Yau weekend babu aiki, don haka ya gama kintsawa ya fito falon ya zauna tare da kunna TV. Sai kallon kawai yake yi a zahiri bai san me ake cewa ba. Ƙamshin girki ya cika ko ta ina na ƙofofin hancinsa, a take yunwar ta motsa. Amma sai ya sake tamke fuska yana cigaba da kallonsa.
A gabansa ta wuce, kai tsaye ta nufi gaban TV ɗin ta zauna tana duba kaset. Ya zura mata ido, yana jin kamar ya jawota jikinsa. Wannan wacce irin ƙaddara ce? Shiyasa babu kyau zurfafa ƙiyayya domin Allah yana iya jarabtarka a kowanne irin. . .