Skip to content
Part 17 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Bata san adadin lokacin da ta ɗauka a wajen ba, amma dai ta ji lokacin da mutanen wajen suka fara mata magana a kan ta basu waje su sha iska, matsalarta ta wuce.

“Sai dai na tabbata ba zaki taɓa samun fiye da Malam ba, kin kuma yi babban kuskure da wauta yarinya.” Babban mutumin ya faɗa, yana jin inama wannan ya haɗa dangi da ita, da ba abin da zai hana shi lakaɗa mata ɗan banzan duka.

Bata damu ba, domin ko kaɗan bata ji haushin maganarsa ba, asalima abin dariya ya bata da sai da ta murmusa.

“Na tabbata kana jin ƙuna da haushina, wannan kaɗai ya gamsar da ni a kan duk maganar da zaka faɗa ba a hayyacinka kake ba.”

Daga haka ta juya ta bar shi da sakakken bakin da yake binta da kallo.

Gidan su ta nifa kai tsaye, kasancewar babu wani abu nata mai muhimmanci wadda bata killace shi a waje ɗaya ba a gidan Sayyadi.

Abin hawa ta tare ya kaita ƙofar gidansu, yammace sakaliya ana gaf da kiran magana, tana da tabbacin Alhaji Malam na gida bai fita ba.

Sallama ta rangaɗa kafin daga bisani ta ɗora hannunta a kai, tana rafka ihu. Wadda yasa duk mutanen gidan suka fito a guje daga ɗakunansu shi kansa Alhaji Malam da yake alola barin butar ya yi ya nufo tsakar gidan.

Ya tadda matansa na kewaye da Hafsa suna jero mata tambayoyin lafiya da ina yaran? Mutuwa a ka yi?

Gyaran murya ya yi wadda yasa su matsawa suka bashi waje.

“Hafsatu lafiya kika shigo mana gida da karin magana kina kuka haka?”

Bata yi magana ba sai jan zuciyar da take, da ƙyar cikin rawar murya ta wadda ya sha kuka ya more ta miƙa masa takarda hannunta, cikin rawar hannu da bugawar zuciya Alhaji Malam ya karɓi takardar ya fara juyata.

“Takardar mene ne?” Ya yi tambayar yana jin tsoro da fargabar amsar da zata fito daga gare shi.

“Sayyadi ya sake ni Alhaji Malam?” Sai kuma ta rushe da kuka a lokacin da matansa suka fara jero salati suna tafa hannu cike da alhini.

Wata a cikinsu ma hannu ta ɗora a kanta tana salati.

“Ya sake ki?” Ya jefa tambayar yana jin shakkun maganar, yana jin kamar kunnuwansa basu jiyo masa daidai ba.

“Ya sake ni Alhaji Malam. Ya kwatanta abin da kowanne namiji ke da ikon yi a kan matansa. Ya kuma biyo komai kwabo da kwabo wadda ake kyautata zatonsa daga mijin da na aura mai kamar Babana.”

Daga haka ta share hawayenta, ta juya ta fice a gidan, tana jin yadda idanuwan su ke yawo a kanta, tana jin yadda wasu daga cikin matansa ke kiranta amma bata waiwaye su ba, kamar yadda bata juyo ta kalle su ba.

Takardar da ke hannunsa Alhaji Malam ya damƙe da ƙarfi, yana jin wani abu mai ɗaci da kauri na tasowa daga cikinsa yana haɗuwa da kakkauran yawun da ke bakinsa suna haɗewa a maƙoshinsa.

Bai buɗe takardar ba, ya koma ya ci gaba da alolar da yake, yana jin nauyi da kunyar matansa, da Hafsa ta gama yarfa masa magana a gabansu.

‘Ɗiyata ta cikina ke min haka, da faɗar kowata magana da ke bakinta.’ Ya yi maganar a ƙasan zuciyarsa.

*****
Ita kam daga fitarta kai tsaye shatar mota ta ɗauko suka kwashe komai nata, da duk wani abu da ta mallaka, daga nan suka wuce sokoto bayan ta biya lada mai yawa da masu motocin, bata da matsalar kuɗi, domin kuɗi ba damuwarta ba ne.

Ta gama zaman Jega zata koma rayuwa a Sokoto gidan Adda Halima, bata da matsala da mijin yayarta, domin tana da wararren ɗaki a gidan. A duk lokacin da ta je gidan, zata iya cewa kamar ya gadar mata da ɗakin ne, babu mai amfani a ɗakin sai ita.

Tun a hanya ta sanar da shi tana hanya da kayanta sun rabu da mijinta.

Ya yi jajjaɓi da salati bai hanata zuwa ba, domin yasan gidansa ne kaɗai zata zauna ta ji sanyi a ranta ta kuma sake. Kuma matarsa kaɗai ce zata iya zama da Hafsa fiye da can ɗin.

Bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya kira Alhaji malam ya sanar da shi halin da ake ciki, bayan ya masa jajen rabuwar auren Hafsa.

“Nan ta iyo kenan?” Ya samu kansa da jefa masa tambayar.

“Eh tana hanya ma yanzu haka.”
“Ba laifi to. An gode ƙwari da gaske malam Alhassan.”

Daga haka ya yanke wayar yana lumshe idanuwansa, yau ko karatu ba zai samu damar yiwa ɗalibansa ba, dan haka ya koma gida bayan ya sanar musu baya jin daɗi.

*****
“Abdul Ya kamata ka zo ka ɗauki yaran nan ka mayarsu wajen Mahaifiyarsu, dan dare ya yi sun fara jin bacci.”

Bai ɗago kai ya kalli Anna ɗin ba, domin tun da ya shigo gidan kansa ke sunkuye a ƙasa “A nan za su kwana yau.”

“Kamar ya a nan za su kwana? Ita kuma Yumnah kam ai ka san halin rigimarta dole dai ita ka kaita gida.”

“Har ita ma anan zata kwana.” Ya yi maganar da ƙyar, yanzu kam muryarsa ta fara rawa.

Zama Anna ta yi kusa da shi ta ɗago kansa tana kallonsa “Me ke faruwa? Ina mamansu ta ke? Nasan tun da ka yi aure baka taɓa wuce ƙarfe takwas a waje ba. Amma yanzu har ƙarfe goma kana zaune, kana kuma faɗa min yaranka ba za su koma gidanka ba. Me ya haɗaku da Hafsa?”

Maganar Anna ta ɗago masa da sabon mikin da ke zuciyarsa, abin da yake ƙoƙarin binnewa tun bayan sakin da ya miƙawa Nahna yanzu Anna ta tado masa da shi.

“Magana nake ma Abdul Mannan?” Ta yi maganar da ƙarfi.

Wadda yasa shi ɗagowa da rinanun  idanuwansa “Mun rabu da ita Anna. Na saki Nahna!” Maganar ta ƙwace a kan bakinsa.

Sai dai kafin ya yi shiru ya ji wani abu mai ƙara da giftawar haske a kan idanuwansa, kafin ya ankare ya sake jin wani lafiyayyen marin da ya ratsa ko ina a jikinsa.

Wannan shine karo na farko da zai ce Anna ta mare shi a tsawon rayuwarsa? Wannan shine karo na farko da ya ga fushin mahaifiyarsa.

“Ka saketa kace Abdul? Wanne irin hauka ne da rashin tunani a kanka? Dama kallon mai hankali da malamin da nake ma na banza ne Abdul?” Ta yi maganar hawaye na gangarowa a kan fuskarta.

“Me yasa zaka yanke irin wannan hukuncin baka yi shawara da ni ba? Me yasa Abdul?” Ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Wadda hakan yasa shi saƙowa ƙasa ya shimfiɗa gwuiwoyinsa a ƙas yana kamo hannun Anna.

Jikinsa rawa yake sosai, jijiyar kansa ta tashi raɗo raɗo, kukan da Anna ke yi na ƙara tsorata shi da karya masa da zuciya.

“Dan Allah Anna ki yi haƙuri ki daina kuka! Ban san ranki zai ɓaci haka ba Anna! Nahna bata sona duk tsawon lokacin da muka ɗauka. Yau har ƙarana ta kai ofishinmu na Birnin kebbi a kan na saketa. Hakan yasa na saketa Anna.”

Kai Anna ta girgirza har a lokacin hawaye na gangarowa a kan fuskarta “Ba gaskiya ba ne Abdul. Ba gaskiya ba ne a ce Hafsa bata sonka. Matar da kuka haifi yara har uku ce zata ce bata son ka kuma ka yarda ka saketa Abdul. 

Wannan kuskurene babba domin ni nasan wacece Hafsa, yarinyar kirki ce Abdul, ka yi babbar hasara, hasara mai girma Abdul.” Hawayen fuskarta ta share tana kallon yadda Abdul ɗin ya ke girgiza kai.

Hannunsa ta kama ta damƙe tana kallonsa ido cikin ido “Abdul Hafsa na sonke fiye da komai. Ba lallai ace ƙuruciya ta barta ta fahimci hakan ba, kamar yadda kaima ka haɗu da ƙuruciyar gaba ɗaya.

Zan faɗa ma wani abu da abaya na ce ba zan faɗa ma ba dangane da matarka, amma ya zame ma dole ka sani Sayyadi.

Shekarun baya da suka wuce bayan an sallameta a asibiti lokacin laulayin ƴan biyu, ta zo nan ta kawo mana kuɗi har dubu ɗari uku, saboda ta ji muna magana a asibiti ni da Yaya Salamatu. Wadda ta bani shawarar ya kamata na fara sana’a kodan yarana mata da ke gabana, saboda na sauƙaƙa ma wasu hidimar da ke kanka. A lokacin na sheda mata rashin kuɗi ne ya hanani yin jarin, wadda kasan itama Yaya Salamatun ba shi ne da ita ba. Na kuma ce ba zan iya tambayarka ba domin baka rage ni da komai ba.

Bamu san idanuwanta biyu ba, haka ta kawo min kuɗin tace dan Allah kar na faɗawa kowa, koda kai ne kaima kada na faɗa ma.

Shi yasa da ka tambaye ni ina na samu jari nace ma Inna ce ta bani aro dan ta siyar gonarta.

Bayan nan an sa auren Nabila ai kaima ka sani lokacin da take da cikin takwara, haka ta ɗauko kuɗi har dubu ɗari biyar ta bani, dan kawai a mata hidimar siyayya da kuma na biki. Bayan ta sanar da ni mace ce ya kamata ta san me ya dace da kayan ƙawa, wadda tana da tabbacin ba lallai kai ka san hakan ba.”

Tun da ta fara maganar yake kallonta, yana kallonta kamar wani sabon magiji ne ya samu, yana jin kamar ya yi kuskure ne ko kuwa dai maganar ce bai ji daidai ba.

Nahna dai ce duk ta yi wannan ga mahaifiyarsa, Idan bai yi kuskuren fahimta ba kamar kuɗaɗen da take amsa ne a wajensa a lokacin rainon cikin yaransa.

Daɓas ya zauna a ƙasa yana jin kansa na masa gingirin gim.

“Mata da yawa na ɗaukan uwar miji a matsayin maƙiya, amma Hafsa ta ɗauke ni a matsayin uwa. Ta kuma ɗauki ƙannenka a matsayin ƙannenta. Ta ruɓanya soyayya da kulawa a tare da mu Abdul. Faɗa min matar da bata son ka ce zata so ƴan uwanka da mahaifiyarka? Matar da bata son ka ce zata ɗauki manyan kuɗi ta bawa uwar da ba tata ba?”

Kai ya shiga girgizawa yana jin hawaye na ƙara tsere a fuskarsa, tabbas ya yi kuskure, ya kuma yi aiki da rashin hankali.

“Ka je ka dawo da matarka Abdul!”
Kai ya shiga girgizawa wani hawayen  na ƙara tsere a fuskarsa “Saki uku na mata Anna!” Ya yi maganar hawaye na ɓallewa a fuskarsa.

“UKU!” Anna ta faɗa kafin ta zame hannunsa daga cikin nasa ta shige ɗaki. Bata da sauran maganar da zata masa a yanzu, domin idan har ta iya zama a kusa da shi zata masa zagin ƙare dangi wadda bata taɓa yin irinsa ba, ƙila ta masa abin da ya fi zagin.

Jingina ya yi daga jikin kujerar yana jin kansa na masa nauyi, nauyi na sosai da sosai “Me yasa Nahna? Me yasa?” Ya yi maganar yana bubbuga goshinsa da hannunsa, wannan shine karo na farko a rayuwarsa da yake jin ya aikata kuskure, ya kuma yanke hukunci cike da wauta.

Shi yasa aka ce sheɗan na gudu a cikin jini fiye da harbawar zuciya a lokacin da rai ya ɓaci, yanzu kam ya tabbata sheɗanin da ya ke ta ƙoƙarin yaƙa shine ya shige jininsa ya sarrafa tunaninsa har ya saki Nahna, saki har guda uku.

Sokoto

Har ƙofar gida motar ta kaita aka sauƙe mata kayanta, a lokacin ta shiga gidan ta sanar da Mijin Adda halima zuwan nasu.

Shine ya fito ya nuna musu wani shago a ƙofar gidan aka loda kayan nata, sannan ita kuma ta shige gidan.

Tana jin Adda Halima na jero mata tambaya amma bata kulata ba, ta shiga ta yi wanka ta ɗauro alwala, bayan ta idar sallah ta kalli Adda Halima.

“Zan samu abinci Adda Halima?” Harara ta maka mata “Abinci Hafsa? Yanzu har kina da nutsuwar da zaki ci abinci a wannan yanayin?”

“Au mutuwa zan yi kenan idan ban nemi abinci ba? Dan miji ya sake ni sai na kasa cin abinci Adda Halima. To ko dai kema bakya maraba da zuwana ne na koma inda na fito ko kuma na shiga duniya?”

Miƙewa Adda Halima ta yi tana ɗaga hannunta “Zauna indai abinci ne ba na kawo miki.” Ta shiga kitchen sai gata ta fito da kulolin abincin manya shimkafa ce da miyar kaji ta sai kayan ganye.

Gyara zama Hafsa ta yi taja faranti ta zuba abincin mai yawa, ita dai Adda Halima kallonta ta ke ganin uban abincin da ta zuba

“Yanzu wannan zaki iya cin sa?”

Bata ba ta amsa ba ta shiga cin abinci da mamakin Adda Halima tas ta cinye.
Ta kuma kora da ruwa.

“Alhamdulillah.” Ta faɗa tana shafa cikinta ta kuma mayar da kallonta ga Adda Haliman da ta saki baki tana kallonta kamar ta samu majigi.

“Tun da Malam ya sanar da ni mutuwar aurenki na kasa koda haɗiyar ruwa ne, balle na ci abinci Hafsa. Amma sai gashi ke kin cika tire kin kuma cinye abinci tas.

Hakan na nuna min ke ce kika buƙaci sakin daga gare shi?”

Shafa kanta Hafsa ta yi tana murza gashin girarta.

“Tun da kin sani mene ne na son tabbatarwa kuma? Kawai dai ƙaddarar auren mu ne ta ƙare da shi Adda Halima.”

Ta yi maganar tana tashi da tattare kwanikan abincin.

“Amma kin cutar da rayuwarsa da ta yaranku. Kina ga hakkinsa zai barki  ki rayu cikin farin ciki?”

Cak ta tsaya tana kallon Adda Haliman “Hakkin sa? Farin ciki? Bana jin a kwai sauran hakkinsa da ya rage a kaina Adda Halima. Na bashi komai da nake da shi, ciki harda yardata da kuma kyakkyawar tagoma shi na soyayya. Na ajiye masa kyawawan yaran da zai kalla wadda zai tuna alkhairin da na bar masa.”

Kai Adda Halima ta girgiza tana kallon Hafsa “Ya za ki yi da soyayyarki da ke zuciyarsa? Ya zaki yi da cutarwar ƙaunar da kika nuna masa a baya?”

“Ya cire zuciyar ya wanke.” Daga haka ta fice ta bar Adda Haliman da sakekken baki. Bata dawo ɗakin ba ta dai ji hirarta da jajen da abokanan xamanta ke mata, tana jin yadda take marereci murya har zuwa lokacin da Malam ya shigo ya ƙara mata nasiha da tausarta a kan karɓan ƙaddara.

“Hmmmm!” Kawai Adda Halima ta iya faɗa, domin ta riga tasan Hafsa mishan ce ɓadda musulmai ji yadda take kwantar da kai tana murya  da rawa..

<< Jini Ya Tsaga 16Jini Ya Tsaga 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×