Skip to content
Part 2 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by Qurratul Ayn Salees

Kamal na fita daga cikin gidan kai tsaye Unguwar jan bulo ya nufa, layin farin gida gidan Hajiya shema’u.

Da zuwansa bugu daya ya yi wa kofar gate din, mai gadi ya bude masa kofa ya shiga, da ya ke mai gadin ya san shi kuma Hajiya ta gargade shi akan Kamal, ko da wasa ka da ta ji labarin ya wulakanta mata shi, shi yasa da ya ganshi da tsumar jiki ya ke tsugunnawa ya gaishe da shi, duk kuwa da irin tarin tazarar shekarun da ke tsakaninsu domin a haife tabbas zai haifi Kamal.

Amma shi gogan naka ko a jikinsa sa asalima ko amsa gaisuwar ba ya yi, ya ke wucewa abinsa yana wani hura hanci sama, a ganinsa ya fi karfin ya tsaya amsa gaisuwar talakan ba kauye irin wannan mutumin.

Mai gadin yabi bayansa da kallo har sai da ya daina hango inuwar hular, sannan ya mike daga tsugun nen da ya ke yana mai girgiza kai tare da tausayawa Kamal a kan gudun wuce sa’ar da ya ke shirin yi wa rayuwarsa.

Gida ne wanda ya amsa sunan gida, domin tun daga wajen gate na gidan zaka san naira na kuka a cikin, labarin ya kan canja ne daga inda mutum ya yi tozali da tsari da tsaruwar cikin gidan, a wannan lokaci kai ne ka dai alkalin da zaka iya lissafin irin dukiyar da aka barnatar, amma tawadar alkalamina ta yi karanci wajen iya zayyano maku fasali na gidan.

Da sallamarsa ya sanya kai cikin  falon, sabida a halin yanzu Kamal ya zamto tamkar dan gida kamar yanda take fada a kullum, baya bukatar iso a wajenta Kafin isowarsa, duk sanda ya so ya ke kuma da ra’ayin zuwa gare ta tana maraba marhabin da shi.

Hajiya Shema’u da ke zaune saman daya daga cikin jerin kujerun da suka yiwa falon kawayenta dago kai tana amsa masa sallamar, Masha Allah shi ne abin da dukkan bil’adam da da ya yi to zali da kyakkyawar fuska irinta ta zai iya ambata mace ko namiji.

Domin ga inda kyawun asali ya ke, Hajiya Shema’u maca ce dirarriya irin matan nan masu matsakaicin tsayi da jiki daidai misali, fara ce sosai tamkar ka taba jini ya fito bama ce farinta ba ne zallah, domin zamani ya zo mana da mawuyaci ne ka samu macen da bata harka da mayukan gyaran fata masu kara fito da zallar asalin farin mutum da sheki musamman manyan mata irinsu, dogon karan hancinta da ya da ce da doguwar fuskarta tamkar an dasa shi, shi ne abu mafi kusa da ke fara janyo hankalin dukkan namijin da ya yi tozali da ita, ma’abociyar manyan idanuwa ce, mai yalwar suma dake kwance lub saman goshinta har zuwa bayanta, a takaice dai ba lallai ne daga kallo daya akan wannan mata ba ka iya gano makusarta nan take ba.

Yarinyar da ke durkushe gabanta tana danna mata kafafuwanta ta mike da sauri kai a kasa ta nufo bakin kofar da Kamal ya ke tsaye, ta dan risina kadan ta gaishe da shi tana mai cigaba da tafiya har ta fi ce daga falon, Kamal kuwa dan tabe baki ya yi kadan kafin ya karasa cikin tsakiyar falon ya nemi guri inda Hajiya Shema’u ke zaune ya zauna a gefanta kafin su kalli juna dukkansu suka yi murmushi a tare.

“Yallabaina kai ne tafe hakak Ban yi tsammanin zuwanka da wurwuri haka ba.”

Kamal ya shafo sumar kansa ta baya kafin ya dan tabe baki ya ce.

“Wallahi matar can ce ta bata min rai matuka, shi ne kawai na yi yo ta nan, domin nasan nan ne zan iya samun ishashshan farin ciki,”

Hajiya Shema’u ta dan yi wata gajeriyar dariyar irin ta manyan mata, ka fin ta bashi amsar.

“A’a fa Yallabaina ko dai kai ne ka data mata? Domin nasan halin Sakinah bana jin hakan daga gare ta.”

Kamal ya ja dogon tsaki, yana mai kau da kai gefe ya dora idanuwansa akan TV, kafin ya furta.

“Yardarki akanta harta kai haka?”

“Fiye da haka ma.”

Ta bashi amsa a takaice, Kamal ya dube ta da mamaki kafin ya basar sai ya samu kansa da fiddo mata da tambayar da ba ita ce a cikin zuciyarsa ba.

“Wai dama a halin yanzu akan samu matan da basa kishin mazajensu?”

“Kamar ya kenan?”

Kamal ya juyo da hankalinsa baki daya wajen Hajiya Shema’u, yana mai cigaba da fadin.

“E to kawai naga kamar Sakinah bata kishi akan aurenki da zan yi”

“Kai kishin ka ke so ta nuna maka kenan?”

Kamal ya yi murmushi kawai yana jujjuya amsar da zai bata cikin ransa tsayin wasu da kiku kafin ya furta mata.

“Ba haka ba ne”

“To ya ya ne?”

Kamal ya sake dago kai ya dubeta yana tantama akan amsar da zai bata, sabida sosai take yi masa kwarjini baya jin zai iya furta mata amsar da ke lullube kasan zuciyarsa.

“Mubar maganar kawai, kin kira ni tun safe na zo, ina kasuwa ne bana jinki sosai, shi yasa na bari kawai na zo har gida na ji lafiya?”

Kamal ya yi kokarin ajiye zancen da suka faro a gefe ya sanyo wani, Hajiya Shema’u ta danyi guntun murmushi domin ta gane janye zancen ya yi.

“E haka ne, dan jira ni kadan.”

Ta kai maganar tana mai mikewa ta nufi wata kofa da ke nan cikin falon, cikin wani irin taku da salon tafiya mai jan hankalin ma’abocin kallonta, Kamal da ya bita da kallo harta shige dakin ya sauke ajiyar zuciya yana mai gyara zamansa sosai akan kujerar da yake zaune, a daidai lokacin kuma ‘Yar aikinta da ta fita dazu ta yi sallama cikin falon hannunta dauke da tire ta ajiye akan dan karamin table din da ke tsakiyar falon ta juya abinta.

A daidai lokacin kuma Hajiya Shema’u ta bude kofa ta fito daga cikin dakin da ta shiga, hannunta dauke da wata bakar jaka mai shegen kyau, anyi mata adon duwatsu farare sai sheki da walwali take.

Zama tayi kusa da Kamal daidai sanda ya ke kokarin zuba lemo a cikin dan karamin kofin karau (glass), Hajiya Shema’u ta yi saurin karba ta karasa zuba masa ta miko masa ya karba fuskokinsu na wanzar da yalwataccen murmushi mai tsada, sai da Kamal ya sha kusan rabin lemon kafin ya ajiye kofin yana mai dawo da kallonsa gunta sosai da alamun sauraronsa ya ke yi akan batun kiran da ta yi masa.

Tamkar tasan abin da ya ke nufi ta sake gyara zamanta kafin ta bude jakartata ta fiddo invitation card dauri guda ta ajiye a gabansa, Kamal ya ajiye dubansa akan katunan kafin ya mika hannu ya zaro daya yana mai karanta wa.

Kayataccen murmushi ne ya kufce masa na ganin kyawu da tsaruwar katin daurin auren nasu shi da ita, sai da ya karanta sau biyu kafin ya dago kai ya dube ta.

“Dukkan wannan gatan ni ka dai?”

Hajiya Shema’u ta wanzar da takaitacciyar dariyarta kafin ta bashi amsa, wacce da dukkan alamu ta zame mata jiki ne, ko kuma dan tasan tana yi mata kyau ne ya sanya ko da yaushe take yinta oho?

“Ka wuce hakan a gare ni Yallabaina, tun da ka sanya hannu biyu ka karbi soyayyata ba tare da gargada ba tabbas zan yi maka dukkan halicci gabanin auren mu..!”

Hajiya Shema’u ta takaice zancen nata tana mai cigaba da jifansa da mayaudarin murmushinta wanda ke wanzar da farin ciki da annashuwa ga dukkan mahalukin da ya yi to zali da shi.

“Ina godiya matuka Hajiyata Allah dai ya tabbatar mana da wannan auren ya yi mana katangar karfe da duk kan wani maki gani a gare mu.”

“Amin s amin.”

Ta amsa tana mai kai hannu kan tire din ta dauki tufa ta fara ci a hankali suka hau hirarsu cikin annashuwa da jin dadi.

*****

Ko da Sakinah ta kammala ninkin kayan da ta ke yi, baki daya hankalinta ya kara tashi matuka, ga wani abu da ke kasan kirjinta wanda ke yo iyo zuwa makogwaronta ya tokare mata kirji, yaki gaba yaki baya, ta yi jugum tsayin wasu dakiku ba ta yi aune ba sai jin abu ta yi na bin fuskarta ko da ta duba hawaye ne, da saurin ta sanya hannu ta share a lokacin kuma wayarta kirar kamfanin Tecno ta fara kukan neman agaji a gare ta.

Hannu ta kai a hankali ta janyo ta cikin yanayin kasala da damuwa, ganin sunan Ummanta ya sanya ta kara karfafa jikinta da muryarta kafin ta daga wayar hade da sallama ta kara wayar bisa kunnenta.

Daga can bangaren Mahaifiyarta ta amsa sallamar tana mai cigaba da fadin.

“Lafiya dai ko Sakinah? Na ji muryarki ta yi wata iri alamun kuka kike yi ko?”

“A’a Umma, kuna lafiya yasu Sajjad”

Sakinah ta yi saurin kau da zancen, sabida bata yiwa mahaifiyarta karya, kuma ba tajin zata iya gaya mata damuwar da take ciki a halin yanzu.  

“Lafiya kalau Sakinah, ya nan gidan naku, komai lafiya kalau ko?”

“E Umma, dama yanzu nake shirin kiran ki sai ga shi kin kira.”

“E to naso ma na zo da kaina ne, sai kuma muka wayi gari Sajjad ba lafiya.”

“Ayya Sikilar ce ta motsa.”

“E amma da sauki sosai, barci ma ya ke yi yanzu haka.”

“Allah ya kara sauki”

“Amin.”

Umman ta amsa, Sakinah ta cigaba da fadin.

“Umma dama Sajidah na ke so ki bani aro ta ta ya ni aiki, sabida gobe Kamal ya ce za’a zo a dan yi mana gyare-gyaren gidan.”

“E daman na ce zan turota, domin jiya ya zo nan ya yi mana batun auren, ya ce a baki Sajidah ta ta ya ki ayyuka, juma’a ne daurin auren ko?”

Sai da kirjin Sakinah ya yi wata irin bugawa har sai da ta kai hannu ta dafe gurin, da kyar ta iya bawa Umman amsar.

“E da zu ya kawo min akwatuna biyu ma, wai na fadar kishiya.”

“Masha Allah, Sakinah..!”

Umman ta Kira sunanta, Sakinah ta amsa murya can kasa, Umman ta cigaba da fadin.

“Ki kara hakuri Sakinah akan wanda na sanki da shi, dukkan macen da ki ka ga ta ci ribar zaman aure kuma ki ka ganta zaune lafiya a cikin gidan ta, to indai kin bibiya ribar hakuri da gajiyarsa ta ke ci,  sannan ki ninka soyayyar mijinki a ranki fiye da yanda ki ka so shi kafin auren ku, ta hakan ne za ki samu damar kyautata masa tare da yi masa biyayya fiye da zamanku a da, ka da ki yarda da dukkan wata gurguwar shawarar kawa ko zancen ‘yan unguwa, ki girmama mahaifiyarsa kiyi mata biyayya tamkar yanda za kiyi min.”

“Sakinah..! Hakuri haske ne mai haska dukkan tsananin duhu, haka kuma juriya a bace mai wanzar da mutum zuwa tafarkin da bai yi tsammani ba, a matsayina na mahaifiyarki na hore ki da abubuwan nan ba dan komai ba sai dai su ne ka dai ababe masu kullewa, ki sanya a ranki aurenki a yi ke yi, kuma aure ibada ne ga ko wacce ‘ya mace ta duniya, kuma shi ne cikar mutunci da kamala ga dukkan wata ‘ya mace, ko kadan ka da ki nuna fushi ko jin haushi akan auren nan, asalima ki karfafa masa gwiwa idan da dama, hakan ka dai zai sanya ki dasa kujera a zuciyar mijinki, kujerar da babu wata wadda ta isa ta tumbuke ta, sai ma karin daraja da girma da kima da hakan zai janyo miki a gare shi.”

“Sannan ki dage da addu’a matuka, ki kasance mai raya daran barcinki, ka da ki gajiya, ka da addu’a ta yanke a bakinki duk tsanani, domin ita ce ka dai maganin da zata iya warkar miki da ciwon kishi, kishi dole ne ga ‘ya mace Sakinah amma na hore ki da yin kishi mafi tsafta akan mijinki, ki yi hakuri ki danni zuciyarki kinji Sakinah..!”

<< Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 1Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×