokacin da akayi hakan ba, amma sai ya kasance na fi kowa laifi agurinka. Ka tsaneni. Zuciyar Naylaa da ke jikina ita ke wahalar da ni. Ina son ka sauwaƙe min, ni na tafi wani wuri, ko gidan iyayena ban nufa ba, kada ka sha wahalar nemana. Ina yi maka addu’ar Allah ya kawo maka sassauci da dangana Mijina.

Taka har kullum matarka ada Jawaheer.

Dunƙule takardar ya yi ya cillar, ya koma ya zauna. Ya ma rasa tunanin me zai yi? Dole ya sanar da iyayensa kada lamarin ya yi girma.

Bayan ya gama yi wa mahaifinsa bayani ne, Abban ya dube shi sosai. Yana tausayin ɗan nasa duk ya lalace. Amma a zahiri ɗaure fuskarsa ya yi sosai, “Mujaheed nayi maka faɗa, nayi maka nasiha, na yi maka jan ido, amma ka ƙi saurarena. Idan banda yarinyar nan zuciyar Naylaa ce a jikinta, wa ya gaya maka zata kai iwar haka a gidanka? Tayi ƙoƙari ma a hakan. Don haka sai kaje ka nemo masu ‘yarsu, sannan ka kawo min takardar sakinta, nima na gaji da wannan auren. Kuma ka dage wajen ganin ka zama cikakken musulmi wanda a kullum yake zaune cikin shirin karɓar ƙaddara aduk yadda ta zo maka. Idan ka cigaba da ganganci kana barin shaiɗan yana maka huɗuba, zaka sha wahala matuƙa. Tashi ka bani wuri.”

Miƙe wa ya yi jiki babu ƙwari, haka wurin Ummansa ma bai ga fuska ba, hakan yasa ya koma gidansa shuru. Domin dai bai san ta inda zai fara nemanta ba. Ji ya yi gidan ya yi masa girma. Babu Naylaa babu Jawaheer.

Kiran iyayenta ya yi ya gaya masu Jawaheer ta gudu. Yana jiyo yadda suke salati da iya ƙarfinsu, hakan yasa ya karaya ya sauke wayar. Haka fargaba yana ƙara shigarsa.

Biro ya ɗauko da takarda yana jin gara kawai ya sake ta ɗin, tunda shi bai san ranar da zai iya daina son Naylaa ba, haka ya kasa ƙanƙareta a cikin zuciyarsa.

Duk yadda yaso hannunsa ya rubuta sakin nan, abin ya faskara. Dole ya koma ya ƙura wa takardar idanu ba tare da ya iya rubuta ko kalma ɗaya ba.

Dare ya yi dare, Mujaheed ya kasa rintsawa. Yana jin zuciyarsa tana zafi, yana jin wani irin raɗaɗi da babu Jawaheer a gidan. Ashe dama haka ya damu da ita? Ashe ba zai iya rintsawa akan wata ba Naylaa ba? Kalaman Abbansa suna sake tarwatsa zuciyarsa. A daren ya ɗaga waya ya kira mijin Suhaima yake tambayarsa ko Jawaheer ta zo gidansa?

Anan Aliyu yake gaya masa yadda Suhaima suka yi da Jawaheer. Hankalin Mujaheed ya ƙara tashi. Tausayin Jawaheer ya ƙara mamaye ko ina na zuciyarsa. Anan yake warwarewa Aliyu abinda ya faru, ya ƙara da cewa, “Mata iyayen tsegumi. Su dai babu ruwansu babban burin su kawai ‘yar uwarsu ta faɗa matsala. Me zai sa duk yadda Suhaima take da Jawaheer ta yi hakan?”

Mujaheed ya dinga jinjina kai, sannan ya sauke wayarsa cike da ɓacin rai.

Suhaima da ke gefe jikinta a sanyaye ta ce, “Haba Aliyu meyasa ba zaka ɓoye sirrin matarka ba? Na gaya maka nayi kuskure. Ni kaina ban ji daɗin abinda na aikata mata ba, sharrin shaiɗan ne.”

Aliyu ya juya mata baya yana gyara kwanciyarsa tare da cewa, “Sharrin gulma da hassadarki dai zaki ce. Da kun aikata hauka, sai ku dawo kuna cewa sharrin shaiɗan. Shi kansa Shaiɗan ɗin baya zuwa wurin da ba a gayyace shi ba. Walh Suhaima na gaza daina mamakin ki. Irin wannan da kin fito mata da asalin fuskarki ne, da kin huta da ɓoye muguwar fuskarki a cikin mai kyan. Kin yi wa Jawaheer haka, waye ba zaki yi wa ba? Ki gaggauta nemanta ki nemi afuwarta don Allah.”

“Insha Allah, zan yi hakan. Amma ka daina ɗaure min fuska hakannan na tuba.”

Tsakanin miji da mata sai Allah tuni suka rungume juna suna aikawa junan su da saƙonni.

<< Jawaheer 14Jawaheer 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×