Skip to content
Part 6 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by Qurratul Ayn Salees

Tuni sun kammala haɗe kayan sha-hin Sakinah, masu aikin har sun zo sun fara aikinsu, Kamal tuni ya jima da fita, suna tsaka da haɗe na ɗakunan Hajiya suka tsinkayi sallama a tsakar gida.

“Assalamu alaikum”

Ita ce kalmar da ta wanzu a cikin kunnuwansu, Farida ce ta fito tsakar gidan tana mai amsa sallamar.

“Amin wa’alaikumussalam, shigo mana Aunty Karima.”

Tai maganar fuskarta fal murmushi, matashiyar matar da ta kira da Karima ta yi murmushi ita ma tare da faɗin.

“A’a Faridah ki ce yau kina gida?, na zo rannan aka ce kin je makaranta.”

“Wallahi kuwa yauma aiki ne ya zaunar da ni, da tuni na tafi.”

Ta kai ƙarshen maganar daidai sanda suka sanya kai cikin falon dukansu.

Sakinah ce ta washe baki tana mai faɗin.

“Karima ke ce a gidan? Sannu da zuwa gashi kin tadda mu kace-kace ana ta aiki”.

“Ki jimin Sakinah, ni baƙuwa ce da za ki ji kunyar na tadda ku a hargitse, ai kamawa ta ke irin wannan ranar.”

“Da gaskiyarki Karima.”

Hajiya ta bata amsa tana mai ajiye kofin da ke riƙe a hannunta wanda ta kammala shan ruwa, Karima ta durƙusa har ƙasa cike da girmamawa ta ke faɗin.

“Barka da rana Hajiya, ya jiki-jiki?”

“Barka dai Karima, jiki sai godiyar Allah, ya mai gidan naki da kowa?”

“Lafiya ƙalau wallahi, ya ce duk a gaishe ku, da tare zamu zo ma to sai aka yi masa kiran gaggawa a office.”

“Allah Sarki, Allah Ya ƙara taimaka ya baku zuri’a ta gari.”

“Amin Ya Allah”

“Aunty Karima kina nan amma kin guje mu kusan kullum Umma sai ta yi batun kin watsar da ita tun da aka yi auren Aunty Sakinah.”

Sajidah ta yi maganar tana ɗan tura baki alamun fushi, Karima ta dawo kusa da ita tare da dafa kafaɗarta.

“Haba dai ka da Umma ta ce haka mana, wallahi kullum kuna raina, amma insha Allahu zaku ganni cikin kwana kinnan, taka nas za mu zo da Jabeer mu gaisheta.”

“Da kuwa kun kyauta wata ƙila ku goge laifin ku wajen Umma.”

Karima ta ɗan buge bayan Sajidah kafin ta ce.

“Ja’ira wataƙila ma ke ce ke ziga mana Umman ko?”

“A’a kawai dai gaskiya ce idan ta kama dole a faɗe ta.”

“Oho ga zancen nan ya fito, to ki dai bawa Umman haƙuri.”

“Ai zata ma haƙura tun da kin bani hakuri ni ma.”

“Ke da Allah zancen ya isa haka kin bi kin cika ta da surutu daga zuwanta, ke da bakya gajiya da zance.”

“Kai Aunty Sakinah ina wani surutu a nan?” 

“Kin ga Karima bar yarinyar nan ta so mu je daga ciki, idan ba haka ba ba zata barki ki huta ba.”

Sakinah ta kai ƙarshen maganar tana mai kamo hannun Karima, kai tsaye ɗakin Farida suka nufa domin ya ɗan fi dama-dama, sabida ko ina sun haɗe kayan, ɗakin Farida ne  kawai ya rage ba su haɗa kayan ba.

Karima Abdallah Ɗan Jinjiri

Shi ne cikakken sunanta, ita ɗin ta kasance ƙawa kuma Aminiya ga Sakinah, tare suka ta so komai na su tare, duk da cewar akwai tazara mai yawa tsakanin gidansu Karima da na su Sakinah, amma hakan bai hana su yin ƙawance na haƙiƙa ba, kwanciya bacci kawai ke iya raba su ko shi ma dan basu da yanda za su yi ne.

Tun daga primary har zuwa matakin Digree ɗin su tare su ka yi, kuma a ko wacce makaranta ajin su ɗaya wajen zamansu ɗaya, sabida Sakinah na da burin zama Barrister ya sanya Karima ta ajiye nata burin na zamtowa Likita ta zaɓi karantar Low akan ta rabu da Sakinah na ɗan lokaci ƙanƙani.

Duk da irin shaƙuwa da junan da suka yi tsayin shekaru, da kuma gujewa abin da zai yi sanadiyyar raba su, amma hakan bai yi yu ba domin sai da aure ya yi musabbbin rabuwarsu.

A Yobe inda suka je bautar ƙasa Jabeer ya ga Karima ya nuna yana sonta, itama bata wani ja lokaci ba ta amince kasancewarsa mutum kamili mai kirki da sanin ya kamata.

Bayan kammala bautar ƙasarsu da wata guda a ka fara batun auren Jabeer da Karima, duk da Karima ta so a ce miji ɗaya zasu aura har ta tuntuɓi Sakinah da batun kota gayawa Jabeer ya aure su duka, wannan magana ta ƙonawa Sakinah rai har sai da ta yi fushi, ganin hakan ya sanya Karima barin maganar duk da cewar a can ƙasan zuciyarta bata fidda ran wata rana ta yi wa Jabeer tayin auren Sakinah ba.

Wannan shi ne musabbabin rabuwar Sakinah da Karima amma duk da hakan zumunci da amincinnsu yana nan kamar kullum.

*****

Zama su ka yi gefan ɗan ƙaramin gadon Farida, Sakinah ta dubi Karima tana faɗin.

“Zauna nan na kawo miki ɗan abin taɓa wa.”

Karima ta yi gaggawar riƙon hannunta Sakinah kafin ta ce.

“Kinga bar wannan batun malama, anjima na ci koma mene, yanzu a ƙoshe na ke kinsan daga gida nan na nufo.”

Sakinah ta zauna gefan gadon itama kafin ta ce.

“To shi kenan, ya gida ya mai gida?”

“Lafiya ƙalau Sakinah sai kuma na ji wani mummunan labari?”

“To ya za’a a yi da abin da Allah Ya ƙaddara sai haƙuri.”

“Ke fa kina da matsala Sakinah, amma shi ne ko a waya ba ki kira kin gayamin ba ko?”

“A’a wallahi na kwan-biyu babu kuɗi a wayar ne, kuma nasan daman dole Jabeer zai gaya miki.”

“Hmm Ina fa, shi ma jiyan nan Kamal ya tura masa da hoton katin ɗaurin auren, shi ne ya ke nunamin yanzu ma ya ce min zai biya ta wajensa idan ya dawo daga office, amma gaskiya ban ji daɗin al’amarin ba ko ka ɗan, Kamal ya ban haushi sosai wallahi Sakinah, a yanda ya nuna miki so kafin auren ku da bayan auren ban yi zaton hakan da wur-wuri a gunsa ba.”

“Ban da abin ki Karima yawancin lokuta abin da baka zata ba ba ka yi tsammani ba shi ne ke faruwa.”

“Haka ne, amma wai baya sa miki kati ne a wayar? Na ji kince kin jima babu kuɗi a wayar.”

“A’a ni dai ban ce ba.”

Sakinah ta yi maganar tana murmushi.

“Kya ji da shi.”

Karima ta faɗa tana mai zuge zif ɗin jakarta ta fiddo da wayarta ƙirar Companyn inpinic, nan ta ke ta yi mata transfer na dubu biyu tana faɗin.

“Gashinan na tura miki dubu biyu ki yi maneji babu yawa.”

“Kai amma nagode wallahi, wayarki ta yi kyau sosai yaushe ki ka canja?”

“Satin nan na canja ta, ke fa duk laifinki ne Sakinah wai ba zaki lallaɓi Kamal ki fara aiki ba?”

“Karimah… Har yaushe bakinki zai gajiya da wannan maganar? Wallahi ni kaina Ina son aikin nan sabida ko ba komai zan dinga saukewa kaina wani nauyin, amma na rasa Kamal wanne irin mutum ne shi, duk yanda ki ka yi tunaninsa ya zarce tsammanin ki.”

“Gaskiya idan da kin haƙura da aiki yanzu ya zama dole ki yi aiki Sakinah, ko ba komai kya yi ƙoƙarin kankarowa kanki mutunci da daraja, kin kuwa san wacece zai aura?”

“Idan ma na sani mai sanin zai amfana min Karimah?”

“Dole ne fa kisan duk yanda za ki yi ya barki kiyi aikinki Malama, yanzu ko me zan faɗa miki ba lallai ki fahimci ne ba, amma da zaran kin fara aikin da kanki za ki bawa kanki amsar dalilin da yasa na da ge akan ki yi aikin.”

“Haka ne, to amma taya zai amince Karima?”

“Zan yi wa Jabeer magana sai ya tuntuɓe shi, kuma ni ma zan yi ƙoƙarin tausarsa ya amince, amma wai shi mene matsalarsa da ƙin aikin.”

Sakinah ta yi murmushi tana mai kallon Karima kafin ta bata amsa da faɗin.

“Ya ce baya so ne na fara aiki idona ya bude na fara jera ajinsa da nawa waje guda, yin aikina raini ne kawai zai janyo tsakanin mu a cewarsa.”

Karima dariya ta sanya har da kyakyatawa kafin ta girgiza kai tana faɗin.

“Kamal na Sakina Allah ya barku tare, al’amarinsa sai shi halinsa sai shi, babu mai iyawa da shi sai ke Sakinah, gaskiya kina haƙuri Allah ya baki ladan haƙurin, amma kinsan Allah ni dai bana tunanin zan iya jure halayen Kamal.”

“To ya za’a yi da abin da ya kasance rubutacce ne a wajen Allah?”

“Haka ne amma gaskiya shawarar da zan baki a yau ki ta shi tsaye tsayin daka, ki tsaya da ƙafauwanki tun wuri Sakinah ki yi wa tufkar hanci.”

“Wanne irin ta shi kuma zan yi Karima?”

Karima ta yi ‘yar gajeriyar dariya tana mai gyara zamanta sosai, kafin ta janye matafinta ta ajiye kan gadon ta dubi Sakinah ta fara magana da faɗin.

<< Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 5Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×