Skip to content
Part 4 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

“Jawaheer zan gaya maki wacece Nayla, amma zan jira inga iya haƙurin ki, zan tsaya induba shin da gaske kina son Mujaheed? Kiyi haƙuri Mujaheed zai dawo gareki, zai zama tamkar ke kike sarrafa shi. Ni zan wuce.”

Jawaheer ta kasa magana sai hawaye da ke bin idanunta. Tana son ta ce a taimaka a kawo mata Zarah tayi kwana biyu, ta tabbata zata fi samun natsuwar zama a gidan. Amma har ya wuce bata iya furta masa komai ba.

Tashi tayi tana leƙa ko ina, har ta iso cikin ɗakin barcinsa. Tsintar kanta tayi da wanke masa ko ina ta gyara shi tsaf. Ko ina ya ɗauki ƙamshi. Ta rufo ƙofar ta fice.

Yana dawowa ya doshi ƙofarsa gabansa ya yi wani irin faɗiwa. Ko rantsuwa ya yi ba zai yi kaffara ba Nayla ta shigo cikin ɗakin nan.

Rufe idonsa ya yi yana karanto duk wani addu’ar da ta shigo bakinsa. Ficewa ya yi, daga ɗakin ya wuce ɗakin Jawaheer. Tana zaune bisa dadduma ya sameta.

“Ke! Waye ya shigo ɗakina?”

A tsorace ta amsa da ita ce. Tsaki ya ja ya nunata da yatsa, “Idan kika sake shiga inda nake sai na karya ki. Ki fita a dukkan abinda ya shafe ni. Ai na gaya maki kafin ki shigo, kika amince da zaki iya. Kin shiga rayuwata kin wargaza min duk wani shirina, kin jawo na karya alkawarirrika masu yawa. “

Kawai ya juya, yana jin wani irin ɗaci a cikin ransa.

Gudu take yi da iya ƙarfinta, haka duk yadda take da tsoron ruwan sama, haɗi da tsawa, hakan bai hana ta gudun ceton rai ba. Wata mace ke binta da wuƙa wacce shekarunta ba zai wuce nata ba. Gudu take yi, tana waiwaye ko Allah zai sa ta ci karo da wasu wa’inda za su iya taimaka mata.

Sai dai titin kamar ansa tsintsiya anshare mutanen da ke kai kawo. Wani tuntube ta yi, wanda yasa gaba ɗaya ta zube a wurin tana ja da baya. Cikin kuka ta ce, “Me nayi maki Nayla? Meyasa kike son ki cutar da ni? Kiyi haƙuri mana, ba laifina bane ki yafe min.”

Wacce aka kira da Nayla ta zaro idanunta da suke fitar da wani haske, “Kin dameni Jawaheer! Kin hanani kwanciyar hankali! Kullum sai kin ambaceni har a cikin Sallarki sunana kike kira akan me? Kin raba ni da farin cikina, duk da kin same shi kin gaza ƙyaleni. Na tsaneki Jawaheer! A yanzu ke ɗaya ce matsalata, don haka dole ki bar duniyar da kike ɗokin zama a cikinta. Zan kashe ki nima inhuta da masifarki.”

Ta sake yo kanta, cikin ikon Allah ta sare ta da wuƙan nan, hakan yasa Jawaheer ta kwantsama ihu, tana buɗe ido idanunta suka ɗinga yi mata gizo, cikin ƙaraji ta tashi daga ita sai rigar barci, kan nan babu ɗankwali tayi waje da gudun gaske.

A wannan lokaci ruwan sama ake tsugawa Mujaheed yana tsaye a gaban windo ya kasa rintsawa, dan haka a kunnensa ya jiyo ihun Jawaheer haka akan idonsa ta fice da gudun gaske.

Cikin sauri ya biyo bayanta, tuni ta buɗe ƙofar Gate tayi waje da gudun gaske. Hakan yasa ya biyo bayanta. Gudun da take yi ya bashi mamaki, da ƙyar ya iya kamota. Gaba ɗaya suka tsaya suna haki, sai tirjewa take yi, “Ka ƙyaleni ingudu, ashe Nayla aljana ce? Ashe da aljana kayi soyayya?”

Hannunsa yasa ya zabga mata mari, wanda yasa ta ɗaukewan wutan wani ɗan lokaci. Mujaheed zai juri komai amma banda aibata masa Nayla. Gani ya yi tana ta mutsu-mutsu alamun ya sake ta, wata zuciyar tana tunzura shi ya ƙyaleta kawai ta wuce, wata zuciyar kuma tana ankarar da shi fushin su Umma.

“Idan baki natsu ba, zan watsar da ke cikin kwata, inyi tafiya ta. Baki da hankaline? Baki ganin dare ne? Idan tafiyar zaki yi ki bari ido na ganin ido babu wanda zai hana ki.”

A tsorace ta ware idanunta, suka ƙurawa juna idanu ta hasken walƙiyan da ake yi. Saurin kawar da idanunsa ya yi, ita kuwa tasa kuka cikin wani irin rauni me taɓa zuciyar duk wani me saurarenta. Jikinta babu inda baya rawa. Shima cikin sanyin jikin ya jawo ta jikinsa, ya kwantar yana shafa gashinta da ruwa ya gama jiƙa shi. Wani tausayinta ya rufe shi, baya son ganin mace tana kuka.

Tana ƙudundune a jikinsa tana wasu surutai, “Na ganta da wuƙa tace zata kashe ni idan ban barka ba.”

“Kada ki damu Nayla bata mugunta, bata taɓa faɗa da wani ba, bare har ta iya riƙe wuƙa. Kada ki sake haɗa min matata da aljana.”

Sakinta ya yi, ya juya kawai. Jawaheer ta shiga binsa a baya zuciyarta tana sake jin tsoron wannan wacce irin soyayya ce? Idan ka sami miji yana yi maka irin wannan soyayyar ka gama samun komai. Bata taɓa ganin irin wannan zazzafar ƙaunar ba. Ko da kuwa mace tana kwanciya ne namiji yana taka ta.

Haka suka dawo dukkansu suka zauna a falon babu me iya furta komai, dubanta ya yi, kayan barcin sun manne a jikinta ta yadda ake iya ganin komai. Kawar da kansa ya yi yana son ya ce ta wuce ta sauya kaya, baya son kuma magana ta sake haɗa su. Don haka ya rufe idanunsa.

“Aboki ina jin zafi a wani wuri, kuma ba zan iya gaya maka sunan wurin ba.”

Dubanta ya yi, ya ce _”Faɗa min ko ina ne kinji Friend? Baki da wanda ya fi ni, baki iya gayawa kowa matsalar ki sai ni, idan kika fara ɓoye min matsalarki zan shiga damuwa.”

Hannunsa ta kama ta yi rubutu, yana buɗewa ya yi maza ya kalleta. Da gudu ta nemi tashi, ya jawo ta ta dawo kusa da shi.

“Alamun kin girma ne friend. Maza jeki ki gayawa Umma zata yi maki bayani. Amma kada ki gaya mata kin faɗa min kin ji?” A sanyaye ta ɗaga masa kai.

Juyowa ya yi, yana kallon Jawaheer ta ɗauko Kaset. Duban Kaset ɗin ya yi, hankalinsa ya sake tashi. Nayla kaɗai tasan inda Kaset ɗinnan yake, ya nema har ya ji babu daɗi, shi ya bata ajiya. Yau ga Jawaheer ta ɗauko masa. Lokaci guda ya ji zuciyarsa tana gaya masa ya tambayi Jawaheer abubuwan da ya baiwa Nayla ajiya masu matuƙar mahimmanci ya tabbata zata iya sani. Lokaci guda wata zuciyar tayi fatali da wannan huɗubar.

Tashi kawai ya yi ya fice ya bar mata ɗakin.

Da sassafe ta shirya ko tambayarsa bata yi ba ta wuce gidan Ummansa, kasancewar gidan tsallake ne kawai a tsakanin su. Tana yin Sallama ta rushe da kuka, hakan ya tada hankalin Umma kuma tasan za ayi hakan. Jawo ta ɗaki tayi tana lallashi. Daga ƙarshe ta ce, “Ummana, Walh Nayla aljana ce, tana zuwar min har cikin mafarki da wuƙa a hannu.”

Umma ta ɗan yi shuru, sannan ta ce “Nayla mutum ce kamar kowa, ba aljana ba ce. Kinsa ta a ranki ne shiyasa kike ganinta a cikin mafarkinki. Yanzu abinda zaki mayar da hankali akai ba zai wuce kula da mijinki ba, ki daina sa komai a ranki kin ji? Gaya min yana cutar da ke?”

Cikin sauri ta girgiza kai, “A’a baya yi min komai.”

Murmushi Umma tayi, tana hango halayyar Nayla sak a tare da Jawaheer. Idan kuwa hakan ya faru, za su fi kowa farin ciki.

Tana dawowa ta same shi zaune a bakin ƙofa yana duba jarida, “Daga ina kike?”

Jikinta na rawa, saboda tsoronsa da ta saka wa kanta ta ce, “Gidan Ummana naje.”

Ɗago kai ya yi yana dubanta. Bai sake magana ba ya cigaba da karatunsa.

Haka ta zauna tayi tagumi, komai ya fita kanta. Suhaima ƙawarta tayi ta kwaɗa sallama shuru, har dai ta gaji ta kutsa kanta ciki. Tagumin ta zare mata tana yi mata kallon mamaki, “Jawaheer anya kuwa ke ce? Meke faruwa haka?”

Ajiyar zuciya ya ƙwace mata, kamar jira take tasa kuka tana gaya mata dukkan abubuwan da suke faruwa. Suhaima ta gyara zama tana duban Jawaheer,

“Yanzu shine kika tsaya kina kuka? Nayla ɗinnan dai ba kyau ta fiki ba, ba iya gayu ta fiki ba. Ke da zaki mayar da kanki kamar wata mara wayo? Ai nuna masa zaki yi kin fi kowa son Nayla. Amma kin tsaya kina wani kuka. Kuma duk inda yake zama ki mayar da wurin gurin zaman ki. Wataran ma kiyi shigar banza ki zauna ba tare da kin dube shi ba. Ke ga salo iri iri sai wanda kika zaɓa?”

“Suhaima Nayla fa aljana ce, ta yaya zan iya da aljanu? Kowa sonta yake. Jiya baki ga yadda ta shaƙe ni ba.”

Suhaima ta girgiza kai cike da tausayin Jawaheer, “Ki ƙara haƙuri, amma dai Nayla ba aljana ba ce. Tashi mu shiga kitchen.”

Haka suka shige kitchen ɗin tana mamakin yadda ga komai, amma bata amfani da su. Suhaima ta dage wajen ganin ta sanya Jawaheer cikin nishaɗi, kafin suka yi sallama.

Da yamma tana sanya turaren wuta, ta ɗago tana duban ƙaton hoton Nayla, wanda dariya take yi aka ɗauki hoton, amma kuma yanzu sai taga kamar fuskarta a ɗaure. A gigice ta fizgo hoton jikinta na rawa, hakan ya yi dai-dai da faɗowan hoton ya fashe. Kallon kallo ake yi tsakanin Mujaheed da Jawaheer, fizgo ta ya yi da iya ƙarfinsa zai mareta, ta ƙanƙame jikinta hawaye na kwaranya. Sauke hannun kawai ya yi, yana dubanta kamar zai yi magana, sai kuma ya kaɗa kansa ya juya. Har ya kai bakin ƙofa ya yi magana a shaƙe,

“Idan da Nayla ce na kawo hotonki na ajiye zata fi kowa tattalin hoton dan tasan kina da mahimmanci ne a rayuwata shiyasa na kawo. Nayla wata irin mace ce da ban taɓa ganin ‘ya mace me irin zuciyarta ba. Tana da tausayi. Kina son kwaikwayon Nayla, amma kin kasa aiwatar da hakan Jawaheer. Yau kuma sai kika fasa min hotonta, idan mutuwa zanyi in mutu ko?”

Jawaheer bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana shessheƙa, “Ka yafe min, ka yafe min, ban taɓa ƙin Nayla ba, ban taɓa ƙin abinda kake so ba, tsautsayi ne yasa na fasa hoton ba wai don bana sonta ba. Ina son Nayla.”

Juyowa ya yi sosai ya zura idanunsa a cikin nata, ya aika mata da wani irin murmushi, wanda bata taɓa ganinsa yana yin irinsa ba. Zata ajiye yau a cikin rana masu matuƙar mahimmanci. Juyawa ya yi ya fice abinsa.

Durƙushewa tayi ta dafe ƙirjinta, ashe so tsantsar wahala ce kawai a cikinta? Ashe soyayya bata da sauƙi? Sai yaushe zata daina kuka? Sai yaushe zata yi farin ciki? Ita kuma irin tata jarabawar kenan?

*****

“Sunana Nayla, na tsinci kaina a cikin farin ciki da kike son Aboki, da farko dai aboki yana da kirki, baya son fushi na, nima bana son nasa. Mayen kunun gyaɗa ne, duk safiya yana son shan kunun gyaɗa. Idan yana cikin matsanancin fushi inhar na miƙa masa hannuna, fushin zai fice daga zuciyarsa sai kawai ya kama hannuna, muyi murmushi. Sau tari da idanu muke magana ba tare da mun bari Ummana da Abbana sun sani ba. Bani da ƙawa sai shi. Kema ki riƙe min shi kafin indawo inkarɓi abuna. Zan dawo zan karɓe Aboki zamu cigaba da rayuwa me daɗi fiye da rayuwarmu ta baya. Ga wannan saƙon ki bashi.”

Tana miƙa hannu da ninyar ta karɓa ta ji bugun ƙofa, hakan yasa ta buɗe idanu taga haske. A gigice ta tashi ta buɗe ƙofar. Kallonta ya yi sama da ƙasa, sannan ya kau da fuska, “Umma tana falo.”

Yana ji tana gaida shi ya fice. A falo ya sami Umma yana duban agogo, “Umma zanje Office sai na dawo.”

Umma ta harare shi, “Dawo nan ina son magana da kai.”

Babu musu ya dawo yana sake duban agogo, “Mujaheed kaji tsoron Allah. Kada ka mance sai Allah ya tambayeka yadda ka zauna da yarinyar nan.”

Shafa kansa ya yi, yana yamutsa fuska. “Umma ta ce nayi mata wani abu ne?”

“Har sai ta faɗa? Ka ga yadda yarinyar nan tayi baƙi ta rame? A haka aka kawo mana ita? Tashi ka wuce Abbanka yana son ganinka anjima.”

Tunani ne fal a ransa ya sa kai ya fice. Abubuwan suna neman su cukurkuɗe masa, ba kamar yadda ya zata ba.

<< Jawaheer 3Jawaheer 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×