Skip to content
Part 14 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Hannayensa ya ɗaga sama yana girgiza kansa “Na hutarki Uwar biyu. Bana son ki wahala da baby.” Ya shige toilet ɗin yana jin tana kiran.

“Allah ya tsare ni da haihuwar biyu, ɗayan ma ya aka kaya da wahalar sa, gashi ka gaza sauƙe nauyin kuɗin rainonsa ma.”

Yana jin sanda ta buɗe ɗakin ta fice, yana murmushi yana kisima adadin ɗabi’un Nahna Hafsa, a tunaninsa tana ƙoƙarin ɓoye kyawawan ɗabi’unta ne, ta hanyar bayyana marasa kyau.

Sai dai dole a cikin halinta akwai mafi kyau da zai sa mutum ya kasa mantawa da ita, ya kuma yi haƙuri da jirkitattun halayyar da take ƙoƙarin tsirarsu dan ɓoye kyawawan.

Bai daɗe a wankan ba ya fito yaga ta ajiye masa ƙananun kaya marasa nauyi.

Murmushi ya yi bayan ya shafa mai yasa kayan, yana jin ƙamshin turare mai sanyi na huda shi.

Fita ya yi cikin nutsuwarsa a lokacin ya taddata tana jera abinci a daining cikin sassarfa ya ƙarasa ya karɓi abincin ya fara ajiyewa.

“Ya baki bari su Nabeela sun yi girki ba kika yi da kanki, har kike jerawa? Hakan da wahala fa sosai Norul Khair.”

Bakinta ta ɗan taɓe tana hura hancinta “Ina son na samu lada ne yau. Nasan wannan ramar da ka yi harda rashin samun cin abincina mai daɗi.”

Kujera ya ja mata yana murmushi a ka ce idan ka haɗu da mutum ka tambaye shi ya yake, amma karka tambayi ya halinsa yake, domin hali zanen dutse ne ba a iya sauya shi.

“Tabbas na yi kewar haɗaɗɗen girkin ki. Amma hakan ba shi ya ramar da ni ba, kawai yanayi ne da kuma ƙarancin samun lokacin da nake da shi.”

Kanta ta girgiza tana buɗe manyan kulolin da ta zuba abincin. Tuwan farar shinkafa ne da miyar agushi, sai farfesun kayan cikin. Kasancewar Sayyadi ma’abocin son tuwo ne yasa ta fi yawan yi masa musamman da yammaci.

“Kai ne ka so bawa kanka wahala Sayyadi. Amma banda haka ban ga abin sa kai da zirga zirga akan matsalolin wasu ba. Aikin Hisbar nan naku da bashi da maraba da aikin sa kai da ba a baku ko sisi a kai, amma kullum kai ne can kai ne nan kamar shanshani uban tafiya.” Ta gama maganar tana tura masa filet ɗin abincin gabansa, da ƙamshinsa ya gama cika shi.

“Ladanmu na ga Allah Nahna. Duk kuma wadda ya yi aikin alkhairi da sa rai akan samun lada daga Allah, haƙiƙa ya dogara da babban bangon da baya rushewa.

Matsalolin aure a yanzu sun yi yawa, Nahna, ko ina ka je ka dawo abu kusan ɗaya ke ta faruwa. Ina jin tausayin gaza sauƙe wannan hakkin, banda dole babu abin da zai sa mace neman barin gidan mijinta.”

Idanuwanta ta ɗago ta ɗora a kansa tana kallonsa a lokacin da ya ke kora ruwan lemon kwakwa bakinsa.

“Kamar ya Sayyadi? Kana nufin har aure kuke rabawa a can ɗin?”

Kai ya gyaɗa mata “Idan muka gaza sulhutan al’amarin da kuma bada dama ga ma’auratan a karo na uku to kawai muna raba auren ne.”

“Yaran fa?”

“Mu barwa mafainsu shi, idan kuma a kwai na baya sai mu barwa macen har sai ta yaye shi.”

Kai ta gyaɗa tana jin babu daɗi a ranta ‘Lallai banda dole babu abin da zai sa mace ta bar gidan mijinta, ta kuma bar yaranta, amma kuma dolem dai dole ce.’

“Ki ci abincinki mana, ko na baki idan ba zaki iya ba?” Maganarsa ta dawo da ita daga tunanin data lula hakan yasa ta girgiza kai tana ƙaƙalo murmushi da kai abincin bakinta, duk yadda ta so cin tuwon sai taji bata jin ɗanɗanosa a bakinta dole ta haƙura da ci ta tashi tabar wajen.

Yana binta da rakiyar ido da kuma girgiza kai. Yasan ko ya tambayeta ba lallai ta kalle shi ba balle kuma ta ɗaga ido ta tanka masa. Hakan yasa ya buɗe ciki ya ci abincin tas.

Bayan watanni huɗu

Tun dare take jin cikinta na hautsinewa yana juyawa, wadda duk lokacin da ya juya sai ta ji bayanta ya riƙe da kuma mararta da take barazanar ɓallewa.  

Tun tana cijewa tana daurewa har abin ta gagareta, dole ta shiga kaiwa Abdul Mannan duka da yake bacci. A zabure ya tashi yana kallonta yana tambayarta ko lafiya.

“Banda rashin imani irin naku na maza yaushe rabon kaga na rintsa, amma dubi yadda kake zuba minshari kamar ragon da yake gaf….”

Ihu ta saki jin wani tsinanen ciwon da ya ƙara taso mata gadan-gadan tana jin kamar bayanta zai haɗe da mararta, yayin da kanta ke barazanar ɓallewa.

“Sayyadi zan mutu bayana, marata xa su haɗe waje guda! Kaina zai bar wuyana, Sayyadi.” Ta yi maganar da ƙaraji wadda tasa shi hantsilowa daga gadon.

Duk ya rikice ya rasa mai zai yi mata. Duka ta kai masa a ƙirjinsa “Ba gaba zaka sani da fuskar tausayi ba, ka kai ni asibiti.” Ta yi maganar tana matse kanta.

A ruɗe ya kinkimeta bai damu da kayan da ke jikinta ba, domin masifarta bata bari ya samu nutsuwa ba, a cikin motar ya kira Anna yake sheda mata  kasancewar lokacin ƙarfe tara na dare yasa ta ce su wuce asibitin gata nan zuwa.

Nurse’s ne suka tare su da sauri suka
shiga ɗaki da ita ɗakin ƴan haihuwa, suna dakatar da Sayyadi daga yunƙurin binsu da yake.

Tsayawa ya yi yana ta faman kaiwa da kawowa a harabar wajen, addu’a kam bai san kalar wadda ya sha yi mata ba. Har lokacin da Anna ta ƙaraso wajen ita da Nabila hankalinsu duk a tashe. Musamman Anna da ta gama sanin kalar wahalar naƙuda da haihuwa.

Zuwan su bai wuce awa guda ba sai ga Nurse ta fito. “A bamu kayan baby da zani xamu saka shi ta sauƙa.”

“Alhamdulillah.” Suka faɗa a tare cikin jeruwar baki.

Da sauri Nabila ta miƙe tawul mai laushi da kayan jariran da bata san ko guda nawa ba ne ta miƙawa Nurse ɗin.

Sai a lokacin Sayyadi ya mayar da kallonsa ga Anna “Nasan za a buƙace su shi yasa na zo da su.”

Uwa mai daɗi kenan, ya faɗa yana murmushi, wadda hakan kaɗai ya tabbatarwa da Anna farin cikin da yake ciki.

“Ni har na manta da hakan ma.” Ya yi maganar yana shafa kansa.

“Na sani ai.” A lokacin Nurse’s biyu suka fito da jarirai guda biyu a hannunsu.

Suka miƙawa Anna da Sayyadi da suke.wangale baki “Tagwaye ta duka maza ne.” Nurse ɗin ta faɗa cikin fara’a.

“Muna taya ku murna sosai. Mai jego na cikin ƙoshin lafiya.” Ɗayar ta faɗa.

Ashe murna na hana mutum magana.

<< Jini Ya Tsaga13Jini Ya Tsaga 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×