Kamar da aka kwaɗa masa guduma a kansa haka ya ji maganar Hafsat ta dira kunnuwansa ta kuma ratsa ƙofofin da ke tsakiyar kansa, ta fara amsa amo a cikin kan nasa.
"A zubar da cikin kika ce Nahna? Ko kuma dai ban ji daidai ha ne?" Ya tattaro duk wani kuzarinsa ya jefa maganar a gareta. Ina jin yawun bakinsa ya masa kauri, wani tashin hankali na kutsowa cikin rayuwarsa suka masa iyaka da farin cikin da ya samu a mintina ashirin ɗin da suka gifta.
"Haka na ce Abdulmannan!" Ya ji sautin muryarta na dawo da shi. . .