Skip to content
Part 1 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

بسم الله الرحمن الرحيم.

Alhamdulillah dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah s.w.a wanda ya bani ikon fara rubuta wanan labarin, ina kuma roƙon Allah yasa duk abin da zan rubuta ya zama alkhairi ne agaremu baki ɗaya.

Sai dai fa labarin awanan karon yasha ban-ban da sauran labarin dana saba kawo muku, wanan tafe yake da ababan ban haushi da ban tausayi. Kalma ɗaya tak ke tafiya acikin labarin, wanda take daƙusar da ko wani karsashi da ƙumajin daƙusar da jarumar labarin, JINI YA TSAGA… ! Haka kowa ke faɗa mata, haka kowa ke dannarta acikin tafiyar.

Sadaukarwa ga Ramlat Abdulrahman Manga (Dambu)

Babi Na Daya

BIRNIN KEBBI
JEGA L.G.

Gidan Alhaji Kamaludden

Gida ne babba wanda yake ɗauke da matan aure guda uku, biyu daga cikin su suna da yara aƙallah zasu kai tara, sai ɗayar da take sabuwar amarya atsakanin su, dan aƙalla aurenta da mai gidan bazai haura wata biyu ba.

Durƙushe take agaban murhu tana faman soya kaji, sauran yaran gidan sai kai-kawo suke awajan ta.

Gefe kuma sauran matan gidan su biyu ne suke hira atsakanin su, wanda bata wuce ta abin daya shafi rayuwar yau da kullum.
Akwai zaman lafiya sosai ashimfiɗe agidan, kasancewar maigidan ya tsaya tsayin daka amatsayin sa na namijin duniya, wanda bai ragesu da komi ba na rayuwa.

Fitowa tayi daga ɗakin da yake mallakin ta, tun bayan mutuwar auren ta data dawo, aka bata shi amatsayin ɗakinta da zatayi zawarci. Kyakkyawar mace mai ɗauke da farar fata, da faffaɗar fuska, wadda ko yaushe take sake da fara’a, hancin ta amiƙe yake ziyat har yana ranƙwafawa, sai bakinta ɗan ƙarami mai ɗauke da jerararrun haƙora farare, idanuwanta basu da girma sosai, asalima ko yaushe suna maƙale alungu, idan baka sani ba sai ka ɗauka harara take aika maka da shi, wanda hakan ɗabi’a ce agareta. Shekarunta bazasu haura 30 ba aduniya.

Ƙarasawa tayi kusa da mata biyun da suke zaune, wanda tana zama tajiyo sautin kukan ɗiyarta itama ta tashi “Abdul maza ɗauko min Bunayya ta tashi abarci.” ta faɗama wani yaro da yake ta faman izawa Amaryar wuta ita kuma tana tsame kajin da suka soyu daga cikin kasko.
Tashi yayi da sauri sanin halin Anty Hafsa da yayi, yanzu tana iya kai masa duka ko bugu idan baiyi hanzari ba.

Juyawa tayi ta kalli matan, ta kwaɓe fuska “Wallahi ku kam kun rako mata duniya, duk da kasancewarku matan mahaifina amma hakan bazai hanani faɗa muku gaskiya ba. Tun da nazo gidan nan ranar girkin Asma’u amarya kaɗai ake cin cima mai daɗi agidan nan. Haka kuma ranar da take girki ne kawai ake samun damar yin dumu-dumu da kaji ayi wadaƙa da su kamar ba da kuɗi ake siyan su ba, amma ku kun miƙe ƙafa cikin mutuwar zuciya da karaya kuna jira agama asan muku.”

Kallonta sukayi cikin mamaki da alhinin maganar ta “Mi kike son faɗa mana Hafsa? Ina duk ɗaya ne ko muyi ko ita tayi, kason data samu shi zamu samu muma. Asalima mu muna finta da kaso mai yawa kasancewar muke da yara agidan nan.” Wadda take amatsayin uwargida ta faɗa tana kai kallonta ga ta kusa da ita.

“Ƙwarai kuwa Yaya Abu ni banga abin nuna jin haushi ko kuma takaici acikin wanan ba, abin wahala da sa aiki.” Rabi’atu ta faɗa tana ƙarasa maganar da murmushi.

Harara ta aika musu da ita, kafin tayi magana Abdul ya miƙo mata da Bunayya ya koma wajan Asma’u yana fifita mata wuta.

“Mtsss! Ya tabbata kun rako mata duniya wallahi, to ko kunyi haƙuri saboda zuciyarku ta gama mutuwa da yadda akan ɗa namiji ni bazanyi shuru na zura ido ina ganin Mahaifina na aikata haramun ba, bazan bari gefen mahaifina ɗaya ya rinjayi ɗaya ba, idan har babu wanda zai bashi shawara yaji ya gyara, ai akwai Hukuma ita kuma doka bata kowa bace bata kuma ƙyale kowa ba, ni nan zan bada sheda na kuma tsaya muku akan rashin adalcin da Mahaifina yakeyi muku.”

Baki buɗe suke kallon ta zuciyar su cike da mamaki da tarar rabin abin da take faɗa, gaza shuru da haƙuri yaya Abu tayi “Kin san mi kike faɗa Hafsa? Kanki ƙalau yake kuwa anya Hafsa?”

Tashi tayi tsaye tana aika musu da uwar harara “Kaina ƙalau yake Yaya Abu, haka kuma rass nake, duk da mahaifiyata bata gidan nan ake rashin adalci to bazan bari na zuba ido aci mutunci ku amatsayinku na mata ba, wallahi sai yanzu nake takaici da bana nan Mahaifina ya saki mahaifiyata, da tun alokacin zamu kwashi ƴan kallo da shi, amma yanzu ma bata sauya ba, lokaci bai ƙure min ba, zan tsaya na yaƙi rashin adalci.”

Da ƙarfi take maganar wanda ya janyo hankulan mutane da yawa kanta, Asma’u kuma banda hawaye babu abin da takeyi. Allah ya sani tun bayan jin halayyar Hafsa zuciyarta taci gaba da tsoro da fargabar zaman su awaje ɗaya, sai gashi tun kafin aje ko ina ta fara nuna tsana da kyara agare ta, shi kansa Mahaifin nata tsoron sharrin ta yake.
Alokuta masu yawa yakan danni matan nasa akan suyi haƙuri da zama da Hafsa, bashi da Yadda zaiyi da ita saboda Jininsa ce ita, haka dolensa ce.

To amma gashi ko wata guda batayi da zuwa ba zata zubarwa da Mahaifin nasu mutunci, za kuma ta kafa mugun tarihi acikin ahalin su.

Hijabinta ta zara ta saka tana goya Bunayya abayan ta, “Ni na tafi ofishin ƴan sanda nakai ƙara.”
Da fari wasa suka ɗauki abin, amma ganin tayi waje yasa suka ɗunguma abaya suka bita. Ƙafafuwan su ko takalma babu suna bata haƙuri da kuma dakatar da ita akan ta tsaya, amma ko sauraran su batayi ba, burinta kawai ta kai ga inda tasa gaba.

Funcikota Yaya Abu tayi tana aika mata da tsawa “Ke wata irin yarinya ce ne Hafsa? Wata baƙar zuciya da mugun hali kike da shi? Mahaifinki kike iƙirarin zakiyi ƙara? Shi kike so ki tonawa asiri bayan Allah ya lulluɓe masa asiri, ya kuma toshe ko wata ɓaraka da zata nuna gazawa ko aibatawa agare shi awajan waninsa.”

Fuzge Hijabin ta tayi daga ruƙon da ta mata, sanan ta kalleta kallon tsaf da ƙananun idonta da ke nuna tijaranci acikin su “So nake duniya ta sheda mugwayen halayyar sa da yake ɓoyeta cikin fuskar ƙarya, so nake mutane su sheda da’awata akan kowani namiji ba adali bane koda mahaifina ne, so nake ya tsira da fuskar zahiri wadda zata zama mashimfiɗi na gyaruwar goben sa.”

Dafe kai Rabi’atu tayi “Ya Allah!” ta faɗa tana daddana wayar dake hannun ta “Akwai matsala Alhaji, kazo yanzun nan ga Hafsa nan zatayi ƙaran ka ofishin ƴan sanda.” abin data faɗa kenan ta datse ƙiran.
Sanan ta kalli wajan tuni ƙofar gidan nasu ya cika, kasancewar hanya ce ta zirga-zirgar mutane, da kuma zamowar su abakin titi.

“Ban taɓa tsammanin halinki ya shallake tunanina ba Hafsa, na ɗauka abin da ake faɗa akanki ba gaskiya bane, kalli yanda kika tara mutane kika cika mana waje, bakya gudun abin kunya? Bakya tsoron abin da zai iya biyo baya idan mutane suka farga da kasassaɓar da kike shirin yima kanki da sauran danginki.”

Baki ta ciza da laɓɓanta sanan ta murza goshin ta da hannunta, ido ta fara jujjuyawa tana kallon mutanen da suke wara nasu idon dan su bashi abinci.
Murmushi tayi ta girgiza kai “Banyi wanan tunanin ba yaya Abu, abin da kawai na tuna shine lambar karramawa da kurantawa da zan samu abakunan mutanen da suka sheda gaskiyar dake tafiya atare da ni da ahalina.”
Kafin ta kai ga wata maganar taji an finciko ta da ƙarfi, juyawar da zatayi taga Babban yayansu ne Ado sai kuma mahaifinsu Kamaludden da yake harɗe da hannunsa aƙirjin sa, kallonta kawai yake yana jinjina kai, babu wanda yasan yaushe suka zo wajan. Sai bayyanarsu da aka gani.

Tun da Rabi’atu ta masa waya ya fito asukwane alokacin suna tattaunawa akan harkar kasuwancin sa shi da Ado, ganin yanda ya taso yasa shima ya biyoshi da sauri, ko ba’a faɗa masaba yasan matsalar ba zata wuce ta gida ba. Gashi ba nisa ne da su da kasuwa ba, amma abin mamaki sai suka tsinkayi maganar da Hafsa take wanda ta tsayawa Alh. Kamaludden arai, ta hanashi aikata komi.

Hakan ya fusata Ado ya fincikota ya kwaɗa mata mari har sau biyu “Kinyi babban kuskure, jahilcin dake kanki ya gaza wajan baki damar da zaki tonawa mahaifin mu asiri bayan Allah ya lulluɓa masa asirin sa. Ke kike da abin kunya da abin da za’a nunaki, idan har kika zauna kika lissafo tarin munanan halayyar ki dake koroki daga gidan mazajan da kike aura suna sakoki a ƴan shekarun ki aduniya. Kije masifar ki ta ƙare akanki, amma kada ki kuskura ki saka Mahaifinmu acikin ta.” da tsawa yake mata maganar yana ji kamar ya lakaɗa mata dukan tsiya.

Ƙuncinta ta riƙe tana yalwata murmushi akan fuskar ta “Na nawa kuma tonuwar Asiri Yaya Ado! Kalli nan” ta shiga nuna masa mutanen da ke wajan “Duka sunji abin da ya faru yau, kuma na tabbata zasu kai gaba, ko ban kai ƙaransa ba labarinsa zai kewaya garin Jega amatsayin ɗiyarsa ta ƙalubalance shi akan rashin adalci ga matan sa. Ko ahaka Alhamdulillahi buƙatata ta biya.”

Hannu ya ɗaga zai ƙara marinta yaji an riƙe hannun “Ƙyaleta Ado karka ƙara dukan ta. Batta taci riba, kije Hafsa kinci riba kinji, amma kafin nan ki tattara komi da yake naki ki bar min gida na, karna ƙara ganin ƙafarki acikin gida na, kada kuma ki sake amfani da sunana amatsayin Uba agareki, daga yanzu bani da ƴa mai irin sunanki balle kamarki. Allah ya fiddama kowa hakkin sa atsakanina da ke.”
Yana gama faɗar haka ya shige cikin gidan yana share hawaye akan fuskar sa. ‘wata irin rayuwa ce wanan ɗiyar ciki nah’…

Wai! Wai!! Anya kuwa Hafsa zata ga da kyau, to dai ga mafarin tafiya cikin shimfiɗar farko a cikin labarin Jini Ya Tsaga, da zai iyu da an toshe hanyar. Lolz
Maza ku adana kimantawar ku ni kuma zan ajiye muku kalmar GIRMAMAWATA acikin tafiyar.

UmNass

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Jini Ya Tsaga 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×