Kamar yanda Sakina ta zata hakan ce ta kasance, domin har suka yi bacci Kamal bai dawo ba.
A can wajen Dinner kuwa ba su suka tashi ba sai wajen sha-biyun dare, kai tsaye gidan Hajiya Shema'u suka raka amarya kafin daga baya ko wacce ta kama gabanta.
Abokan Ango sun tsaya sunyi siyan baki kamar yanda ake yi a al'adance tare da wasu Aminan Hajiya Shema'u su Hajiya Turai kenan, kafin daga baya suma su fashe su bar Ango da Amaryarsa, tare da yi musu fatan alkhairi.