Tuni sun kammala haɗe kayan sha-hin Sakinah, masu aikin har sun zo sun fara aikinsu, Kamal tuni ya jima da fita, suna tsaka da haɗe na ɗakunan Hajiya suka tsinkayi sallama a tsakar gida.
"Assalamu alaikum"
Ita ce kalmar da ta wanzu a cikin kunnuwansu, Farida ce ta fito tsakar gidan tana mai amsa sallamar.
"Amin wa'alaikumussalam, shigo mana Aunty Karima."
Tai maganar fuskarta fal murmushi, matashiyar matar da ta kira da Karima ta yi murmushi ita ma tare da faɗin.
"A'a Faridah ki ce yau kina gida?, na zo rannan aka ce. . .