Skip to content
Part 12 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Kamar da aka kwaɗa masa guduma a kansa haka ya ji maganar Hafsat ta dira kunnuwansa ta kuma ratsa ƙofofin da ke tsakiyar kansa, ta fara amsa amo a cikin kan nasa.

“A zubar da cikin kika ce Nahna? Ko kuma dai ban ji daidai ha ne?” Ya tattaro duk wani kuzarinsa ya jefa maganar a gareta. Ina jin yawun bakinsa ya masa kauri, wani tashin hankali na kutsowa cikin rayuwarsa suka masa iyaka da farin cikin da ya samu a mintina ashirin ɗin da suka gifta.

“Haka na ce Abdulmannan!” Ya ji sautin muryarta na dawo da shi cikin nutsuwarsa.

Murmushi ya yi yana kallonta “Wasa kike amma ko? Wannan ba lokacin irin wasan nan bane Nahna.”

“Da gaske nake Abdul Mannan. Tun daga zuciyata wannan maganar take fitowa. Me zai sa na ma wasa a irin wannan lokacin da nake kokawa tsakanin rai da rayuwa.” Ta bashi amsa tana yamutsa fuskarta da ɗora ƙananun idanuwanta  kansa.

Kansa ya shiga girgizawa kamar zai cireshi daga wuyan sa “Wannan yasasshen zance ne. Wannan ruɗaɗɗen tunani ne, Nahna! Ni Abdul-Mannan Ishaƙ ne zan zubar da ciki? Wannan ko a mafarkina ban taɓa ganinsa ba, Nahna.” Ya yi maganar da muryarsa mai rawa.

Ita kaɗai take ganin tashin hankalin da yake ciki, ruɗewar da yayi kaɗai ya isa ya tabbatar mata da cewar ya zauce daga tunaninsa.

Laɓɓan bakinta ta ciza, tana sosa girarta guda ɗaya “Zaɓi biyu ai na baka Sayyadi. Tun da ba zaka iya yarda a zubar da cikin ba sai ka biya kuɗin rainonsa da zan yi a cikina.”

Runannun idanuwansa ya ɗago yana ɗora su akan kyakkyawar fuskarta, yana hango yaƙadarin murmushin muguntar da take jifansa da shi.

Hannunsa ya ɗora a kan kafaɗunta ya fara girgizata a hankali “Dan Allah, Nahna ki dawo hayyacinki. Wannan ba Nahna ta ba ce, ba haka kike ba. Karki ci min cuwo mai zurfi a zuciyata. Dan Allah ki dawo hayyacinki Nahna!”

Daga yanayin yadda yake magana kaɗai ta fahimci Sayyadi ya zare ɗin.

Hannunta ta ɗora a kan nasa tana sauƙe shi daga kafaɗunta  “Hafsat Kamaludden Muhammad nake Sayyadi. Duk abin da na faɗa kuskurewa ba ne da kuma ruɗewa. Tun da har ka matsu da son abin da ke cikin cikina ashe kuwa zaka iya kashe komai a kansa. Akasin hakan kuma zan iya yin komai. Idan na ce komai ina nufin komai Abdul-Mannan Ishaƙ.”

Ta yi maganar tana kafe shi da idanuwanta, wadda hakan ya sa shi miƙewa yana girgiza kansa, bai san wata ƙaddara ba ce mai girma ta ke ɗawainiya da shi ba, bai san wane abu ne ya zama kuskure a gare shi ba da har ƙaddara ta mallaka masa mata irin Hafsa.

“Kuɗi kike so, Nahna?” Ya faɗi maganar a kan maƙoshinsa, yana jin kamar maganar na keto wani ciwo mai zurfi a wuyansa tana barinsa da raɗaɗinsa.

“Kuɗin rainon ɗanka ba.” Ta bashi amsar tana jingina da filon da ke ɗakin.

“Nawa kike buƙata?” Ya jefa maganar har a lokacin yana jin ɗacin abin da raɗaɗinsa na ƙin barinsa.

Shiru ta yi kamar mai tunani wadda hakan ke tasirantuwa da jin ɗaci a maƙoshinsa. Ya fahimci kalar matar da ƙaddara ta bashi, dan haka ba zai iya ci gaba da ɓata lokacinsa a wajenta ba, yana buƙatar keɓantaccen wajen da zai kokawa rayuwarsa.

Littafin banki ya zaro da biro ya fara ributu “Miliyan ɗaya nake buƙata.” Tsayawa ya yi daga rubutun da yake yana kallonta.

Ina zai samu miliyan ɗaya? Duka abin da ke cikin asusun bankinsa bai wuce dubu ɗari uku ba. Domin kuɗinsa ba na tarawa ba ne, yana samu yana bayarwa yana hidimar gida da kuma ta su Anna.

Kansa ya girgiza wani ruwa na taruwa a cikin idanuwansa “Ba ni da wannan kuɗin Nahna!” Ya yi maganar da murya mai rauni, yana jin yanzu kam ya zo iyaka.

Ajiye mata littafin ya yi a kusa da ita  “Ni ba mai arziƙin da yake libge kuɗi yana kasafinsu ba ne, Nahna. Asalima duk wasu abubuwa da suka shafi rayuwata ta yau da gobe kin sani.

Bani da adadin abin da kike buƙata. Zan iya baki komai da kike buƙata na farin ciki da jin daɗi, fiye da yadda zan bawa kaina. Amma ba zan iya baki tsabar kuɗaɗe irin wannan ba Nahna.

Allah ya sani ina son haihuwa. Ina son abin da zan samu a tare da ke, sai dai hakan ba zai sa na shiga dawa ba. Hakan ba zai sa na tilastawa rayuwarki akan dole ba. Yara amana ne da Allah ya ke bamu, haka kuma kyauta ce babba wadda babu wani mahaluƙi a duniya da zai iya bamu ita, da yawa a cikin mutane suna bazuwa da fantsama dan su sameta. Amma ba a gadar hakan a gare su ba, sai hakan ya zama abin nema a garesu.

Ko turawa da suke da aƙida ta kafirci a zuciyoyinsu basa tilastawa mazajensu da biyan kuɗaɗen rainon yaronsu, da kansu suke jin ya dace su haihu. Da kansu suke murna da sa ran lokacin haihuwarsu ne ya yi.”

Ajiye mata check ɗin ya yi yana murza hannunta “Dubu ɗari uku ne ya rage kawai a asusun bankina. Idan har ya miki kina iya ɗaukan su duka.”

Daga haka ya juya yana barin ɗakin, yana jin idanuwanta na yawatawa a jikinsa.

Shuru ta yi tana tariyo maganarsa tana ajiyeta a kan kowanne mizani na tunaninta, tana ƙiyasta adadin rainin hankalin da AbdulMannan ya mata.

_’Wato turawa manyan kafirai ma suna ra’ayin haihuwa da kansu?’_

Idan har ta fahimceta nata kaidin yana so ya ce ya zarta na masu jajayen kunnuwa kenan.

Ɗaukan takardar ta yi tana jujjuyata a lokacin kuma Anna suka shigo ita da Nabila da Aisha.

Da saurinsu suka ƙaraso kusa da ita suna jero mata sannu.

Anna da kanta ta zuba mata abin ci a flet take bata, loma biyu ta yi ta fara jin cikinta na hautsinewa yana juyawa, kafin su ankara ta tashi da mugun sauri ta shige toilet ta fara kela amai, tana jin kamar zata zubar da ƴaƴan hanjin cikinta.

Tun tana yi da ƙarfinta har abin da ke cikinta ya ƙare, ƙarfinta ya raunta, Anna ce ta taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta tallafeta suka fito, sai jero mata sannu ta ke kamar zata mayar da ita cikinta dan tausayi.

“Nabila, kira likitan da ya dubata.” Anna ta faɗa tana kwantar da ita, wadda kafin ta rufe bakinta Nabila har ta tashi ta tafi da sassarfarta.

Basu jima ba sai gata ita da likitan. “Ta farka kenan?” Dakta Mu’az ya faɗa yana dudduba ta.

“Eh Likita, amma daga cin abinci sai Amai.”

“Sai a hankali dama ai yanzu Anna. Zata samu sauƙi in sha Allah nan da wasu lokutan, da zarar cikin ya yi ƙwari.”

Ya yi maganar yana haɗa allura bayan ya mayar mata da jonin ruwan jikinta.

‘Sai ma ciki ya yi ƙwari zan samu sauƙi? Tabbas wannan da sake.’ Hafsa ta faɗa tana lumshe idanuwanta tana jin haushin mutanen na ratsa ƙofofin jikinta.

******

Zamanta a asibiti ta ga gata da ƙauna daga Ƴan uwanta da kuma ɗangin mijinta, kowa tattalinta yake yana kawo mata abin da suke ganin zata so.

Bakunansu ɗauke suke da soyayya da ƙaunarta, a ranta ta ke jin inama dai wannan ƙaunar tabbataciya ce daga garesu, sai dai ta san bata samu ƙaunar sai da ta samu abin da ke cikin cikinta.

Gefen Sayyadi ba a magana, ko yaushe zai shigo zai shigo mata da ababen marmari ne da kuma gasasshen nama, daga kan hanta zuwa nau’ikana naman da ake gasawa.

Duk da cewa bata son komai, bata jin ƙaunar komai, amma zaman Anna a tare da ita da tattalin da take nunawa a kanta yakan tilasta mata cin su ko babu yawa.

Adda Halima takanas ta yi tattaki tun daga jega ta zo ta dubata. Tana iya ganin farin ciki lulluɓai a zuciyarta, har zuwa lokacin da mutanen ɗakin suka fice ya rage sai su biyu.

Hannunta ta kamo hannayen Hafsa duka biyun ta sanya a cikin nata, tana kallon cikin idanuwanta kamar yadda itama Hafsa ke kallon Adda Halima tana son jin sabuwar farsabar da zata zo mata da ita.

“Baki ba zai iya faɗar farin cikin da kika sa ahalinmu a yanzu ba. Kamar yada kalma ta yi ƙaranci ta fallatsar da tarin alkhairan da kika shimfiɗa a cikin rayuwar ahalinmu.

Alhaji Malam da kansa bakinsa ya gaza ɓoye farin cikin da ya ke ciki, duk a silar wannan abin da ke cikinki. 

Yanzu kowa ya yarda da cewar kin sauya, kin kuma samu nutsuwa ga Abdul Mannan. Sai dai ni na kasa jin hakan daga zuciyata.

Asalima tana ƙiyasta min abubuwa da yawa a kan faruwa wannan abin, dan Allah Hafsa kada ki cutar da waɗanda suka yarda da ke!” Ta gama maganar tana matse hannunta duka biyu.

Idanuwanta ta lumshe tana sake buɗesu da ɗan rage su suka ƙara shigewa ciki. Tana ɗora kallonta ga Adda Halima da nazartar ta.

Yayin da ta ke cike da mamaki da dagiyar bin diddigin Adda Haliman a kanta, koda ta lulluɓai idanuwan mutane a kanta, bata iya rufe idanuwan Adda Haliman da fahimtar zahirinta.

“Kamar mun gama wannan maganar tun a waccan lokacin da kuka zo? Kamar kin kasa yarda da abin da na faɗa miki a waccan ranar? Na ɗauka abin da ke tare da ni zai siye yardarki a kaina har ki ji gamsuwa da alfaharin amsar abin da kowa yake son ganina da shi.” Hafsa ta yi magana tana ƙara kanne ƙananun idonta, da turo ƙaramin bakinta.

Sai da ta ja fasali ta furzar da iska a bakinta sannan ta sake kallon Adda Haliman.  “Duk da wannan abin da kuma sadaukarwa da na yi amma kin kasa yarda cewar na sauya ɗin.”

Murmushi Adda Halima ta yi tana murza yatsun Hafsat da suka sha lalle “Ni ce mafi kusanci da ke, na sanki fiye da yadda nasan kaina, Hafsa. Na kuma yarda da duk wani alwashin da kika ɗauka, bakya barin abu har sai kin kai ƙarshensa.

Sai dai wannan ban san ya kika tsara shi ba, bana so ki gama yin rawar da babu liƙi a cikinta.”

Dariya mai sauti ta yi tana lumshe idanuwanta “Dama haka uwa take ji? Haka ake rainon ciki Adda Halima? Amma duk da wannan wahalar maza suke nuna ƙarfin iko a kan yaran?” Ta yi maganar tana zame hannunta daga ruƙon Adda Halima, tana ɗora shi akan shafaffen cikinta.

“Tun bayan da aka sanar da ni ina ɗauke da shi, sai naji kamar an sanar dani tarin wahalhalun da zan sha a tare da shi ne. Ko da sau ɗaya ban ci wani abu ya zauna min a ciki ba, ba tare da ya dawo ba. Lallai na jinjinawa kowacce Uwa a duniya.” Ta gama maganar tana lumshe idonta, tana jin wani abu na ɗarsuwa a ƙasan ranta, wani abu mai girma da bata san ko menene shi ba, ya yin da take tasirantuwa da ƙaunar abin da ke cikin cikinta.

“Tukunna ma indai rainon cikine. Shi yasa tun a yanzu nake son ki yarda da kowanne abu da ƙaddara ta mallaka miki, ki kuma karɓe shi hannu biyu.”

“Na riga da na karɓe shi ai Adda Halima. Na kuma samu tabarrakin zama tare da shi. Shin wannan bai isa ya gamsar da ke cewar na karɓi Sayyadi a matsayin ƙaddarata ba?”

Dariya Adda Halima ta yi wadda har kumatunta guda ɗaya ya lotsa, jerarrun haƙoranta suka fito.

“Allah ya tabbatar da hakan.” Ta faɗa tana shafa kan Hafsa, a lokacin da aka turo ƙofar aka shigo da sallama mai ƙarajin data cika wajen.

Hakan yasa suka mayar da hankalinsu zuwa wajen mai sallama, duk da sun san Abdul Mannan ne ke da muryar.

Gyara zama Hafsa ta yi tana kallonsa da lumshe idanuwanta, ba ta da hujja ko ɗaya ta ƙin mutumin kamar yadda bata da gamsasshen dalili guda da zata so shi.

Tana yaba masa, tana kuma girmama shi da jin tausayin yadda yake hidimtawa duk wani al’amari da ya kasance nata ne.

“Barka da zuwa Malam. Baka gajiya da hidima, kullum hannunka ɗauke da abu, gashi ba wani ci take sosai ba.” Adda Halima ta faɗa tana amsar ledodin hannun nasa.

“Idan bata ci wani ba na tabbata zata ci wani, Adda.” Ya bata amsar da murmushi a fuskarsa.

Ita fa nauyin sunan da yake kiranta da shi take ji, amma bata da ikon hana shi kiranta da shi, duk da cewar ko ta hanashin ma ba zai hanu ba.

“Kana dai ƙara sangarta ta ne a taƙaice.”

“Ina ƙoƙarin kula da lafiyarta dai Adda.” Ya tari numfashinta yana yalwata fuskarsa da murmushi.

“Barka da zuwa Sayyadi.” Hafsa ta faɗa tana kafe shi da idanuwanta.

Idanuwansa ya buɗe ya ƙara lumshe su sannan ya ɗora a kanta “Barka dai Ummu. Ya ƙarfin jikin naki?” Ya faɗa yana ɗora hannunsa a wuyanta.

Hakan yasa Adda Halima miƙewa tana bar musu ɗakin.

“Na gaji da zama a asibitin nan Sayyadi. Jikina har ya fara ƙoƙarin son kama warin asibitin nan.” Ta faɗa tana yamutsa fuskarsa.

“Ki ƙara haƙuri jikinki ya yi ƙwari sai mu karɓi sallama.”

Kanta ta girgiza “Ciwona ba mai yankewa ba ne a ƙaramin lokaci Sayyadi. Laulayin ciki ba kaina farau ba, bana jin zan zama ƙarau. Nifa na ma gaji da turururwar dangin da suke ta zirga zirgar dubani, abin na gundurata da yawa.” Ta kai ƙarshen maganar tana yamutsa kitson kanta, da take jin ya tsufa tana buƙatar a sabunta shi.

“Baki ɗauki cekin da na baki ba?” Ya jefa mata maganar yana kallonta.

“Ta ina zan ɗauka? Ka taro min dangi, kana ta yayata ciwo na kamar dai ni kaɗai ce macen da ta fara ciki da laulayi.”

Bakinsa ya rufe yana ƙoƙarin riƙe dariyarsa, shifa yanzu faɗan Hafsa baya damunsa, asalima komai ta yi yana jin ƙaunarta na ƙaruwa a zuciyarsa, bai sani ba ko ya zurma da yawa a sonta shi yasa baya iya ganin laifinta.

“Kana ta kallona ka ƙi magana Sayyadi, nifa na gaji da zaman asibitin nan.” Ta yi magana da murya mai amo.

“Shikenan bari na je na samu Dakta Mu’az sai na masa maganar sallamar.”

“Ya dai fi kam. Dan ni na gaji da zaryar masu dubiya, wasu ma neman ƙwaƙƙwafi ne zai kawo su da neman suna.”

Shi dai ficewa ya yi yana sauƙe ajiyar zuciya, da kuma fatan nema mata shiriya, dan Hafsa lamarinta dole ya fara haɗa mata da addu’o’in tsari, ita bata da gwani ko kaɗan.

Bayan fitarsa ba daɗewa sai gashi sun dawo shi da Dakta Mu’az, mutum mai barkwanci da yawan fara’a “Madam aka ce kina buƙatar sallama. Bayan kuma jikin naki bai gama warwarewa ba.” Dakta Mu’az ya faɗa da murmushi a kan fuskarsa.

“Sai ku bani magani na je gida ina sha Dakta. Amma yanzu na gaji da zaman asibitin nan, mako biyu na wasa ba, ƴan uwa na nesa da na kusa duk sun zo dubiya.” Ta yi maganar tana murmushi.

“Ba zaki ƙara mana wani mako biyun ba?” Ya jefa tambayar yana murmushi da kuma yin rubuce-rubuce a file ɗinta.

“Wannan ma dan ba yadda zan iya ne yasa na jure su. Amma idan da abin da na ƙi jini a rayuwata bai wuce zaman yini guda a asibiti ba.”

“Kamawa dama ta ke Madam. Da har na fara tunanin zamu ɗauke ki ko aikin raba kati ne ga marasa lafiya.” Ya gama maganar yana miƙa mata takarda, ganin takardar ya sa ta gagara yin maganar da take shirin yi.

Wadda dama Abdul Mannan ke ta jero addu’a da fatan kada Hafsa ta basu ƙafa.

“Dama yau ne zamu sallame ki, da fatan zan sake dawowa nan da wata guda dan duba lafiyarki da ta baby.”

“In sha Allah.” Ta faɗa tana miƙawa Sayyadi takardar.

Karɓa ya yi yana yiwa Dakta Mu’az godiya da masa rakiya, bayan sun fita ya sheda su Anna da Adda Halima cewar an sallame su.

Shiga ɗakin suka yi suka tattara kayansu suka fito, yana tambayarsu ina zai kai su.

“Ka wuce da ita gidanku mana.” Adda Halima ta bashi amsa.

“Na ɗauka za mu je gidana ta ƙara hutawa.” Anna ta faɗa cike da kulawa, wadda yasa Adda haliman saurin girgiza kanta, duk da nauyin Anna ɗin da take ji.

“Anna ai ta warke. Zamanta w ɗakin nata zai fi sauƙi a kan a wajenku, dan hankalin mutane zai karkata kanta a fara tunanin ko bata warke ba.

Tun da ga Khadija da Nabila nan sai suna zuwa suna tayata aiki har zuwa lokacin da zata yi ƙwari.”

“Eh kuma haka ne Halima. Allah ya bata lafiya ya raba su lafiya dai.” Anna ta faɗa cike da tausayi.

Hakan yasa Hafsa jinginar da kanta jikin kujera tana lumshe idanuwanta, badan ta yi barci ba, a’a sai dan tana neman warware matsayarta ne da kuma sabuwar rayuwar da ta kutse kanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 11Jini Ya Tsaga13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×