Skip to content
Part 23 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Umma! Kina gani, a gaban idonki Anty Hafsa ke azabtar da Bunayya, amma ba ki ɗauki kowanne mataki a kai ba. Baki hana Anty Hafsa azabtar da marainiyar yarinya ba.

Ki kalli yadda ta ke miki magana da izgili Umma. Ki duba damar da kika bawa Anty Hafsa wadda ko iyayenta basu bata ba. Shin Umma wannan soyayya ce ta jini ko kuwa cutar kai da kai ne kuke yiwa junanku?” Hajara ta yi magana da sanyin murya tana jin muryarta na rawa, tan ajin ɗacin da ke tasowa tun daga kan maƙoshinta yana ketowa har zuwa harshenta.

Kai ta girgiza hawaye na gangarowa a kan fuskarta “Wannan ba soyayya ba ce Umma. Wannan ba soyayya kikewa Anty Hafsa ba. Domin idan kana son mutum kana faɗa masa laifinsa ka kuma dakatar da shi daga faɗawa halaka. Ka kuma nuna ƙarfin ikon ka akan duk wani taƙadirancin mutun.

Umma ki dawo daga mutuwar wucin gadin da kika yi, ki buɗe idanuwanki ki fahimtar da Anty Hafsa ke ce yayarta, a ƙarƙashin ikon ki take take ci da alfarmarki.”

Kallon Hajaran ta yi a karo na ba adadi tana ƙoƙarin ajiye  maganarta a bigiren da ya dace, sai dai bata so ta bata ƙofa ɗaya da zata ji a ranta cewar Hafsa na da naƙasu ga rayuwarsu.

“Hafsa ƴar uwata ce, Hajarko! Ina so ku fahimci hakan ku kuma riƙe hakan a matsayin kalmata. Duk lalacewar Hafsa ina sonta, ba zan iya mata gorin muhallina da sunan nawa ba, balle na koreta daga cikinsa.

Bana so ki dawo da magana ɗaya, ki kuma ci gaba da nanata, Bunayya ɗiyarta ce da ta haifeta, ta kuma fi mu jin zafinta, me zai sa mu hana zuciyarmu nutsuwa ga wadda yake da kwantacciyar zuciya kamar Hafsa.

Daga yau bana buƙatar ganinki a gidan nan muddum xaki min maganar Hafsa ne ko aibanta ta.”

Matse hannun Bunayya ta yi daga ruƙonta, tana kuma ciza laɓɓanta kamar zata taunesu gaba ɗaya.

“Shikenan Umma, zan tafi. Ki yi haƙuri idan abin da na faɗa miki ya ɓata miki rai, ina fatan Allah ya tsayar duk wata fitinar da zata raba ki da hankalinki, da kuma gujewa tarkon kaidin Anty Hafsa.”

Daga haka ta juya tana riƙe da hannun Bunayya.

“Ina zaki kaita kuma da kika ɗauketa?”

“Zan kaita inda ya cancanta ya dace da ita.” Daga haka ta sa sauri tabar gidan tana jin Ummanta na kiranta amma bata waiwayo ba, asalima mashin ta haye tana bada umarnin tafiya da ita.

Tunani ta fara yi a kan mashin ɗin, idan ta wuce da Bunayya gidanta to Anty Hafsa zata je ta ɗauketa bayan ta gama barbaɗa mata rigar rashin mutunci, mafita ɗaya gareta a yanzu, shine ta mayar da Bunayya wajen dangin mahaifinta, waɗanda suke nan Sokota. Daga gidanta zata ɗauki nauyin kowata ɗawainiya da wahalarta, ciki harda zirga zirgar makarantar ta da suturarta.

Cikin sa’a kuwa tana zuwa gidan ta samu yayan Mukhtar mahaifin Bunayya, shi da ƙaninsa sun zo gaida mahaifiyarsu.

Ganin Bunayya yasa suka fara fara’a da tararsu. Bayan gaisawar da suka yi, Hajara ta basu labarin komai da ke faruwa da Bunayya, wadda hakan yasa su yin jimami da tu’ajjabin abin da ke faruwa, suka fara salati.

“Ba wai na dawo da Bunayya dan bani da halin riƙeta ba, ko kuma cikinmu babu mai ƙarfin da zai riƙeta ba ne.

A’a na kawota nan ne dan ina ganin zai fi zama kariya da garkuwa a gareta, daga nan ɗin zata samu sauƙi da sassaucin uƙubar da mahaifiyarta ke bata. Ni kuma zan ɗauki ɗawainiyar kowanne abu na rayuwarta daga kan karatunta lafiyarta har zuwa suturinta, in sha Allah.

Ni dai fatana ku riƙeta anan ɗin, zan jure kowata matsala da zata shigo tsakanina da Anty Hafsa.”Hajara ta faɗa cikin sanyin murya.

Hakan yasa Mamansu matse hawayen fuskarta “Lallai idan da ranka kaga abin mamaki. Ban taɓa tunani ko hasashen hakan zai faru ga marainiyar yarinya kamar takwara ba, kamar yadda ban taɓa kawowa a raina Hafsatu na da wasu halayya marasa kyau irin wannan ba. Mun gode sosai yarinya, Allah ya saka da alkhairi ya kuma ƙara zumunci.”

“Babu abin mamaki a wannan rayuwar, komai mutum zai iya yinsa dan wasu burika nasa. Hajara mun gode sosai, sannan ba zamu barki da wahalar ɗaukan nauyin komai na Bunayya ba. Mune mafi cancanta da hakan, kuma in sha Allah zamu yi mata komai a matsayinmu na ƴan uwan mahaifinta.” Yayan Mukhtar ya faɗa.

Wadda hakan yasa Hajara risinar da kanta “Dan Allah Baba ku barni na samu ladan marainiya. Ina son Bunayya kamar yadda nake son su Jiddah. Nasan kune mafi cancanta da komai na rayuwarta, amma ina so nima ku bani ladan tallafawa maraya da kuma ƙarfafa zumuncin mu. Ina son komai da ya kasance na Anty Hafsa kamar yadda Umman mu ke sonta, ku bar ni na cika gurbin soyayyar da kyautatawa Bunayya. Dan Allah.” Ta yi maganar cikin sanyin murya.

Dukkan su da ido suke binta suna jinjinawa karamci da ƙarfin zumunci irin na ahalin Alhassan.

“Yaya mu barta ta yi abin da take so, idan ta kakare sai mu yi mu ɗin, ai duk bata ɓaci ba.” Kawu Lamiru ya faɗa ƙanin Mukhatar.

“Ban taɓa tunanin a duniya akwai mutane masu kyakkyawar zuciya irin taki ba.

Kyautatawa wadda ya cutar da kai, wannan abu ne da ba ya faruwa a rayuwar zahiri. Allah ya miki albarka ya buɗa miki ƙofofin alkhairai.” Alh. Zaidu ya faɗa.

Hakan yasa suka amsa da min ita kam Mama ta rasa bakin magana haka dai ta yi ta jero mata albarka har zuwa lokacin da ta miƙe a kan ƙafafuwanta tana ajiye kuɗaɗe da aƙalla za su yi dubu ashiri “Ga wannan gobe a kai Bunayya makaranta, idan bai isa ba ga lambar wayata sai a kirani.” Ta haɗa harda katin ta na aiki, kasancewarta ma’aikaciyar lafiya ce.

“Kaya kuma zuwa dare zan aiko mata wasu in sha Allah.”

Daga haka ta miƙe a kan ƙafafuwanta tana jin yadda suke jero mata godiya da fatan alkhairi hadda rakiya.

Ta tare Adai-daita ta hau suna ɗaga mata hannu.

*****
Lokacin da Hafsa ta dawo gida daga yawon maƙota taga babu Bunayya babu Hafsa, ta tambayi Adda Halima ta faɗa mata sun fita tare ba ƙarin hauka ta yi ba, ta gayawa Adda Halima magana son ranta.

“Ni bana son shisshigi bana son munafunci, akan me wata zata ɗauki ɗiyata ta fita da ita babu izini kuma kina kallo baki hana ba. Yanzu wannan uban kunun ayar da na yi ni zan fita talla ko ke? Ko kuwa yaranki masu kan ɓari da basa ciniki sai ganjaɓo.”

Ita dai bata tanka mata ba, ganin lokaci na tafiya ta zari hijab ta tafi, gidan Hajara, sai dai ga mamakinta mai gadi ya tareta yana sheda mata ba kowa a gidan.

“Ba kowa kamar yaya?” Ta jefa masa tambayar cike da izgili da rashin mutunci, shima da yake cikekken buzu ne ya jefa mata harara.

“Kamar yadda kika gani dai.” Ya buga ƙofar get ɗin ƙaranta na sauƙa har a tsakiyar kanta.

A lokacin ne taji dirin tsayiwar adaidaita a bayanta hakan yasa ta juyo a hautsine ganin Hajara na sallamar mai Adaidaita yasa ta ƙaraso wajen a fusace tana duba cikin adaidaitar. 

Sai dai babu Bunayya babu dalilinta.

“Ina ɗiyata take Hajara?”

“Tana inda ya dace sa ita.”

Ta yi maganar tana raɓawa ta gefenta sai dai Hafsa ta fizgota ta dawo gabanta “Gidan uban wa kika kai min ƴata Hajara?”

“Gidan ubanta.” Ta bata amsar a taƙaice tana barin wajen.

Hakan yasa Hafsa runtuma uwar ashaar “Yau kuwa akwai bala’i. Kin kuma janyowa uwarki shi da hannunki.”

<< Jini Ya Tsaga 22Jini Ya Tsaga 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×