Ko kafin Mujaheed ya tunkare su, Jawaheer ta ƙaraso akan ƙaton mashin ɗinta mai kama da jirgin ruwa. Hular ta sake ƙwabewa yalwataccen gashinta ya watsu a bayanta, har yana rufe mata fuska. Siraran yatsunta tasa masu kyau, wa'inda suka ji ado da ƙumbunan kanti ta mayar da gashin baya, a lokaci guda ta ɗaure gashin ta ƙudundune.
Riga da wando ne a jikinta masu ɗaukar hankali, tana yamutsa fuska kamar wacce bata taɓa kallon rana ba. Mujaheed ya rasa dalilin da a karo na biyu ya sake jin gabansa ya faɗi. Meyasa tun kafin ya. . .