Skip to content

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa | Babi Na Goma

4
(1)

<< Previous

Kamar yanda Sakina ta zata hakan ce ta kasance, domin har suka yi bacci Kamal bai dawo ba.

A can wajen Dinner kuwa ba su suka tashi ba sai wajen sha-biyun dare, kai tsaye gidan Hajiya Shema’u suka raka amarya kafin daga baya ko wacce ta kama gabanta.

Abokan Ango sun tsaya sunyi siyan baki kamar yanda ake yi a al’adance tare da wasu Aminan Hajiya Shema’u su Hajiya Turai kenan, kafin daga baya suma su fashe su bar Ango da Amaryarsa, tare da yi musu fatan alkhairi.

Washe Gari

Kamal ne ya buɗe idonsa da ƙyar sabida yanda ya ji sunyi masa nauyi har wani irin sarawa ya ji tsakiyar kansa na yi, lokacin ƙarfe biyar da kusan mintuna arba’in, a hankali ya kai dubansa gefan hagu Hajiya Shema’u ce kwance ka shirɓan tana sharar baccinta hankali kwance, ziro ƙafafuwansa ya yi ƙasa da nufin sauka daga kan gadon.

A hankali ya miƙe ya nufi banɗaki yana faman jan ƙafafunsa da ƙyar yana layi tamkar wanda ya sha ƙwaya.

Bayan wasu mintuna ya fito jikinsa duk ruwa da alamun wanka ya yi da alwala, kai tsaye abin sallah ya nema ya shimfiɗa, kafin ya buɗe cikin kwaba ya ɗauko wata farar tattausar jallabiya ya sanya, tana ɗaya daga cikin kayan da Hajiya Shema’u ta siya masa masu ɗan karen kyau da tsada.

Juyawa ya yi ga Hajiya Shema’u yana kiran sunanta a hankali da nufin tashinta, da ƙyar ta buɗe idonta tana faɗin.

“Wai lafiya? Kake ta faman tashina haka.”

“Ki tashi ki yi sallah, gani na yi har gari zai waye.”

“Mtsww..! Dan Allah ka rabu da ni zuwa anjima na yi, na gaji wallahi bacci kawai na ke buƙata a yanzu.”

“Shi kenan, a tashi lafiya.”

Abin da ya ce kenan, kafin ya juya yana mai ta da kabbarar sallarsa, ba tare da ya damu da rashin tashin nata ba.

*****

Sakinah tun kiran sallar farko suka tashi bayan sun yi nafilfilunsu tare da yin sallar asuba Karima ta koma ta kwanta domin more baccin gajiya, amma hakan bai samu ba ga Sakinah, domin zama ta yi a wajen tana mai kaiwa Allah kukanta tare da neman daidaita zamansu da mijinta da kishiyarta, sai da gari ya yi haske sosai ta koma ta kwanta itama sabida yanda ta ji idanuwanta na mannewa tamkar an zuba mata superglue, ka sancewar duk a gajiyen suke babu wanda ya yi tunanin tashi ya haɗa abin karyawa kowa komawa ya yi ya more wa baccin gajiyarsa.

10 am

Hajiya Shema’u ce zaune gefen gado cikin wani haɗaɗɗan leshi maroon mai ratsin adon peanch colour sai fesa wani ƙayataccen ƙamshi ta ke, Kamal da ke tsaye gaban mudubi yana shiryawa cikin nasa gayun ya dubeta da faɗin.

“Anjima za muyi baƙi, Abokaina zasu zo cin girkin Amarya”.

Hajiya Shema’u ta yalwata fuskarta da yalwataccen murmushi kafin ta dubeshi ta ce.

“Da wurwuri haka? Kasan gajiyar hidimar biki bata sake ni ba, su bari har zuwa gobe mana.”

“Babu damuwa duk yanda kika ce hakan za’a yi Amarya ran gida.”

Kusan a tare suka yi dariya daidai sanda yake ɗora hularsa saman kansa, kafin Hajiya Shema’u ta cigaba da magana.

“Ni fa akwai maganar da nake son yi tun ba yanzu ba, al’amuran biki ne suka riƙe ni ba muyi zancen ba.”

Kamal ya dawo kusa da ita ya zauna tare da faɗin.

“Ina jinki faɗi dukkan maganarki.”

Hajiya Shema’u ta kai-kai-ce murya tare da ɗan gyara zama ta karyar da kai gefe kafin ta ce.

“Daman kan maganar Sakinah na ne.”

Ta katse maganar tana mai kallon fuskarsa domin karantar yanayinsa, abin da ta sanya cikin ma’adanar tunaninta shi ne kuwa ya bayyana a fuskar Kamal, domin baki ɗaya fara’ar da ya ke yi ta kau gefe, kallonta ya cigaba da yi ba tare da ya ce komai ba, hakan ne ya ba ta damar cigaba da maganar da ta faro.

“Na yi tunanin mene zai hana ka dawo da ita wancan ɓangaren kaga ko babu komai ka huta da zaryar gida biyu.”

Kamal shiru ya yi tsayin mintuna, kamar yanda itama ta yi shiru tana jiran ta ji mai zai ce, gajeriyar gyaran murya ya yi a hankali kafin ya ce.

“Kina ganin hakan babu takura a tattare da ke? Dan bana so ke da gidanki ta zo ta takura miki fa.”

Hajiya Shema’u ta ɗan dara kaɗan kafin ta ce.

“Wacce irin ta kura kuma? Abin da ba a kaina zata zauna ba, kawai kai na ke nemawa sauƙi dai.”

“Gaskiya kinyi tunani mai kyau, na gode sosai da ƙauna, yanzu zan fita zan biya gidan sai na faɗa mata ta shirya akwaso kaya ta dawo nan ɗin”.

“A’a wanne kwaso kaya kuma? Komai fa akwai su a ɗakunan, kawai kayan sawarta zata zo da su.”

“To babu damuwa, daman ai ba wasu kaya gareta ba duk sun tsufa, na ga dai auren nan da zan yi an taimaka an canja mata kayan ɗakin, amma ban da haka a ce kaya tun na auren mu haba, ai shiyasa na dage na ƙara auren ma, kinga yanzu ai sun canja mata, ni fa son samuna da ina da hali duk bayan wata biyu zuwa uku zan iya canja kayan ɗakunan ku fa.”

Hajiya Shema’u ta kwashe da dariya kafin ta ce.

“Auran naku shekara guda shi ne har kaya sun tsufa?”

“Ba zaki fahimta ba ne Hajiyata, ni dai zan fita may be na dawo da wuri, domin iya ban gajiya kawai zanje yiwa Abokaina na dawo, wataƙila ma na tawo miki da kishiyar taki tun da naga kin matsa ki ganta kusa da ke.”

“E na ji koma dai me zaka ce ka faɗa, ni dai ta dawo kusa da mu zamu fi jin dadi gaskiya.”

Kamal dariya ya sanya yana mai ficewa ba tare da ya kuma cewa da ita komai ba, itama bin bayansa ta yi da dariyar tana mai cije leɓanta na ƙasa, tare ɗan yin ƙayataccen murmushi mai ɗauke da ma’anoni daban-da-daban, wanda ita ka dai ta san abin da ta ke nufi da hakan.

Duk kansu zaune suke falon Hajiya suna hira Kamal ya yi sallama ƙofar falon bayansa Zayyad na biye da shi tare da Jabeer mijin Karima, shigowa suka yi kai tsaye yayin da su Karima suka basu guri guda suka zauna fuskokinsu na wanzar da murmushin jindaɗi.

Kai tsaye Hajiya suka gaisar kafin da ga bisani su Sakinah su gaishe da su, Jabeer ya dubi Karima bayan amsar gaisuwar yana faɗin.

“Da fatan kin gama shirinki domin tare zamu tafi.”

“Tun yanzu ai ka bari na wuni dai.”

Cewar Karima ta bashi amsa cike da zolaya, Jabeer ya jefeta da harara cikin zolaya shima yana mai cigaba da faɗin.

“Ko kuma na barki ku zauna tare har aba da ba.”

“Wallahi da ka kyauta kuwa.”

Sakinah ta bashi amsa, dariya suka sanya, kafin Zayyad ya ce.

“Amaryarmu ya gajiyar biki kuma, Allah ya sanya alkhairi ya ba da zaman lafiya, tun san da aka fara batun bikin ban samu zuwa ba, ni ɗin ne yanzu sai a hankali.”

Sakinah ta yi dariya kafin ta amsa masa da “Amin”

Farida ta karɓe zancen da faɗin.

“Ya Zayyad ban da zolaya dai Amarya na can kana mai da min Yayata baya, ita ai yanzu ta hau matakin manya Uwargida gida ce guda.”

Ta ƙare maganar tana kallon Kamal tare da murguɗa masa baki a fakaice.

“To ni dai bakina ya riga ya saba Amaryarmu ce har gobe babu wani Uwargida.”

Nan ma dariya suka yi dukan su kafin Kamal ya miƙa tsaye yana mai duban Sakinah da faɗin.

“Ki same ni ɗaki.”

Bai jira jin amsarta ba ya fi ce daga falon zuwa cikin nasu falon.

Ko mintuna biyu bai yi da fita ba Sakinah ta bi bayansa ta barsu nan zaune suka hira cikin nishadi.

Da sallama ta sanya kai cikin falon yana zaune kan ɗaya daga cikin jerin kujerun falon mai cin mutum biyu, kusa da shi ta nemi guri ta zauna kanta a ƙasa take faɗin.

“Gani Allah ya sa dai lafiya?”

Sai da ya ja gwaron numfashi kafin ya ɗan keɓe bakinsa yana faɗin.

“Daman batu ne na zo da shi idan kinga ya yi miki to dan babu takura, za ki koma can gidan Hajiya Shema’u da zama, ma’ana zan haɗe ku waje guda idan kin ga za ki iya bina amma.”

Sakinah ta yi shiru tsayin wani lokaci tana nazarin maganarsa kafin ta ce.

“Duk yanda ka ce bani da ja akai, domin kai miji kake a gare ni kai ke da ikon zaɓamin duk inda ka ga zaka iya ajiye ni, amma wani hanzari ba gudu ba Hajiya tasan da maganar?”

Kamal ya kalleta wani sheƙeƙe kafin ya ce.

“Daman nasan ba zaki ƙi ba, ko banza za ki gidan hutu ai, batun Hajiya kuma ai ba zata hanaki bi na ba idan kin so hakan.”

“Haka ne amma yana da kyau ka sanar mata tukunna.”

Kamal ya sake dubanta a karo na biyu kafin ya ce.

“Ka da fa ki dame ni domin sanar da Hajiya ba huruminki ba ne, kamar yanda ba ki isa ki sani abin da ban yi niya ba kinji ko, ni fa na tsani wannan nuna isa da gadarar da kike nunamin Sakinah, kinsan halina idan an faɗi magana sau ɗaya kin san na ji, bana son a sake maimaita ta biyu kin fi kowa sanin hakan.”

“Allah ya baka hakuri ni abin da naga ya da ce na faɗa ba wani abin ba.”

Kamal dogon tsaki ya ja kafin ya miƙe ya fice daga ɗakin cikin fushi ya koma falon Hajiyar ya nemi guri ya zauna tsayin mintuna yana sauraron hirarsu kafin daga baya ya dubi Hajiya da faɗin.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×