Yau garin an tashi da sanyi, don haka dukkan su suna sanye da kayan sanyi, suka kama hanya domin shiga ƙaton kanti domin siyan abubuwan da basu da shi.
Sun yi nisa wajen siyayya, Mujaheed ya ji muryar wata tana cewa, "MD idonka kenan?"
Waiwayowa ya yi, tare da murmushi. Nayla tana gefensa tana dubansu. Hannu ta miƙa masa, alamun su gaisa. Abin mamaki Nayla ta yi saurin janye hannunsa da suka kusa haɗewa, ta miƙa mata nata. "Da ni ya kamata mu gaisa, shi kuma sai kuyi magana da baki, ko Aboki?"
Mamaki yasa ya kasa. . .